Matsalar tsaro a Arewa maso Gabas

Hare-hare da kisan mummuke da ke ci gaba da aukuwa a Jihar Borno abin Allah wadai dashi ne. Domin kuwa hare-haren sun jefa mutanen garin cikin halin kaka nika yi na rashin abinci da ruwan sha  da sauransu, baya ga asarar rayuka da dukiyoyi da akayi. Haka zalika, anyi garkuwa da yara mata 20, kuma […]

Matsalar tsaro a Arewa maso Gabas
Matsalar tsaro a Arewa maso Gabas

Hare-hare da kisan mummuke da ke ci gaba da aukuwa a Jihar Borno abin Allah wadai dashi ne. Domin kuwa hare-haren sun jefa mutanen garin cikin halin kaka nika yi na rashin abinci da ruwan sha  da sauransu, baya ga asarar rayuka da dukiyoyi da akayi. Haka zalika, anyi garkuwa da yara mata 20, kuma babu labarinsu, balle asan halin da suke ciki. Har yanzu babu wani kokari da gwamnatin Najeriya da sauran kungiyoyi masu rajin kare hakkin dan Adama da suka yi, don ganin an ceto wadannan yara.
Wannan danyen aiki da ya auku a garuruwan Bama da Izge da sauran sassa na Jihar Borno ya kai intaha, domin kuwa ya maida yara da dama marayu, wasu matan sun rasa mazajensu, a wani bangaren kuma maza sun rasa matayensu da ‘ya’yansu. Iyaye sun koma bizne yaransu sakamakon wannan tashin hankali, mai makon yaran su rika bizne iyayen nasu.
Wani abin takaici shi ne yadda gwamnatin tarayya ta nuna halin ko in-kula ga mummunar ta’adin da ke faruwa a Borno.  Labarai sun ruwaito Gwamna Kashim Shettima na Borno na cewa makaman da ‘yan ta’addan ke amfani da su sun fi wanda Jami’an tsaro da aka tura garin don samar da zaman lafiya inganci, amma sai gwamnati ta karyata wannan magana da gwamnan ya yi, mai makon a kalli bayanan nasa da idon basira. Shakka babu, ya dace a ce jami’an tsaron da aka tura suna da isassun kayan aiki kuma masu inganci.
Yanzu ya fito fili karara, musamman ma ganin yadda Gwamnatin Najeriya karkashin Goodluck Jonathan ta ki cewa uffan kan lamarin, da kuma halin ko oho da sauran kungiyoyi na cikin gida da na waje suka nuna cewa sam wannan tashin hankali da ke faruwa bai damesu ba. Domin kuwa, yanzu dai ran dan Adam bai da wani muhimmanci a Najeriya sakamakon irin kisan gillar da ake yi wa al’umma ba dare ba rana. Yana da wuya a shafe kwana bakwai ba a ji labarin rasa rayuka ba a Arewacin Najeriya. Yau ka ji an ce an kai hari a Damaturu ko Maiduguri, gobe ka ji an yi wani rikicin a Jos tsakanin wadanda ke kiran kansu ‘yan asalin gari da wadansa suke yi wa lakabin ‘baki.’
A gaskiya dukkan wanda yasan irin halin da wadannan mutane ke ciki ya san dole a tausaya masu. Ya zama dole akan hukumomi su samar da cikakken tsaro a yankin Arewa maso gabas tare da kare rayukan al’ummarsu, wanda hakan ne zai kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma ci gaba.
Babbar ayar tambaya a nan itace, wai shin su waye ke kashe mutane a Jihar Barno ba gaira ba dalili? Meye hujjarsu na wannan kisa? Mene ne suke bukata? Wane hobbasa Gwamnatin Najeriya ke yi na ganin an kawo karshen wannan bala’i da ya daidaita garin Maiduguri da sauran sassan Arewacin Najeriya. Suwa ke samar wa ‘yan ta’addan makamai wanda ya fi karfin wanda jami’an tsaro ke amfani da su? kananan yara 20 ’yan makaranta da aka sace wane hali suke ciki? Ya iyayen wadannan yara da ’yan uwansu suke ji a yanzu? Yaushe zaman lafiya zai dawo a Maiduguri da Arewacin Najeriya? Wadannan kadan ne daga dimbin tambayoyi da ’yan Najeriya ya dace su samu amsarsu daga gwamnati, kuma ba za su bar tambaya ba, har sai an ba su gamsassun amsoshi. Ya zama dole akan dukkan mai son ci gaban kasar nan ya kalubalanci wannan gwamnati kan rikon sakainar kashin da take yi wa fannin tsaro a Najeriya.
Wani abin haushi da daure kai, shi ne yadda a tsawon sama da awa daya da mintoci da Shugaban kasa Goodluck ya kwashe yana hira da manema labarai kai tsaye daga fadarsa a yammacin Litinin da ta gabata, babu wata kalma ta alhini da juyayi kan yara ‘yan makaranta 20 da aka yi garkuwa da su a jihar Barno daga bakin Goodluck, sai ma dai barazanar janye sojojin da ke Maidugurin ya yi, Inda yake cewa wai idan gwamna Kashim yana ganin sojoji basa aiki a Barno to ya shaida masa shi kuma zai janyesu na tsawon wata daya, sai a ga ko gwamnan zai iya rayuwa a gidan gwamnati. Wannan irin magana ba ta kamata ko kadan ta fito daga bakin Shugaba Jonathan ba. Shugaban kasa ya yi maganganun da ba su dace ba a wannan ganawa da ya yi, inda a kaikaice yake goyon bayan tsagerun Neja-Dalta, domin kuwa a cewarsa basa kisan kan mai uwa da wabi kamar ’yan boko haram.
Da alamun tsugune ba ta kare ba, domin wannan hirar da shugaban kasa ya yi ba ta nuna cewa ya shirya yin wani abin a zo, a gani dangane da matsalar tsaro da ta addabi Arewa maso gabas ba.
Zai yi kyau idan shugaba Goodluck Jonathan da sauran masu ruwa da tsaki suka dauki matakan gaggawa wajen kawo karshen wadannan kashe-kashe da tashin hankula da ke faruwa a Najeriya, tun kafin wankin hula ya kai su dare. Ya kamata Shugaba Jonathan yasan cewa wannan matsala da ke addabar yankin Arewa maso Gabas ba wai matsala ce ta yankin kawai ba, matsala ce da ta shafi kasa baki daya. Yin biris da nuna halin ko in kula, ba za su haifar wa kasar da mai ido ba. Munga yadda kasar Riwanda da Afghanistan da sauransu suke a yau. Shin haka ake so tamu kasar ta koma? Don haka lokaci ya yi da za a dakatar da hare-hare, tare da tada bama-bamai a Borno. Dole a dakatar da zubda jinin al’ummar yankin Arewa maso gabas. Lokaci ya yi da za a daina kashe al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba. Lokaci yayi da kowa zai yi tofin ala tsine ga dukkan mai hannu a wannan bala’i dake addabar Arewa maso gabas da kasa baki daya. Lokaci yayi da kowa zai fito ya bada tasa gudunmuwa don ganin kanan nan yara yan makaranta 20 da aka yi garkuwa da su sun fito. Babu wata kasa da za ta ci gaba, ba tare da al’ummarta suna zaune lafiya ba. Kuma zaman lafiya shi ke kara habaka tattalin arziki. Allah Ya kawo mana zaman lafiya a Maiduguri da kasa baki daya.
Muntaka Abdul-Hadi Dabo, a iya tuntubarsa ta i-mail dinsa: [email protected]

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno