Matsalar tsaro: Buhari ne ya dace ya shugabanci kasar nan -Naja’atu Muhammad
Hajiya Naja’atu Bala Muhammad wata fitacciyar ‘yar siyasa ce da ke kusa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhar, a wannan hirar da Aminiya ta yi da ita ta yi bayanin dalilin da take ganin Janar Buhari ne ya fi dacewa da shugabancin kasar nan a halin da take ciki. Ga […]

Hajiya Naja’atu Bala Muhammad wata fitacciyar ‘yar siyasa ce da ke kusa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhar, a wannan hirar da Aminiya ta yi da ita ta yi bayanin dalilin da take ganin Janar Buhari ne ya fi dacewa da shugabancin kasar nan a halin da take ciki. Ga dai yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Mene ne alakkarki da tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari?
Naja’astu: Ni ce mataimakiyar direkta na kwamitin sadarwa na Janar din.
Aminiya: Wannan shi ne karo na hudu da Buhari zai yi takara, kina ganin a wannan karon zai kai labari kuwa?
Naja’atu: Eh to zai kai da karfin Allah, saboda yanzu kasar nan ba kamar da ba ce. A cikin karo 3 da ya yi Najeriya ba ta tabarbare haka ba, kuma ba ta shiga halin yaki ba. A duk duniya inda ake yaki; irin su Ingila da Amurka, watau duk lokacin da ake cikin rikici sai su dauki tsohon Janar dinsu su ba shi shugaban kasa domin ya shugabanci yakin. Ina ganin a Najeriya ma wannan lokacin ya yi. Shi Janar Muhammadu Buhari kowa ya san shi a maganar murkushe yan tawaye. Don haka da shi aka yi yakin Biyafara suka je suka murkushe yankin Biyafara suka dawo da ita cikin kasa. Shi ne kuma ya jagoranci raka ‘yan Chadi sai da ya kai su wajen kilomita 40 a cikin Chadi, a lokacin da suke zuwa suna mamaye mana Najeriya kamar yadda suke yi yanzu, su yi sata su koma garinsu. Kin ga yana da masaniya a wannan harkar kuma yana da masaniya a kan harkar rashawa da cin hanci. Kowa ya san lokacin da ya yi mulki, ya san yadda ya yi yaki da rashawa da cin hanci, domin sune suke kassara kasa.
Kudin da yakamata yanzu a dauka a bai wa sojoji a sayo musu makamai da kayan yaki da yakamata a koyar da su yadda ake yaki, yanzu shi ne aka yi sama da fadi da shi, shi ya sa kasa ta zama abin da ta zama. Wannan shi ne yake karya tattalin arzikin kasa. Ke nan idan Allah Ya taimake mu ya yaki wannan ta’addacin da rashawa da cin hanci ina tabbatar miki komai zai fi na baya. Kuma ga walwala ma ya yi wuya. Da yake ‘yan Najeriya ma sun fahimci cewa wadannan abubuwan gaba dayansu Jonathan ya kasa yi. Su da kansu jikinsu ya gaya musu. A da mutanen Arewa ne baki dayansu suka fi zaben Janar Muhammadu Buhari, amma yanzu muna da kudu maso yamma da kudu maso kudu da yawa, muna sa ran za mu samu kuri’u sosai. Muna da Arewa ta tsakiya. Misali idan kika dauki jihohin Binuwai da Filato sune wadanda ba su ba mu kuri’a yadda yakamata, amma yanzu kowa ya fahimta. An yi amfani da addini, an yi wa mutane karya, mutane sun karkashe kansu, ba su kuma samu ribar komai ba. Saboda haka yanzu ina jin kowa ya gane . Ba zai yiwu har abada ana yi wa mutane karya ana yaudaransu ba. Akwai ranar da Allah zai bude musu ido, yanzu kowa ya gane cewa gara a rabu da wannan bala’in ta gwamnatin PDP.
Aminiya: Kin yarda da ofishin matar Shugaban kasa?
Naja’atu: Ya zan yi in yarda da abin da doka ba ta tanadinsa ba? Doka ba ta yarda a yi ba, kamar yadda Janar Buhari ya ce, kuma haka din ne, amma matan shugaban kasa tana da izinin da za ta taimaka wa al’umma. Misali; ita matar Janar Buhari na gani kwanakin baya tana tattara sako da taimako ga wadanda suke ‘yan gudun hijira na Borno. Ai wannan ai ba mulki suke yi ba. Amma mutum ko a ina ya samu kansa in dai mai agazawa ne zai agaza,ba wai sai kana da ofis ba da za a ce na matar shugaban kasa sannan za ka taimaka. Gaskiya a dokance babu, amma wannan bai hana matar shugaban kasa ta taimaka musu a harkar kamfen ba. Bai hana ta nemo masa taimako na matasa da mata ba. Kuma bai hana ta shiga harkokin siyasa ba. To idan bai hana ta shiga harkokin siyasa ba, yadda za a taimaka a ci zabe ba, don me kuma za a ce ba za ta bada agaji ba kamar yadda yakamata?
