Matsalar tsaro: Samar da ’yan sandan jihohi ne mafita – Gwamnan Neja
Kwanan baya Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya kai ziyara Amurka kuma ya tattauna da wakilinmu a birnin Washinton DC kan batutuwa daban-daban. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Ta yaya wannan taron da kuka yi zai shafi mutanen jihar Neja?Lallai mun tattauna kan batutuwa da dama, wanda kuma tsaro shi ne kan […]

Kwanan baya Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya kai ziyara Amurka kuma ya tattauna da wakilinmu a birnin Washinton DC kan batutuwa daban-daban. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ta yaya wannan taron da kuka yi zai shafi mutanen jihar Neja?
Lallai mun tattauna kan batutuwa da dama, wanda kuma tsaro shi ne kan gaba, kuma an fi magana ne a kan mutanen jihar Borno, inda nan ne ake samun rikicin ‘yan Boko Haram, da kuma mutanen da suka yi hijira daga gidajensu suka koma sansanin ‘yan gudun hijira, wadanda kuma gwamnan jihar Borno ya yi bayanin halin da suke ciki, musamman na irin halin yunwar da mutane ke fuskanta a wadannan sansanonin da kuma irin taimakon da suke bukata.
Kuma an yi maganar tsaro da ya shafi arewacin Najeriya gaba daya, misali, ni bayanin da na yi a kan barayin da ke satar mutane da masu satar shanu ne. A gaskiya mun tattauna sosai game da tsaro, domin duk al’ummar da ba ta da tsaro to babu yadda za a yi abubuwa su tafi daidai. Kuma kowane gwamna ya samu dama ya yi bayanin irin hali tsaron da jihar take ciki.
Aminiya: Wane irin taimako ne gwamnatin Amurka za ta ba ku?
Mun zauna da sakataren harkoki wajen Amurka John Kerry da kuma Susan Rice. Shi Kerry bayan mun gama tattaunawa da shi ya bukace mu da mu mika bukatunmu a rubuce na iri taimakon da muke so su yi muna.
Aminiya: A jihar Neja me kake yi domin inganta kudin shiga, kuma me gwamnatinka tayi daga lokacin da ka karbi ragamar mulki kawo yanzun?
Allah Ya sa mun shigo a lokaci da babu kudi, gaskiya a jihar Neja ban tsammanin an taba kaiwa lokacin da har albashi yana gagara ba, sai wannan karon, domin a wasu kwanakin da suka gabata mun samu matsalar biyan albashi, amma Allah cikin ikonSa Ya sa aka warware. Amma na tabbata har ga Allah duk mai nema yana tare da samu kuma muna iyakar kokarinmu, domin komi a jihar ya dan dakata, abubuwa da yawa sun lalace, makarantun sun lalace, daga firamare har zuwa sakandare, inda za ka ga yara na daukar karatu a kasa ko kuma suna kwance a kasa ko wurin cin abinci kamar na dabbobi. Wannan ya sa muka bai wa ilmi muhimmaci a cikin abin da muke fata mu yi, don haka yanzu mun fara gyaran makarantu, musammam makarantun kwana. Ina fata lokacin da za a kammala aikin gyaran wadannan makarantun to duk wanda ya kai ‘ya’yan sa makarantar kudi sai ya fidda su ya dawo da su na gwamnati.
Aminiya: Kana ganin za ka iya gyara daukacin makarantun kwana da ke cikin jihar har su zama abin alfahari?
Sai dai inyi bakin kokarina, fata shi ne wanda zai karba daga gare ni ya dora, domin abin da yawa. matsalolin da ke kasa na makarantu da sauran abubuwa Allah Ya yi yawa da su.
Aminiya: Za ku karbi wani ne daga iyayen yara domin tallafa wa fannin ilmi?
Yanzu haka dai na kafa kwamitin da zai samar muna yadda za a samu kudin shiga kuma ba zan sanya musu baki ba, zan barsu suyi aikinsu, amma batun sanya haraji ga iyayen yara zai yi wuya, domin ko a nan Amurka da muka tattauna mun yi maganar ilmin ‘ya’ya mata, yayin da muke son mata su je makaranta idan muka bullo da batun haraji a makaranta gaskiya zai yi wahala.
Aminiya: Ko da kamar Naira goma ko ashirin?
