Matsalar tsaro: Sarkin Kano ya kalubanci minista kan amfani da fasaha
Sarkin Kano ya ce tunda da waya ‘yan bindiga suke kira su nemi kudin fansa, wajibi ne ma’aikatar ministan ta rika a amfani da fasahar zamani wajen gano maboyarsu domin a murkushe su.
Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya ce jazaman ne Ministan Sadarwa, Bosun Tijani, ya tabbatar ana amfani da fasahar zamani da kuma kwarewarsa wajen yakar kalubalen tsaro a Najeriya.
Sarki Aminu Ado Bayero wanda ya karbi bakuncin ministan a fadarsa a safiyar Alhamis, ya bayyana cewa minisan na da babban rawan da zai taka a yaki da matsalar tsaro, musamman a wannan yanayi da ’yan bindiga sun hana al’umma sakat.
“Da wayoyi ’yan bindiga da suke amfnai su yi magana da iyalan wadanda mutanen da suka sace, saboda haka akwai gagarumar gudummawar da ya kamata ma’aikatarka ta bayar wajen amfani da fasaha domin kamo su a hukunta su.
“Akwai bukatar ku yi amfani da fasahar zamani yadda ya kamata wajen yakar matsalar tsaro da ke kara tsanani a kasar nan, kuma mun san shugaban kasa yana da kwarin gwiwa a kanka shi ya sa ya ba ka wannan matsayi.
- Ra’ayin Kanawa kan sulhun Ganduje da Kwankwaso
- Da gangan na ki fito da sakamakon WAEC dina —Buhari
- Mai Ciki Ta Haihu A Kofar Gida Saboda Yaki Bayan Dokar Hana Fita A Mangu
Da yake mayar da jawabi, ministan ya ba wa Sarkin Kano da al’ummar Najeriya tabbacin cewa zai yi iya kokarinsa wajen sauke duk nauyin da ya rataya a wuyansa.