Matsalar Tsaro: Sheikh Gumi ya kai wa Obasanjo ziyara

Gumi da wasu shugabannin addinai sun gana da Obasanjo a Abeokuta.

Matsalar Tsaro: Sheikh Gumi ya kai wa Obasanjo ziyara

Sheikh Gumi da Obasanjo da tawagar wasu shugabannin addinai

Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmed Gumi, ya gana da tsohon Shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo a Jihar Ogun.

Tawagar malamin ta isa harabar dakin karatu na tsohon shugaban kasar da ke birnin Abeokuta da misalin karfe 11.00 na safiyar Lahadi.

Mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Kehinde Akinyemi ne ya tabbatar wa da Aminiya hakan wanda a cewarsa tawagar ta kunshi wasu jagorori na addini.

“Tabbas Gumi da wasu shugabannin addinai sun gana da Baba,” a cewar Akinyemi.

A bayan nan shehin malamin ya rika ganawa da wasu kungiyoyin ’yan daban daji a jihohin Zamfara da Neja inda yake tattaunawa da su a kan sakin mutanen da suka fada hannunsu a matsayin garkuwa.

Kazalika, Shehin Malamin ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta yi sulhu da ’yan bindigar da suka rungumi zaman lafiya ta hanyar ajiye makamai.