Matsalar tsaro: Shugaba Jonathan da sojojin Najeriya sun gaza –Sanata Gaya

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da rundunar sojojin Najeriya sun gaza game da damar da tsarin mulki ya ba su na tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar jama’ar kasar nan.Sanata Kabiru Gaya ya fadi haka ne yayin da ya ziyarci tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari a Kaduna bayan da Allah ya tserar da shi […]

Matsalar tsaro: Shugaba Jonathan da sojojin Najeriya sun gaza –Sanata Gaya
Matsalar tsaro: Shugaba Jonathan da sojojin Najeriya sun gaza –Sanata Gaya

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da rundunar sojojin Najeriya sun gaza game da damar da tsarin mulki ya ba su na tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar jama’ar kasar nan.
Sanata Kabiru Gaya ya fadi haka ne yayin da ya ziyarci tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari a Kaduna bayan da Allah ya tserar da shi daga harin bam da aka kai masa a makon jiya.
Sanata Kabiru Gaya ya ce wannan harin akwai lauje cikin nadi don ya fi karfin kungiyar Boko Haram. Ya ce abin kunya ne yadda gwamnatin Jonathan ke kin sauraren mutane kamar ’yan majalisa da sauran masu ba da shawarwari kan yadda za a yi gyara a kasar nan.
Sanata Gaya ya ce ya ba da shawarar cewa ya dace a tabbatar an shawo kan Boko Haram tun kafin su wuce Borno da Yobe, amma abin kaito yanzu ga shi har ana cewa sun kai hari a Jihar Legas.
Sanatan wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne ya ce Allah Ya kare barkewar mummunan rikici da ba a samu damar kashe Janar Buhari ba. Ya ce in da an kashe Sheikh dahiru Bauchi da Janar Buhari a rana guda da yanzu Najeriya ta tsunduma cikin bakin rikicin da Allah kadai Ya san iyakarsa.
Sanata Gaya ya ce an ba sojojin Najeriya wata daya don su shawo kan rikicin Boko Haram, amma suka bukaci majalisa ta ba su wata uku don rikicin ya zama tarihi, amma har yanzu shiru. “Idan sojan Najeriya za su je su yi yaki a Laberiya da sauran kasashen Afirka, me zai hana su murkushe Boko Haram?
Sanatan ya ce Shugaba Jonathan ya gaza a mulkin kasar nan yadda ya kamata kuma sun san abin da za su yi. Kuma zai tuntubi Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Dabid Mark don kiran taron gaggawa na hadin gwiwa don tattauna batun harkar tsaro da ke kara ta’azzara a kasar nan, kamar yadda suka yi a lokacin rashin lafiyar marigayi Shugaba Umaru ’Ya’aduwa.
Ya ce ana kashe Naira biliyan 150 duk shekara ga ’yan ta’addan yankin Neja-Delta amma Jonathan ya kebe wa yankin Arewa maso Gabas Naira biliyan biyu kacal, “wannan da bai dace ba.”
Sanata Gaya ya ce, me ya sa Shugaba Jonathan ba zai yi afuwa ga ’yan Boko Haram ba, kamar yadda ’Yar’aduwa ya yafe wa ’yan ta’addan yankin Neja-Delta ba?
 Janar Muhammadu Buhari na ci gaba da tarbar masu zuwa yi masa jaje tare da kawunsa kuma tsohon Manajan Daraktan Kamfanin buga jaridun New Nigerian Newspapers Ltd, Malam Mamman Daura da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Birgediya Lawal Ja’afaru Isa da wasu masoyansa.