Matsalar tsaro ta haifar da tsaiko a harkar kasuwanci -Bashari Bala
Wani jigo a bangaren masu sayar da leda a kasuwar Alaba Rago da ke jihar Legas, Alhaji Bashari Bala, ya bayyana cewa, natsalar tsaro da yanayin tattalin arzikin da Najeriya ta shigasun taimaka wajen fadawa matsalolin da kasuwanni suka shiga.Ya ce, ‘Yanayin rashin tsaro da ake fama da shi a jihohin Arewa da kasashen Afirka […]
Wani jigo a bangaren masu sayar da leda a kasuwar Alaba Rago da ke jihar Legas, Alhaji Bashari Bala, ya bayyana cewa, natsalar tsaro da yanayin tattalin arzikin da Najeriya ta shigasun taimaka wajen fadawa matsalolin da kasuwanni suka shiga.
Ya ce, ‘Yanayin rashin tsaro da ake fama da shi a jihohin Arewa da kasashen Afirka ta Arewa ya kara taimakawa wajen rashin ciniki da tabarbarewar kasuwanci. Sai dai muna fata gwamnati za ta kawo mana dauki ta dauki matakan da suka dace da za su gyara al’amura ta yadda ’yan kasuwa za su ci moriyar kasuwancinsu ba tare da wata matsala ba’.
Alhaji Bashari wanda yake harkar sayar da tamfol a kasuwar Alaba ya ce tsayawar damina shi ne dalilin da ya janyo musu tsaiko a cinikin Leda a kasuwar.
Alhaji Bashari Bala wanda dan asalin jihar Katsina da ke sayar da tamfol da igiya da buhu, ya bayyana haka ne a yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata.
Ya ce, ‘Saboda Allah kwanaki an fi samun ciniki a harka irin tamu. Lokacin da ruwa yake sauka harkokinmu sun fi tafiya. Amma yanzu lokaci ne na sayan kaya a ajiye. Watan watannin Nuwamba da Disamba har zuwa sabuwar shekara duk lokaci ne na tara kaya har sai zuwa watan Afrilu da ruwa zai fara sauka, muna kyautata zaton kasuwa za ta bude’.
Ya ci gaba da cewa, ‘Yanzu farashin tamfol ya fadi domin tamfol din da a da ake sayarwa Naira dubu 20 yanzu dubu 10 ake sayar da shi. Wanda ake sayarwa Naira dubu 40 yanzu dubu 20 ake sayar da shi. Wanda ake sayarwa Naira dubu 60 yanzu Naira dubu 40 ake sayar da shi. Igiyar ruwa ma haka farashinta ya sauka’.
Ya bayyana cewa, dalilin da ya sa farashin ya fadi shi ne masu motocin da suke sayan tamfol suna saya ne saboda su rika rufe kayan da suka dauka.