Matsalar tsaro: Masarautar Daura ta yi kwarya-kwaryar garambawul
Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Frouk, ya yi garanbawul a majalisar masarautar don inganta tsaro. Babban jami’in yada labarai na masarautar, Malam Usman Ibrahim, shi ne ya tabbatar wa Kamfanmin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) hakan a fadar Sarkin ranar Laraba. Malam usman ya ce an daga likkafar Sarkin Tsaftar Daura, Alhaji Lawal Usman, zuwa […]
Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Frouk, ya yi garanbawul a majalisar masarautar don inganta tsaro.
Babban jami’in yada labarai na masarautar, Malam Usman Ibrahim, shi ne ya tabbatar wa Kamfanmin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) hakan a fadar Sarkin ranar Laraba.
Malam usman ya ce an daga likkafar Sarkin Tsaftar Daura, Alhaji Lawal Usman, zuwa Kauran Daura, wanda hakan ya mayar da shi daya daga cikin hakimai masu nada Sarki a masarautar, yayin da shi kuma Alhaji Yusuf Nalado, wanda a da shi ne Sarkin Sudan, yanzu ya koma Babban Mai Ba da Shawara ga Sarki.
A cewar kakakin masarautar, Sarkin na Daura ya ja hankalin sabbin hakiman da aka daga likkafar tasu da su kara jajircewa wajen tabbatar da adalci da zaman lafiya a masarautar.
Sarkin ya kuma ja hankalin al’ummar yankin da su ci gaba da yi wa Masarautar da ma kasa baki daya addu’a musamman a wannan mawuyacin halin da take ciki na matsalar tsaro.
Ya kuma tunatar da mutanensa wani Hadisi a kan muhimmancin yafiya da hakuri.
“Mai imani na gaskiya shi ne wanda mutane suka kubuta daga sharrinsa; wanda idan an masa sharri zai mayar da alheri”, inji shi.
Jihar Katsina dai ta yi ta fama da matsalar tsaro sakamakon hare-haren ’yan bindiga, har ta kai aka fara nuna wa masu rike da mukaman gargajiya yatsa kan cewa suna da hannu a ciki.
Ko a ranar Litinin sai da mai taimaka wa Shugaba Buhari kan harkar yada labarai, Malam Garba Shehu, ya yi zargin cewa akwai masu rike da sarautar gargajiya a jihar da ke taimaka wa ’yan bindigar tserewa idan jami’an tsaro suka fatattako su.