Aminiya: Wane kokari kuke yi don ganin magoya bayanku sun karbi katin zabe na dindindin?
Naja’atu: A gaskiya ana kokari a jam’iyyarmu, amma ba laifin mutane ba ne da ba su karbi katinsu ba daga wurin hukumar zabe (INEC ) ba, ba mu san me za ta yi da kuri’a kusan miliyan 15 ba. Don ba na mantawa, a shekarar 2003 mun san cewa Janar Obasanjo haka kawai da sanyin safiya ba a fito da sakamako ba ya ce yana da kuri’a miliyan 8. Miliyan 8 din nan aka rasa daga ina suka fito.
Abin da muke zato shi ne, hukumar INEC idan ba ta bada wadannan kuri’u miliyan 15 ba, to su ma abin da za su yi ke nan, da sanyin safiya kafin a gama zabe su ce Jonathan yana da kuri’a miliyan 15. Idan har ba su fito sun bai wa mutane katin zabe na dindindin ba to mun san abin da za su yi ke nan. Amma dole kuma majalisa ta tabbatar da cewa hukumar INEC idan ma ba za ta iya bayar da katin dindindin ba a bar mutum katin da yake da shi ya kada kuri’a da shi. Babu dalilin da za a ce kada mutane su kada kuri’a, domin ba laifinsu ba ne, laifin hukumar zabe ne.
Aminiya: Kina ganin yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan takara suka kulla za ta yi aiki kuwa?
Naja’atu: Ai wannnan ba yarjejeniya ce ta zaman lafiya ba. Cewa akayi kowanne ya fada wa magoya bayansa don Allah kada a yi rigima. Ya kuma danganta da yadda gwamnati ta so. Dama ‘yan sanda da sojoji suna yin ta’addanci su da kansu. Kuma kin ga a karkashin gwamnatin tarayya suke, watau a karkashin Jonathan. Saboda haka shi ne yakamata ya ja musu birki. Kuma bai kamata a ce soja ya fito wajen zabe ba, babu dalilin da zai sa shi ya fito. Amma yanzu cewa ake yi da soja da kwastam duk za su fito. Me za su zo su yi? Mene ne amfanin kwastam a wajen harkar zabe? So suke su musguna wa jama’a, su zauna su yi magudi.
Domin magudi na daukar salo iri-iri. Yanzu ma shi ya sa aka dauko manya-manyan ‘yan ta’addan aka kai su Lagos. Akwai kamishina Mbu wanda ya dinga uzzura wa mutane a jihar Ribas, yanzu an dauke shi an kai shi Legas. Da daya kamishinan wanda an san shi kotu na nemansu a maganar sace mutane don a bada kudi. Har yanzu suna da kara a kotu wanda har yanzu ba a kare ba. Kotu ma tana nemansa, amma an yi masa karin girma kuma yanzu yana Legas. To me ya je yi?
Aminiya: Kin gamsu da yadda ‘yan takara suke gudanar da yakin neman zabensu a halin yanzu?
Naja’atu: Alhamdulillahi! Ni dai na gode wa Ubangiji a yadda muke yin namu. Allah Ya kawo mana al’umma suna tururuwa suna binmu. Kuma suna bin dan takara Janar Muhammadu Buhari, saboda haka ba abin da za mu ce wa Allah sai godiya. Kuma muna fata muna kuma rokan Allah Ya tabbatar mana da tururuwan kuri’a a cikin zaben.
Aminiya: Wane kira za ki yi wa ‘yan takara da magoya bayansu?
Naja’atu: Kiran kawai da zan yi wa magoya baya shi ne, kowa ya kwantar da hankalinsa kuma su fito su yi zabe a ranar zabe, shi ne kawai zai tabbatar da soyayyarsu ga Janar Buhari. Kuma kullum su tuna, kamar yadda Janar yake fada, ba don jin dadin cigaban kansa ba ne yake neman shugaban kasa, don gyaran kasar ne kuma don jin dadin al’umma. Al’umma idan suka kwana da sanin cewa kansu suke wa wannan yakin,to za su fito za su yi zabe kuma za su kada kuri’arsu kuma za su kare kuri’arsu.