Matsalar tabarbarewar tsaro a Jihar Zamfara

Wannan shi ne lokaci mafi muni na rashin tsaro da Jihar Zamfara ta taba samun kanta. A shekarun baya, ba jahar da ke da tarihin zaman Lafiya kamar Jiharmu ta Zamfara, sai dai a ’yan shekarun nan jahar na sahun gaba wajen, rashin tsaro. Kullum ana kashe mutanen da ba su ji ba, ba su […]

Matsalar tabarbarewar tsaro a Jihar Zamfara

Wannan shi ne lokaci mafi muni na rashin tsaro da Jihar Zamfara ta taba samun kanta.

A shekarun baya, ba jahar da ke da tarihin zaman Lafiya kamar Jiharmu ta Zamfara, sai dai a ’yan shekarun nan jahar na sahun gaba wajen, rashin tsaro. Kullum ana kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. 

Yayin da al’ummar karkara su ke azabtuwa da fuskantar kisan gilla daga barayin shanu da  yi musu kisan dauki daidai tare da sace masu dukiya da kone wadcce ba su iya dauka tare da yi wa ’yan mata  da matan aure fyade.

Mu Kuma da ke cikin garuruwa muna fuskantar matsalolin tsaro daga ’yan ta’adda da suka mayar da kisan al’umma wata sana’a tare da la’antar mutane ba gaira ba dalili, tare da barayi da kan shiga gidajen al’umma su wawushe dukiya tare da yin gaba da kaddarorinsu.

Hakika wannan matsalar ba ta biyunta a Jihar Zamfara. Kuma kacokan wannan matsalar za mu iya dora kashi caas’in din ta ga Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Abdul’aziz Abubakar Yari, ganin yadda Gwamnatinsa take nuna halin ko-in-kula  da wannan matsalar tun tana sabuwaDomin idan muka dubi abun da ya ke faruwa a kauyukkanmu na karkara, farkon wannan matsalar za a iya magance ta cikin ruwan sanyi, amma aka yi biris da su har suka mallaki miyagun makamai. Hakazalika babban abun da ya kawo wannan matsalar a cikin garuruwanmu shi ne, tsabar rashin aikin yi ga matasa ga kuma kunnen uwar shegu da Gwamnatin ta yi da mu matasa, ba mu da aikin yi, uwayenmu na cikin kunci na rashin biyansu hakkokinsu kamar yadda ya dace a karshen wata, ga tsantsar jahilci da ya yi mana yawa, ganin yadda Gwamnatin kan ki biyan kudin Jarabawar WAEC da NECO kan kari wanda hakan kan sanya matasa da dama tsaiko wajen  cigaba da karatun, daidaikun da ke da zuciyar yi, sai sun fara sai talauci ya yi masu katutu dole su daina domin ba wani tallafi da gwamnatin ke bai wa dalibbai wajen karfafa musu gwiwar yin karatu.

Sai kuma babbar matsala ita ce,  yadda al’ummar karkara ke kokawa da cewa ko da sun tseguntawa hukuma  masu aikata aika-aikar kwana biyu bayan an kama ’yan ta’addar ake sako su, tare da sanar da su ’yan ta’addar wanda ya tona masu asiri. 

Daga karshe sai ka tarar an yi wa wanda ya bai wa jami’an tsaron labarin aukuwar abun illa! An Kashe shi, kasan gilla tare da tozarci. Wanda hakan ne, silar da ya sa ba kasafai ake samun hadin kan ’yan kauyen ba. Wanda hakan na nuna akwai jami’an tsaron, da su ake hada kai wajen kara jefa jihar Zamfara cikin kuncin rashin tsaro. 

Dan haka muddun ana son yin maganin wannan matsalar, sai ita Gwamnatin jahar Zamfara, ta sanya a ranta cewa tana bukatar kawo karshen wannan matsalar, ta hanyar shawo kan matsalolin da suka zama silar tarwatsuwar al’amurran.  

Ya zama dole Gwamnatin jahar Zamfara ta tashi tsaye wajen kare rayukkan jama’a da dukiyoyinsu domin Wallahi wannan masifar ta yi muni matukar gaske! 

Sannan dole a sanya wa jami’an tsaronmu ido domin bata-garin cikinsu ne, ke kara assasa wannan masifar. 

A karshe muna rokon Allah Ya sa wannan koken namu ya kai ga kunnuwan wadanda muka yi domin su, Ya kuma  ba su ikon kawo mana dauki. Allah kana amsar addu’o’in bayinka a duk lokacin da suka roke ka. Ya Allah muna rokon Ka kawo muna karshen wadannan tashe-tashen hankullan, Ka kawo muna dawwamammen zaman Lafiya a jiharmu ta Zamfara, yankin Arewa da ma Najeriya baki daya. Allahumma amin.

 

Abdulmalik Sa’idu Mai Buredi Tashar Bagu Gusau (Jami’in Hulda Da Jama’a Na Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa Reshen Jahar Zamfara) 08069807496