Matsalar talauci da rashin aikin yi a Najeriya: Laifin gwamnati ko na al’umma?3
Dukkan alkaluman da ake amfani da su na tantance bunkasar tattalin arzikin kasa sun nuna yadda talauci da rashin aikin yi suka yi katutu a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin wa za a dora wa alhakin kasancewar haka, gwamnati ko al’ummar kasa? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana: Laifin […]
Dukkan alkaluman da ake amfani da su na tantance bunkasar tattalin arzikin kasa sun nuna yadda talauci da rashin aikin yi suka yi katutu a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin wa za a dora wa alhakin kasancewar haka, gwamnati ko al’ummar kasa? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Laifin bangare biyu ne – Sarkin Zangon Deidei
Alhaji Muhammadu Sa’ad Kusada, Sarkin Zangon Deidei: “Kowa da nasa laifin. Har kullum abin da kake kira da bakinka, shi kake samu; duk wanda ya tsine wa shugabansa, to sai Allah Ya ba shi shugaban da zai wahalar da shi. Annabi ya ce mutum ya fadi alheri ko ya yi shiru. Ina ganin wannan na daya daga cikin matsalolin da ya taimaka wajen samar wa kasar nan yawaitar shugabanni marasa tausayi da tsoron Allah, wanda a sakamakon haka ake ta samun karuwar talauci a maimakon raguwa.”