Matsalar tattalin arkiki kasa: ga irinta nan
Tun kusan tsakiyar shekarar 2013, Masana tattalin arzikin kasa na kasa da kasa da hukumominsu, irin su Bankin Duniya da Asusun ba da lamuni na duniya, wato IMF da nan cikin gida suka yi ta gargadin mahukuntan kasashe, musamman wadanda suka dogara da kudaden arzikin man fetur ciki kuwa har da na, kasar nan, a […]
Tun kusan tsakiyar shekarar 2013, Masana tattalin arzikin kasa na kasa da kasa da hukumominsu, irin su Bankin Duniya da Asusun ba da lamuni na duniya, wato IMF da nan cikin gida suka yi ta gargadin mahukuntan kasashe, musamman wadanda suka dogara da kudaden arzikin man fetur ciki kuwa har da na, kasar nan, a kan cewa lallai su fara gagarumin shirin yadda za su iya tallafar tattalin arzikin kasashensu, kasancewar a `yan shekaru kadan masu zuwa za a fuskanci annobar faduwar farashin man fetur warwas a duniya baki daya. Ma`ana kasashe irin namu da suka dade suna cikin facaka da kudaden arzikin man fetur sasakai, to, lallai su fara shirye-shiryen yin takatsantsan, don fuskantar mawuyacin lokacin da ke tafe.
kasashen da suka ji wancan gargadi da kunnen basira, ba su yi wata-wata ba, wajen daura damara don tunkarar mawuyacin lokaci da yanzu ya bayyana a duniya baki daya, wadanda kuma suka dauki gargadin tamfar busa kamar kasar nan, suka kuma ci gaba da yin abin da suka ga dama, ga shi yau Allah Ya nuna mana lokacin, ta yadda kasashen da suka ki ji, to, yanzu suna ji ganin mawuyacin halin da aka samu kai.
Mu a nan kasar, mun yi rashin sa`ar a kalla abubuwa biyu zuwa uku, tun a lokacin da aka fara gargadin, har zuwa lokacin da ya bayyana karara.
Na daya, dama can mahukuntan kasar tun daga sama har kasa ba kasafai suke tsayawa su jajirce wajen aiwatar da dukkan wasu manufofin da za su taimaka wa tattalin arzikin kasar nan ba, saboda irin yadda son zuciya da sabawa da yin facaka da almubazzaranci da dukiyoyin al`umma shekaru aruru. Na biyu, harkokin cin hanci da rashawa da yin sama da fadi da dukiyar al`umma sun zama jini da tsoka tsakanin Mahukuntan da mabiya.
Na uku, shekarar 2015, ta kasance shekarar babban zaben kasar nan, ta yadda mahukunta da sauran `yan siyasa tun daga sama har kasa kowa kokari ya yi ta kowane hali ya ga cewa jam`iyyarsa ita ta lashe dukkan zabubbaukan da za a yi ko ana ha-maza-ha-mata, musamman gwamnatin tsakiya da a lokacin jam`iyyar PDP ke mulki da ita har tsawon shekaru 16. Don haka kasha kudi don cimma waccan buri, ba wani abu ba ne, ko da kuwa ba a yi tanadin kudin ba, don harkokin zabubbukan kamar yadda yanzu muke ji daga irin rahoton binciken da Hukumar da ke yaki da ta`annati da kudin jama`a, wato EFCC, musamman daga tabargazar da aka yi a gwamnatin tsakiya ta jam`iyyar PDP da kudin sayo makamai, har Dalar Amurka sama da biliyan biyu ($2biliyan), kudin da ake cewa, yanzu ma an gano sun kai Dalar Amurka biliyan 15, ($15biliyan). Baya ga irin biliyoyin Nairorin da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi da hukumomin gwamnatoci suka kashe a bayan fage da sunan samun nasarar zaben. A duk tsawon waccan lokaci, kuma babu wasu matakai da gwamnatocin suka dauka da sunan yadda za su tallafa wa tattalin arzikin don zuwan wannan mawuyacin lokaci, da yanzu ya riske mu kace-kace.
