Matsalar talauci da rashin aikin yi a Najeriya: Laifin gwamnati ko na al’umma?2
Dukkan alkaluman da ake amfani da su na tantance bunkasar tattalin arzikin kasa sun nuna yadda talauci da rashin aikin yi suka yi katutu a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin wa za a dora wa alhakin kasancewar haka, gwamnati ko al’ummar kasa? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana: Gwamnati […]
Dukkan alkaluman da ake amfani da su na tantance bunkasar tattalin arzikin kasa sun nuna yadda talauci da rashin aikin yi suka yi katutu a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin wa za a dora wa alhakin kasancewar haka, gwamnati ko al’ummar kasa? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Gwamnati ce da laifi – Ibrahim Ahmadu
Ibrahim Ahmadu: “Wato gaskiyar lamarin, gwamnatin Najeriya ita ce da babban laifi a kan batun talauci da yake ci gaba da addabar al’ummar kasar nan dalili kuwa shi ne, ita ce take da wuka da nama amma sai ya kasance shugabanni a karkashinta suka bi suka kashe kasa baki daya, babu tsaro da zai ba kasashen waje amincewar zuba jari a kasar nan. Tattalin arzikinmu ya ruguje, babu kamfanoni ko wasu masana’antu masu yin aiki kai tsaye ballantana a samu aikin yi, sannan kuma idan aka lura sosai da idon basira, sai a ga cewa gaba dayan shirin gwamnatin ya kare ne cikin yaudara da rudani, domin gwamnatin ba ta ba al’ummar kasar nan damar sanin inda ta sa gabanta.”