Matsalar shaye-shaye a Jihar Kano
Salam, Editan jaridar Aminiya, zan so ka ba ni dama don in yi tsokaci game da abin da ke damun al’ummarmu ta Arewa, musamman mazauna Jihar Kano. Wannan matsala kuwa ita ce ta shaye-shaye ga samari da kuma ’yan mata. A wasu lokutan ma har da matan aure da magidanta. Misali a Qaramar Hukumar Dala […]
Salam, Editan jaridar Aminiya, zan so ka ba ni dama don in yi tsokaci game da abin da ke damun al’ummarmu ta Arewa, musamman mazauna Jihar Kano. Wannan matsala kuwa ita ce ta shaye-shaye ga samari da kuma ’yan mata. A wasu lokutan ma har da matan aure da magidanta. Misali a Qaramar Hukumar Dala abin ya ci tura inda da zarar an ce dare ya yi to za ka iske babu masaka tsinke sai dai ka rika jin warin wiwi da sauran hayakin kayan maye sun mamaye unguwar. A kwanakin baya sai da Babban Jami’in ’Yan Sanda (DPO) mai kula da yankin Dala shi da jami’ansa suka kai sameme kuma suka yi nasarar yin kame amma kwanaki kadan abin ya sake ci gaba.
Yanzu haka mazauna Unguwar Dala suna cikin fargaba da tashin hankali inda masu yin shaye-shayen suke cin karensu babu babbaka don haka muke kira ga jami’an tsaro da su kawo mana dauki.
Muna godiya ga jaridar Aminiya yadda take isar mana sakonninmu ga mahukunta.
Daga Sadiya Dala 09053204833