Matsalar talauci da rashin aikin yi a Najeriya: Laifin gwamnati ko na al’umma?6
Dukkan alkaluman da ake amfani da su na tantance bunkasar tattalin arzikin kasa sun nuna yadda talauci da rashin aikin yi suka yi katutu a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin wa za a dora wa alhakin kasancewar haka, gwamnati ko al’ummar kasa? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana: Laifin […]
Dukkan alkaluman da ake amfani da su na tantance bunkasar tattalin arzikin kasa sun nuna yadda talauci da rashin aikin yi suka yi katutu a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin wa za a dora wa alhakin kasancewar haka, gwamnati ko al’ummar kasa? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Laifin na jama’a ne da gwamnati – Abdurrahman Khalil
Abdurrahman Ibrahim Khaliel Azare: “Gaskiya akwai laifi ta kowane bangare, don mutane ke zama gwamnati amma saboda tsare-tsaren da gwamnati ke yi ba a tabbatar da su yadda ya kamata shi ya sa ba a gani a kasa. Duk da haka mutane ba za su kwanta su ce sai an musu ba, ta nan akwai laifinsu na rashin tashi tsaye ko kuma raina baiwar da Allah Ya yi musu, suna kashe zukatansu da dogon buri, alhali da sannu mutum zai kai matsayin da yake hange; wanda ya fi inda yake. Gwamnati ta fito da hanyoyin samun kudi don magance matsalar da kuma tabbatar da cewa an yi aiki da wadannan hanyoyi yadda ya kamata; domin duk wanda aka yi dominsa ya shaida, shi zai samar da zaman lafiya. Su kuma mutane bai dace su kwanta su ce gwamnati ce za ta yi musu komai ba. Dole kowa ya tashi tsaye kan sana’ar da ya gada daga iyayensa ko ya tashi ya ga wani nasa a kai, shi ma ya kutsa kai ya shiga koda kuwa akwai kaskanci a ciki da haka zai yi sama a duk lokacin da ya samu sukunin yin hakan.”