Matsalar shaye-shaye laifin wane ne?
Ga dukkan alamu zan iya cewa shaye-shayen abubuwan da ke sanya maye ko kawar da hankali sun zama ruwan dare a Najeriya, idan aka yi la’akari da yadda dimbin matasa suke shaye-shaye ba dare ba rana. Zai yi wuyar gaske a wannan lokaci mutum ya shiga kusan kowace unguwa ba tare da ya yi kicibis […]
Ga dukkan alamu zan iya cewa shaye-shayen abubuwan da ke sanya maye ko kawar da hankali sun zama ruwan dare a Najeriya, idan aka yi la’akari da yadda dimbin matasa suke shaye-shaye ba dare ba rana. Zai yi wuyar gaske a wannan lokaci mutum ya shiga kusan kowace unguwa ba tare da ya yi kicibis da matasan suna burarewa ko shacewa ba. Wani abin ban haushi da takaici yanzu amfani da kayan kawar da hankali ba wai ya tsaya ga matasa maza kadai ba ne. Su ma ’yan mata sun jefa kansu cikin wannan mugun sha’ani.
Yayin da matasa suka dukufa ga shan tabar wiwi da farar kwaya da roci d dizi da sholisho da ruwan gam da madarar sukudaye da shakar masai ko dagwalon kwata da kashin kadangare da fetur, su kuma ’yan matan sukan sha fakalin da emzolin da banalin da totolin da shisha da sauransu.
Sai dai inda wannan lamarin ke kara daure kai, wannan harka ta shaye-shaye ta fara nisa domin ta isa har ga wasu tsofaffi masu budurwar zuciya, inda suka tsoma hannunsu cikin tu’ammali da miyagun kwayoyi. Su kuma suna karkata ne zuwa ga shan taramol da asmanol F da farar kwaya da wiwi da yawaita shan neskafe da sauransu. Abin mamaki kusan kowace kasa tana da hukumar da ke hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, to amma duk da hake shaye-shayen suna ta kara bunkasa!
Iyaye suna ganin irin halin da ’ya’yansu ke ciki amma sun zura musu ido. Shin laifin wane ne? Saboda haka ina bai wa gwamnati da iyaye da malamai da sarakuna da kungiyoyi da mu kanmu matasa, shawarar cewa mu tashi haikan wajen yin kira da jawo hankali da fadakarwa da yin wa’azi ga masu shaye-shayen. Mu nuna musu illolin hakan, kuma mu nuna musu su ne za su zama shugabannin gobe. Ita kuma hukuma ta tashi haikan wajen ganin ta hana shigowa ko safarar miyagun kwayoyin. Domin sai an shigo da su ne sannan mashayan za su saya. Kuma hukuma ta rika yin hukunci mai tsanani ga dillalai da masu sayar da miyagun kwayoyin da masu sha. Domin yin hukuncin zai zame darasi ga sauran jama’a ko masu sha’awar shiga cikinta.
Haruna Muhammad Katsina,
Shugaban kungiyar Muryar Jama’a, Reshen Jihar Katsina.
07039205659 ko 0705749105