Matsalar tsaro a Najeriya
Matsalar tsaro a Najeriya sai daukar sabon salo take yi, duk da cewa matsalar ba sabon abu ba ne, to, amma yadda ake maganin lamarin kai kasan bai isa ba.. Yayin da hankali ya koma kan Boko Haram, agefe guda sai ga matsafa da ‘yan kungiyar asiri da ‘yan fashi da makami a manyan tituna […]
Matsalar tsaro a Najeriya sai daukar sabon salo take yi, duk da cewa matsalar ba sabon abu ba ne, to, amma yadda ake maganin lamarin kai kasan bai isa ba.. Yayin da hankali ya koma kan Boko Haram, agefe guda sai ga matsafa da ‘yan kungiyar asiri da ‘yan fashi da makami a manyan tituna da barayin shanu da‘yan daba da ‘yan tarzoma da rikicin addini da kabilanci, sai karuwa suke ko’ina a birane da kauyuka.
A dazukan Zamfara da Katsina da Kaduna da dajin Falgore dankare suke cike da barayi da masu kwace shanun jama’a da kashe su. Ga garkuwa da mutane, inda kwanan nan kusan kauyawa 40 aka sace a wasu kauyukan Jihar Zamfara, abin da ya kai ga musaya tsakanin barayin da Gwamnatin Jihar Zamfara. Rahotanni sun nuna cewa, sai da aka bayar da sama da saniya 300 kafin a fanso kauyawan. Wannnan abin bantsoro ne, domin yana nuna karara cewa ‘yan fashin shanun nan tamkar sun gagari kundila. Amincewa da a kai da su har ta kai masanya, kamar an halatta ayyukansu ne. Abin tambaya a nan, shin wannan shi ne karshen satar shanu da kisan mutane babu gaira, babu dalili da ke faruwa a Jihar Zamfara da wasu jihohin Arewa maso Yamma?
Wani abin da ke daure mana kai yadda wasu jami’an gwamnati ke fitowa fili a kafafen yada labarai suna kokarin kare makasan! Maganganun irin wadannan shugabannin na jefa alamar tambaya cewa, su wane ne barayin shanun, su wane ne ba barayin ba? Mutanen da ke yawo a babura sabe da bindigogi kirar AK 47, su kuma ba jami’an tsaro ba, to, yaya sunan su? Su wane ne ke kai hare-hare bisa babura a kauyukan Zamfara da sauran su? Fulani ne ko ko wasu barayin shanun ne da ba a san da su ba? Kuma shanu sama da dubu 200 da Gwamnatin Zamfara ta yi amfani da su wajen fanso mutanenta daga ina aka samo su? Ko kuwa sawo su aka yi? Kuma tukwici ne ko kudin fansa ne?
Baya ga barayin shanu da masu satar jama’a, akwai ‘yan fashi da makami a manyan titunanmu. Misali tsakanin Gwambe zuwa Numan, ana yawan tare bayin Allah, ana yi musu fashi. Sai yaushe za a kawo karshen wannan masifa? Sauran hanyoyi da ba dare ba rana ana fashi kan su me ya sa abin ya gagari kundila? Nawa ne kasafin kudin tsaro, kuma nawa a zahirin gaskiya ke tafiya kan tsaron?
Domin gano maslaha, yana da kyau shugabannin Najeriya su fahimci cewa duk wani shafe-shafe ba zai kawo tsaro a Najeriya ba, musamman a Arewacin Najeriya. Muna kira da a fasa duk dazukan nan, da aka san na cike da barayi, a kuma zuba jami’an tsaro, su zauna ciki dindindin.
Dokta Aliyu Muri ya bayar da shawara, cewa, a saya wa jami’an babura da rakumma su ci gaba da sintiri (patrol) a dazukan. Mun gaji da sharar daji, domin ko an share an tafi, to za su dawo. Kazalika a inganta tsaron iyakokin Najeriya, a zuba sojoji, domin kwastan kawai ba za su iya kare iyakokinmu ba, ciki har da ire-iren barauniyar hanya da suka cika iyakokinmu. Kundin tsarin mulkinmu, ya bayar da damar kirkiro da ‘yan sandan sarauniya. Kowa ya san ‘yan sandan Najeriya sun yi kadan, duk kuwa da dubu 10 da za a dauka. Domin muna bukatar sama da ‘yan sanda miliyan guda idan muna son kanmu da lafiya. Tunda sashe na 10 na dokar ‘yan sanda ta amince da cewa a lokaci na musamman, kwamishinan ‘yan sanda na jiha zai iya daukar ‘yan sandan sarauniya,wadanda za a ba su horo kamar na sauran ‘yan sanda. Su dai ‘yan sandan sarauniya, ana daukar ‘yan asalin al’ummar wurin ne, kuma za a dinga biyansu albashi, sannan karkashin gwamnatin tarayya suke. Don haka kowace karamar hukuma za a iya daukar adadin ‘yan sanda guda dubu, kuma a dinga biyan su alawus din dubu 30 duk karshen wata. Mun tabbatar wadannan ‘yan sanda za su rage gibin ‘yan sanda da muke fama da su. Kazalika, tunda ‘yan gari za a dauka, to za su taimaka wajen dakile laifuka daban-daban, ciki har da garkuwa da mutane da safara da shan miyagun kwayoyi da tashe-tashen hankula da makamantan su.
Tsarin tsaron Najeriya ya mayar da ‘yan sanda sun tare a birane, yayin da kauyukanmu babu tsaro. Dole in ana son a daina kwasar kauyawa ana kai su Sambisa da sauran mafakar ‘yan ta’adda ana mayar da su ‘yan kunar bakin wake, ya zama kauyukanmu na da tsaro. Yanzu abin kunya ne gari kamar Dankama, amma babu babbar tashar ‘yan sanda(Dibision), wai sai dan karamin ofishi, wato ‘outstation’ a Turance. To idan Dankama ba Police Dibision ya batun Dankaba da Lafiyaru da Jihatu da Dankunama da dimbin kayukan Najeriya?
Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, shi ne Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka a Najeriya 08165270879