Ai Naira goma ko ashirin a halin rashin abincin nan kudin kamar Naira miliyan ne a wurin wani, domin wani idan ka ba shi Naira goma ko ashirin ko hamsin, kila ma tunda safe bai ganta ba, kuma ka ce irin wannan mutumin ya kawo ta a matsayin haraji, kai ka san aiki ne babba.
Aminiya: Me kake yi game da gyaran hanyoyi, duk da yake wadansu a karkashin gwamnatin tarayya suke?
Kwanaki na gyara hanya daga Minna har zuwa Suleja, amma yau idan ka biyo hanyar nan sai ka ga kamar ba a taba gyaranta ba. Saboda hanya tsakanin Makera Tegina zuwa Birnin Gwari har Kaduna akwai gadojin da wurare da yawa da suka lalace, manyan motoci sun daina bi, kusan gaba dayansu sun koma bi ta Bida su wuce Legas, ba yawan motocin ne matsala ba, amma irin kayan da suke dauka ne abin damuwa domin ya yi yawa. Abin da muka sani shi ne, mota tirela ba ta wuce ton 30 zuwa 36, amma yau suna daukar ton 36 ko 40, kai wadansu har 60 zuwa 70 suna dauka, dole hanya ta fashe. Na ga inda tirela ke tafiya hanya yana fashewa saboda nauyi, wannan nine na gani ba wai wani ne ya fada mani ba. Kuma hanyoyinmu na Najeriya ana yinsu domin ton dubu 30 zuwa 35. A da akwai wadansu wurare da ake auna nauyin tirela, idan ta zo dole ne ta hau a ga nauyi kayan da ta dauka, amma a yau duk babu wadannan, duk inda gwamnbati ta kashe kudi wajen gyaran hanya na kwana biyu ne kawai. Yanzu wannan hanyar da na gyara kamar ba a taba gyaranta ba.
Kwanakin baya na yi magana da shugaban kasa cewa a taimaka, misali hanyar da tashi daga Kamfanin Bobi zuwa Kasuwar Garba zuwa Bangi zuwa Gulbin Boka, akwai kuma hanya daga Gulu zuwa Ebute zuwa Lambata, akwai kuma hanya daga Pandogari zuwa Alawa Erina zuwa Shiroro, sannan akwai daga Lumma zuwa Agwara zuwa Rofiya. Kuma ya tabbatar mani gwamnati tarayya za ta taimaka, ina ganin babu wata jihar da take da yawan hanyoyi na gwamnati tarayya kamarmu, shi ya sa muke shan wahala.
Zan gabatar da maganar gaban gwamnoni. Ba za mu hana kasuwanci ba, amma kamata ya yi tirela ta dauki kaya daidai da abin da titi zai iya dauka, wato ton dubu 33 zuwa da 36, shi ne wanda muka saba da shi, muddin mun tsare, wannan hanya zai yi kyau, za a samu raguwar lalacewar hanyoyi, amma idan ba haka ba ana gyara hanyar ne tana kara lalacewa. Kuma wa ke shan wahala, mu mutanen kasa muke shan wahala, saboda yawancin masu kamfanonin tirelolin ba su tafiya kan hanya sosai balle su ga irin abin da motocinsu ke haifarwa. Domin kullum ana hadari motoci na faduwa, mutane na mutuwa, wannan yana iya shafar ko ma wane ne.
Akwai wani direban tirela da na tambaye shi me ya sa suke daukar kayar da ya wuce ka’ida, sai ya ce shi har ton dubu 60 yana dauka, kuma shi da mai daukar ton dubu 30 albashinsu daya ne.
Aminiya: Wadansu jihohi na so a ba su damar samar da ’yan sandar jiha, kana jin cewa hakan zai taimaka wa harkokin tsaro?
kwarai zai taimaka, saboda yanzu idan ka duba wurare da yawa ’yan banga ne suke taimaka wa harkokin tsaro, ka ga a da ta bangaren satar mutane a kan kawo mana gudunmowar bayanan sirri, amma yanzu sun bari. Domin idan suka kawo aka tafi aka kama mutum, bayan kwana biyu sai ka tarar an saki mutumin, shi kuma sai ya nemi wanda ya ba da wannan bayanin, wata sa’ilin ma har a kashe shi.
Aminiya: ‘Yan sandan gwamnatin tarayya ke nan sukan yi haka, ina ga a ce ‘yan sandan gwamnatin jiha ne?
