Matsalar Tsaro: Ku sayi makamai don kare kanku — Sarkin Argungun
Sarkin ya kuma buƙaci al’ummomin da ke cikin masarautar da su kasance masu sanya ido tare da ɗaukar matakan kariya da wuri a kan ’yan ta’adda da sauran ɓata-gari da galibi ke mamaye yankunan.
Sarkin Argungu, Alhaji Muhammad Samaila Mera ya yi kira ga talakawansa da su mallaki makamai ta hanyar da doka ta amince da ita domin kare al’ummominsu daga hare-haren ’yan bindiga da ba su ƙauƙautawa ba.
Ya kuma buƙaci al’ummomin da ke cikin masarautar da su kasance masu sanya ido tare da ɗaukar matakan kariya da wuri a kan ’yan ta’adda da sauran ɓata-gari da galibi ke mamaye yankunan.
- Mai juna biyu na wata 8 ta shigar da ƙarar neman saki
- Mutum 4 sun mutu a hatsarin jirgin sama a Croatia
Sarkin ya yi wannan kiran ne yayin wani taro da ya yi da Hakiman gundumomi, masu Unguwanni da Dagatai a fadarsa da ke Argungu.
Ya ƙara da cewa, kamata ya yi al’ummomi su yi tunanin tara kuɗaɗe cikin haɗin gwiwa domin sayen makaman da doka ta amince da su don kare kai.
“Idan kuka mallaki irin waɗannan makamai ta hanyar doka, ku tabbatar ’yan fashin dajin sun sani cewa al’ummaku suna da kayan da za su iya kare kansu. Wannan kaɗai zai iya zama riga-kafi kuma zai hana su kawo hari,” in ji shi.
Ya jaddada cewa, addinin Musulunci ba ya kwaɗaitar da mutane su zauna a matsayin gajiyayyu a lokacin da ake fuskantar tashin hankali.
“Bai dace ba ga Musulmi ya zauna ya zuba ido yayin da masu laifi ke kashe mutane, suna garkuwa da ’yan ƙasa marasa laifi, kuma suna yi wa matanmu fyaɗe. Ku kasance a shirye don kare kanku, iyalanku da al’ummominku daga kowane irin hari,” in ji Sarkin.
Basaraken ya nuna ɓacin ransa kan yadda al’ummomi da dama suka zama masu rauni saboda rashin kayan kariya.
Ya ce, “Idan ’yan fashin daji suka kawo muku hari, sai ka ga mutane suna gudu, har da masu unguwanni. Wannan yana faruwa ne saboda al’ummomin ba su da isassun hanyoyin kare kai.”
Ya bayyana cewa, ba ya goyon bayan al’ummomi zuwa ga ɗaukar doka a hannunsu ko tsunduma cikin ayyukan ta’addanci ba, illa dai yana fafutukar neman kariya ta halal ne, inda ya lura cewa ƙalubalen tsaron ya zama abin da ya fi ƙarfin jami’an tsaro kaɗai su iya magance shi.
Ya ce, abin takaici ne yadda al’ummomi ke ci gaba da rasa rayuka ba tare da wani yunƙuri na nuna tirjiya ba, yayin da ya yi gargaɗi game da rikicin ƙabilanci da kuma ƙarƙashe mutane ba tare da bin ƙa’idar doka ba.
Sarkin ya yi gargadin cewa ba zai goyi bayan duk wani da ke ɗauke da makami da nufin kai hari ga sauran ƙabilu ko shiga cikin kisan ba ƙauƙautawa wanda ya saɓa wa doka ba.