Matsalar tsaro: An kaddamar da shirin tattaunawa da jama’a
Gwamnati ta kaddamar da tattaunawa da jama’a domin kawo karshen matsalolin tsaro
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin tattaunawa da jama’a domin kawo karshen tayar da kayar baya da ayyukan ‘yan bindiga da rikice-rikice da sauran matsalolin tsaro na cikin gida.
Yayin bude taron a Maiduguri, Jihar Borno, Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ta bakin kakakinsa ya ce gwamnati na neman shawarwarin masana domin samun nasara a kokarin, wanda ya bukaci ‘yan kasa su mara wa baya.
“Wasu kasashe sun fuskanc irin wadannan matsaloli kuma suka yi nasarar magance su.
“Muma haka za mu yi, babu abin da zai hana; amma kain mu yi nasara muna bukatar goyon bayan jam’a.
“Ya kamata mu fahimci cewa batun samar da tsaro da tsarinsa abu ne mai sarkakiya.
“A sama sojoji ne daga na sai ‘yan sanda sai kuma sauran hukumomin tsasro.
“Masu dauka da kuma tallafa wa tsarin tsaron kuma su ne ‘yan kasa wadanda daga cikinsu jami’an tsaron suke”, inji shi.
Ya jaddada cewa al’amarin samar da tsaro kan yi nasara ne idan ‘yan kasa na samar da bayanai tare da nuna goyon baya ga jami’an tsaro.
“Babu wata hukumar tsaro da za ta taba yin nasara muddin ba da samu goyon bayan jama’a ba.
“‘Yan tayar da kayar baya da sauran masu aika manyan laifuka mutane ne ba fatalwa ba, duk da cewa su ne ‘yan tsiraru.
“Ba za su iya zurewa ba idan har jama’a suka hada kai suka kuma jajirce ta hanyar bayar da muhimmanci ga al’amarin tsaro”, inji ministan.
A nasa bangaren Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayar da tabbacin cewa jama’ar jihar za su kara ba wa Gwamnatin Tarayya goyon baya domin ganin an samu tsaro da aminci a fadin jihar.