Da ‘yan sandan gwamnatin tarayya da na jihohi duk daya ne, za ka ce mene ne hujja, abin da za a ce shi ne idan jihohi suka samu ‘yan sanda za a ce gwamna zai yi duk abin da ya ga dama, to su ma na gwamnatin tarayya idan shugaban kasa ya ga dama zai yi abin da ya ga dama da ’yan sanda .
Aminiya: Yanzu ma da suke ba karkashin gwamnatocin jiha suke ba idan ta kai ta dawo Gwamna na iya yin yadda ya ga dama da su, me za ka ce?
Idan ba ka kai ka kawo ba kuma fa?
Aminiya: Akwai mutumin da ya kai mukamin gwamna a Najeriya kuma bai kai ya kawo ba?
kwarai kuwa, kuma ni gwamna ne nake fada maka haka, akwai gwamnonin da kafin su samu wani abu sai sun yi kamun kafa ko kuma lallabawa ta wurin wadansu takwarorinsu gwanoni.
Aminiya: Gwamnatin tarayya ta gabatar da shirin a koma noma, shin ina matsayin jihar Neja a cikin wannan shirin?
Gaskiya mun gode wa gwamnatin Janar Muhammudu Buhari ta bangaren noma, da kuma gwamnan babban bankin Najeriya, domin sun bullo da wani shiri da ake kira da turanci Anchor Borower Scheme, wanda kuma gwamnatin jihar Kebbi ta fara kuma gwamnonin jihohin Arewa wasu ma suna yi, inda ake taimaka wa manoma, a yi musu rajista, kamar mu jihar Neja mun yi sa’a, domin kamar a wasu jihohi shinkafa kawai ake yi, amma mu a namu shirin za a yi shinkafa a yi auduga, kana a yi waken soya, kuma ni na tabbata a Najeriya nan da shekara daya zuwa biyu idan dai maganar abinci ne za a samu sauki, domin wannan shekarar an noma shinkafa sosai, mutane sunyi noma, sai dai mu a jihar Neja ta wani bangare an samu ambaliya, wannan ya sa an dan samu asarar shinkafa sosai, amma duk da haka za a samu abin da aka samu. Kuma halin da ake ciki a Najeriya kowa ya sani, wanda wannan ya sa mutane da yawa sun koma harkar noma, kuma gaskiya na ji dadin haka, domin tun farko shi ne muka gada, domi ba mu da mai, amma idan muka rike noma, to lallai arzikin arewacin Najeriya zai karu sosai.
Aminiya: Ko kana tunanin duba kamfanin sarrafa shinkafa na Badegi?
Badegi na nan an samu wani kamfani da zai ci gaba da aiki a wurin, tun lokacin da waccan gwamnatin ta wuce aka samu ‘yan matsaloli, amma yanzu ina ganin an dan warware, kuma yanzu haka muna magana da kamfanin, ina ganin kwanan zai bude a fara aiki.
Aminiya: Kana tunanin shiga wata yarjejeniya a kan gonar Mokwa, duk da yake gonar mallakar gwamnatin tarayya ce?
kwarai kuwa, ai kaga a Asiwashi akwai ’yan indiya masu nomar shinkafa, akwai wata gona a wajen Kidi gwamnatin ta fara ta bari, muna kokarin ganawa da su domin mu ga yadda za mu amfana da shi, akwai abubuwa da yawa wadanda zasu taimaka wa noma wanda ina son ganawa da ministan gona domin ganin yadda za mu hada kai saboda amfanin jama’ar jiharmu da ma kasa baki daya.Kuma akwai manoma da yawa da suka fara girbi muna son mu ga yaya za a taimake su domin a sayi hatsin nan daga gare su domin su samu kudi.
Aminiya: Wadansu na zargin gwamnatika ta ki ta binciki wadda ta gada, me za ka ce?
Wannan ba gaskiya ba ne, ana bincike, domin mun kafa kwamiti kuma an kira dukkan kwamishinonin da suka sauka domin su yi bayani, bincike ana yi, mutane su yi hakuri, su bi a hankali, ni kaina na matsu a samo wani abu daga wurinsu domin mu kara cikin aikinmu, kuma akwai wadanda aka samu wurin wadanda suka ci kudin ‘yan fansho, an karbo wani abu daga hannunsu, amma wannan baitulmalin ‘yan fansho za a mayar da kudaden.