Matsalar taki a bana

Daminar bana dai tubrkalla, duk kuwa da cewa ta zo da matsaloli da yawa.  Da farko dai ruwan shuka bai samu ba da wuri a wasu sassan Arewacin kasar nan, sa’anan kuma manoma sun yi ta hakilo wajen neman kayayyakin noma da ya kamata a ce sun samu tun kafin faduwar daminar. Baicin haka nan […]

Matsalar taki a bana
Matsalar taki a bana

Daminar bana dai tubrkalla, duk kuwa da cewa ta zo da matsaloli da yawa.  Da farko dai ruwan shuka bai samu ba da wuri a wasu sassan Arewacin kasar nan, sa’anan kuma manoma sun yi ta hakilo wajen neman kayayyakin noma da ya kamata a ce sun samu tun kafin faduwar daminar. Baicin haka nan kuma ruwan sama ya yi gyara a  wurare da yawa sa’ilin da daminar ta fara nisa. A wasu garuruwan, musamman a  shiyyar Arewa,  an ga abin mamaki game da yanayin faduwar ruwan, wanda aka ce an yi shekaru kusan 200 ba a taba samun irin haka ba. Duk da cewa daminar bana ta yi jinkiri, har sai da ka dukufa rokon ruwa a wasu wurare na Arewaci, amma daga bisani an samu ruwa mai yawa da ya haddasa ambaliyar da ta janyo rushewar gidaje da lalata amfanin da aka shusshuka a gonaki.
 Ana cikin haka ne kuma sai aka shiga wani hali na matsanacin rashin takin zamani sakamakon ci gaba da tsarin da gwamnatin da ta shude ta bullo da shi na dillancinsa da talakwa ba su gama nakalta ba, wanda kuma bai amfane su ba don rashin fa’idarsa ga harkokinsu. An bullo da sabon tsarin samar da taki ne don a magance almundahana da  ha’incin da ke wanzuwa a kasuwannin sayar da taki da yadda ake bin dabarun haramta shi ga ainihin manoman da ke matukar bukatarsa, ana bi takan hamshakan mutanen da ba abin da ya hada su da noma, amma sai ga shi nan kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu, domin ma’aikatan hukumomi wadanda ke lilo a kujerun cikin ofis, suna shan rabar eyakwandishan ne ke aiwatar da tsarin da wasu can dabam suka kitsa don kakkabe hannun wadanda ba manoma ne ba wajen hada-hadar samar da takin. Shi ya sa aka yi wa manoma salalar tsiya a wannan marrar don sun bi ta kan wayar salula wajen sayen takin da bai wadatar da su ba, ba su kuma samu kan kari ba.
Dangane da haka ana iya cewa mafi yawan takin da ya shiga hannun manoma daga kasuwannin bayan fage ya fito, kuma duk da dan karen tsadarsa haka nan wasu suka rufe ido suka saya, domin kuwa idan har da manoman sun tsaya jiran takin hukuma ne da har daminar sai ta wuce ba su noma gonakinsu ba. Maimakon wannan tsari da gwamnatin tarayya ta bullo da shi ya inganta dabarar sayar da takin ga mabukatansa, sai ma ya kara dagula al’amura, takin ya ki samuwa, manoma kuma suka shiga cikin gagarumar damuwa. Abin da ya fi sa hankulan manoma dugunzuma shi ne ganin yadda damina ke neman gushewa, ga yabanyar gonakinsu ta fara yaushi da canja kala, amma ba wani takamammen lokacin samun takin da zai farfado da ita.
 dan takin da ake ganin hukuma ta samar na gwamnatin tarayya ne, gwamnatocin jihohi  da yawa, da kuma aksarin kananan hukumomi ba su tabuka ba wajen samar da takin a bana. An ce sun kashe makudan kudi wajen sayowa, amma babu wanda zai iya cewa ga yadda aka yi da takin. Idan kuma da za a ce gwamnatocin jihohi za su firfito da takin a wannan lokacin ba wani  tasirin da zai yi ga  manoma, domin kuwa bakin alkalami ya dade da bushewa, an bar gini tun ranar zane. Shi ya sa manoma da yawa suka ga samu, suka kuma ga rashi; rijiya ta bayar da ruwa amma guga ta hana. Ga dai damina ta kankama, ta karfafa zukatan manoma, amma rashin taki ya karya musu gwiwa.
Sa’ilin da manoma da sauran jama’a ke tsakiyar kukan targade sai kuma ga karaya ta zo a wuri mai wuyar dorawa. Amma duk da haka nan wasu manoman sun  ganganda dan abin hannunsu da wanda suka iya rantowa daga ‘yanuwa da abokan arziki, suka narkar a gonakinsu, sun fara ganin alamun albarka mai waya, amma cikin kankanen lokaci sai murnarsu ta koma ciki, domin kuwa kokofin sama’u sun yi ta  bubbudewa, ruwan sama kuma ya yi ta kwararowa kamar da bakin kwarya a wasu sassan kasar nan, inda hakan ya haddasa ambaliyar da ta jawo  asarar rayukan da ba su kidayuwa da dukiyar da ba ta misaltuwa. Amma  illar ambaliyar ta fi kazanta ne a gonakin talakawa, inda har ya zuwa gobe babu wanda zai iya kintata adadin asarar amfanin da aka yi a wadanda ruwan ya mamaye. Amfanin da ambaliyar ta lalata ya hada da dukkan nau’o’in abincin da ake nomawa a kasar nan; wasu sun nuna, an fara girbewa, wasu kuma ana cikin shirin kawarwa daga gonakin zuwa rumbuna.
To, ba ga asarar rayuka da gidaje ne illar ambaliyar ruwar ta tsaya ba kadai, asarar amfanin gonar da hakan ya shafa ta shafi ilahirin jama’ar kasar nan, domin kuwa hakan zai iya kawo karanci da hauhawar farashin abinci a dukkan kasuwanni. Sa’annan kuma idan aka yi la’akari da yadda rashin takin zamani a bana ya jawo wa manoma fitintinu da wahaloli ana iya hasashen cewa amfaninn gona a bana na iya kasa na sauran shekarun. Wannan babban abin damuwa ne ainun da ya kamata tun yanzu a tashi haikan wajen yi wa wannan al’amari tubkar hanci. Ta haka ne za a iya shawo kansa tun kafin ya yi kamari bayan wucewar daminar bana, domin kuwa ga shi tun a yanzu farashin muhimman kayayyakin abinci ya fara haurewa.