Matsalar tsaro ta sa Gwamna Yuguda ya ki yin Sallah a Bauchi
Wasu majiyoyi sun ce matsalar tsaro da ake ci gaba da fuskanta a wasu daga cikin jihohin Arewa maso Gabas ta tilasta Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda kin yin Sallar Idi a Jihar Bauchi.A bara ma Gwamna Isa Yuguda ya yi Sallar Idi ne a garin Dass hedkwatar karamar Hukumar Dass maimakon garin Bauchi […]
Wasu majiyoyi sun ce matsalar tsaro da ake ci gaba da fuskanta a wasu daga cikin jihohin Arewa maso Gabas ta tilasta Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda kin yin Sallar Idi a Jihar Bauchi.
A bara ma Gwamna Isa Yuguda ya yi Sallar Idi ne a garin Dass hedkwatar karamar Hukumar Dass maimakon garin Bauchi fadar jihar.
Wannan ya sa aka rika kananan maganganu kan yadda Gwamnan ke barin fadar jihar a lokacin Sallar Idi.
Da wakilimu ya tuntubi mataimakin Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamna Yuguda Malam danlami Baban Takko ya bayyana wa wakililinmu cewa tabbas Gwamna Yuguda bai yi karamar Sallar da ta wuce a Jihar Bauchi ba, amma Mataimakin Gwamna Alhaji Sagir Aminu Sale da wasu kusoshin gwamnatin jihar sun halarci Babban Masallaci Idi na Bauchi tare da Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu inda suka gudanar da Sallah lafiya.
Baban Takko ya kara da cewa babu kanshin gaskiya game da jita-jitar cewa matsalar tsaro ce ta hana Gwamna IsaYuguda yin karamar Sallah a Bauchi. Ya ce, Gwamnan ya tafi aikin Umara ne a daidai lokacin Sallar, ba wai ya ki halartar masallaci ba ne saboda dalilin tsaro kamar yadda wasu ke yadawa ba.
Ya ce jihar tana daya daga cikin jihohin da ake samun zaman lafiya da kwanciyar hankali saboda haka ya shawarci jama’a su guji yada jita-jita.