Matsalar tsaro: Buhari ba zai yi murabus ba- Gwamanatin Tarayya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ba zai yi murabus  daga mukaminsa ba, saboda kalubalen  tsaron kasar. Ministan yada labarai da al’adun Najeriya Lai Muhammed, ne sanar da hakan ranar Alhamis yayin da yake tattaunawa da manema labarai. Ministan ya mayar da martanin ne game da yadda wasu ke yin kira ga Shugaban ya yi murabus  saboda […]

Matsalar tsaro: Buhari ba zai yi murabus ba- Gwamanatin Tarayya

Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ba zai yi murabus  daga mukaminsa ba, saboda kalubalen  tsaron kasar.

Ministan yada labarai da al’adun Najeriya Lai Muhammed, ne sanar da hakan ranar Alhamis yayin da yake tattaunawa da manema labarai.

Ministan ya mayar da martanin ne game da yadda wasu ke yin kira ga Shugaban ya yi murabus  saboda tabarbarewar tsaro a kasar. “Shugaban kasar ba zai yi murabus ba,  har sai ya cika alkawarin da ya yi wa ‘yan Najeriya na yi masu aiki zuwa karshen wa’adin mulkinsa zuwa watan Mayu na shekarar 2023.” In ji Ministan.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa