Matsalar tsaro: Gwamnonin Arewa za su yi taro da na Nijar
Gwamnonin za su yi taro don tattauna matsalar tsaro da ta shafi yankinsu.
Gwamnonin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya za su yi wani taro da gwamnonin jihohin Jamhuriyar Nijar da suka hada iyaka domin tattauna batun matsalar tsaro a yankinsu.
Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, shi ne ya sanar da hakan bayan ziyarar da ya kai Jihar Maradi ta Jamhuriyar Nijar, inda ’yan gudun hijirar da suka tsere daga Najeriya ke zama.
- ’Yan sanda sun kwato mutum 187 daga hannun ’yan bindigar Zamfara
- An ceto mutum 47 a gidan mari a Kano
Tambuwal, ya ce za su gudanar da taron ne tare da gwamnonin jihohin Dosso, Tahwa da kuma Maradi na Jamhuriyar Nijar.
Daga cikin gwamnonin Najeriya da za su halarci taron har da takwarorinsa na jihohin Kaduna, Zamfara da Katsina.
Gwamnan ya bayyana cewa abun takaici ne yadda matsalar rashin tsaro ta dabaibaye yankin nasu, duk kuwa da cewa suna yin iya bakin kokarinsu don samar da zaman lafiya.
Tambuwal ya kuma mika sakon godiyar Shugaba Buhari ga Shugaba Mohammed Bazoum, a kan karamcin da kasarsa ta yi wa Najeriya na kula da dubban ’yan gudun hijirar da suka samu matsuguni a Nijar.
Najeriya da Jamhuriyar Nijar na ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan ta’adda daga sassa daban-daban, lamarin da ke salwantar da rayuka da dukiyoyin al’umma bi-la-adadin.