Mai karatu wasu daga cikin dalilan da suka sanya bayan kammala zabubbukan 2015, din ne da kuma irin gagarumin CANJIN da aka samu na kawar da Gwamnatin PDP, mai iko da gwamnatin tsakiya, dama wasu jihohi tunda aka fara mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, ya sanya yanzu ta bayyana karara cewa, kasar nan tana cikin mawuyacin matsalolin tattalin arzikin kasa. Samun CANJIN ya sanya Hukumar EFCC ta kara dukufa wajen bincike a harkokin gwamnatocin da suka shude da ma na wasu hukumominsu. Dama tun kafin a yi babban zaben ma`aikatan gwamnatin tarayya da na jihohi da hukumominsu, suna bin albashi da alwaus-alawus na watannin 3 zuwa 9. Wannan anobar kasa biyan albashi ta sanya a cikin watan Yulin bara gwamnatin tsakiya ta APC, ta umurci Babban Bankin kasa ya gano cewa jihohi 27, daga cikin 36, suna bukatar lamunin =N=662biliyan, don biyan albashi da alawus-alawus din ma`aikatansu, wanda daga bisani a watan Satumbar barar gwamnatin jihohi 19, suka karbi lamunin =N=222biliya, kuma har yanzu jihohin suna karbar tallafin.
Duk da wancan lamuni, da yake da ruwan kashi 9 cikin 100, kuma za su biya cikin shekaru 20, amma har yanzu gwamnatocin ba su fita daga wannan siradi na kasa biyan albashi ba, balle kuma su biya dimbin bashin Biliyoyin Naira da `yan kwangila da sauaran hukumomi na ciki da wajen kasar nan suke binsu, balle kuma ka yi batun za su iya yi wa mutanensu ayyukan raya kasar da suka yi musu alkawari.
A taron da kungiyar Gwamnonin kasar nan ta yi da Shugaban kasa Muhmmadu Buhari, a cikin makon jiya, ta tabbata har yanzu jihohi irin su Bauchi da Yobe da Imo da Nassarawa da Delta da Barno da Kaduna da Taraba da Oyo da Kogi da Kwara da Filato da Ogun da Binuwai, duk ba sa iya biyan albashin ma`aikatansu da na Hukumomin bada Ilmin bai daya wato SUBEB da na Majalisun kananan Hukumomi da na Sarakunan gargajiyarsu, abin da ya sanya wasu gwamnonin suka fara tunanin zaftare albashin masu rike da mukaman siyasa da kasha 50 cikin 100, da ma na ma`aikatansu da kashi 30 cikin 100, kamar yadda aka yi yarjejeniya a Jihar Imo tsakanin gwamnatin jihar da kungiyar kwadagon jihar, jihar da ma`aikatan ke bin albashin watanni uku, tun daga na Fabrairu.
Wannan ta sanya a wancan taron da gwamnonin suka yi, suka mika wa shugaban kasa wani kundi da suka ce suna kyautata zaton shi zai magance irin mawuyacin halin rashin kudin da suke ciki, kundin da ya kunshi irin yadda za a sake tsarin rabon kasafin kudin kasar nan. A yanzu dai gwamnatin tarayya na samun kashi 52, ya yin da jihohi ke samun kashi 26, kananan Hukumomi 774, kuma su na tashi da kashi 22 cikin 100. Gwmnonin sun kuma nemi a dakatar da cire musu basussukan da ake cire musu duk wata na wata daya, sannan kuma a duba yiwuwar dakatar da cire basussukan har na tsawon watanni 18. Sun kuma nemi a duba bukatar biyansu makudan kudin da suka yi wa gwamnatin tarayya wasu ayyukan raya kasa a jihohinsu, kamar su tituna da filayen jiragen sama, wanda tuni gwamnatin tarayya ta kafa Kwamitin da ke tantance mata irin wadancan ayyuka. Dukkkan wadannan bukatu na gwamnoni, shugaban kasa ya ba da tabbacin duba su, da alkawarin share musu su, kamar yadda aka ruwaito Malam Garba Shehu, daya daga cikin Kakakin Shugaba Buhari yana fadi.
Tabbas, gwmnatocin jihohi suna matukar bukatar tallafi ko don ma yadda za su rinka biyan albashin ma`aikatansu a kan kari, amma su ma suna bukatar su tashi tsaye su ga cewa sun fara yaki da cin hanci da rashawa a cikin jihohinsu, don kwato irin dukiyoyin da wadanda suka gada da `yan kwangilarsu ko na kusa da su, suka yi sama da fadi ko almubazzaranci da su kamar yadda gwamnati tarayya take yi. Kazalika akwai bukatar su rage facaka da sama da fadi da kudin jama`a da suke yi yanzu a kan abubuwan da ba su dace ba, sannan kuma su nuna da gaske suke wajen ganin suna inganta hanyoyin tara kudin shigarsu na cikin gida, tare da rungumar ayyukan noma da hako ma`adanai da aka yi ittifakin su kadai suka rage na daga hanyoyin da za a ceto tattalin arzikin kasar nan na din-din-din. Yanzu ya kamata kuma su fara.