Matsalar tsaro: Wasika zuwa ga Shugaba Buhari
Hakika yadda harkokin tsaro suke kwan-gaba-kwan baya tare da kara tabarbarewa a baya-bayan nan abu ne mai matukar tayar da hankali. Alhamdulillahi an samu gagarumin ci gaba a yaki da Boko Haram, ta yadda yanzu ayyukan kungiyar suka takaita a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, maimakon akasarin jihohin Arewa. Sai dai duk da haka […]
Hakika yadda harkokin tsaro suke kwan-gaba-kwan baya tare da kara tabarbarewa a baya-bayan nan abu ne mai matukar tayar da hankali. Alhamdulillahi an samu gagarumin ci gaba a yaki da Boko Haram, ta yadda yanzu ayyukan kungiyar suka takaita a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, maimakon akasarin jihohin Arewa. Sai dai duk da haka hare-haren da ’yan Boko Haram suke kaiwa a baya-bayan nan da kuma ta’asar masu garkuwa da mutane a akasarin jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ya kamata Shugaban Kasa ya yi tankade da rairaya ga bangaren tsaro don samar da maslaha.
Kowa ya ji yadda a ’yan kwanakin nan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu wadda ita ce babbar hanyar da ta hade Borno da sauran jihohin kasar nan take fama da hare-haren Boko Haram. Hare-haren da suke jefa jama’ar da ke bin hanyar a cikin mummunan hadari, domin a kullum ’yan ta’addar suna kai hari a hanyar inda ake hasarar rayuka da dukiyar jama’a. Ta kai a yanzu babu wanda zai yi kasadar bin hanyar bayan karfe 4:00 na yamma kamar yadda bayanai suka nuna.
Ina ganin ayyukan ta’addanci na Boko Haram da garkuwa da mutane suna ci gaba da aukuwa ne, saboda an baro shiri tun farko. Wadannan abubuwa gwamnatin Shugaba Buhari ta gaje su ne. Kuma a matsayin Shugaba Buhari na tsohon Janar din soja kuma tsohon Shugaban Kasa, mun dauka abu na farko da zai fara yi bayan ya zama Shugaban Kasa a shekarar 2015, shi ne ya gudanar da bincike cikin sirri domin gano masu hannu a wannan muguwar kungiya da masu taimaka mata da masu fakewa da ita suna aikata ta’asa da kuma wadanda suke amfani da kasancewarta wajen sace dukiyar kasa daga cikin jami’an tsaro da sauransu. Haka mun dauka zai yi bincike cikin sirri don gano su wane ne masu garkuwa da mutane? Kuma a ina suke samun makamai, kuma su wane ne masu tallafa musu wajen yin wannan ta’asa a tsakanin jami’an tsaro da shugabannin gargajiya kai har da kungiyoyin kabilu da na sa kai.
To amma ganin yadda har yanzu Boko Haram ke da sauran karfin da za ta iya tsare manyan hanyoyin da suka hada da Maiduguri zuwa Damaturu da Maiduguri zuwa Bama da sauransu wannan ya nuna cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta tunkari yaki da Boko Haram ne kawai a fagen daga, ba ta yi binciken kwakwaf ba don gano tushen kungiyar ko masu tallafa mata a ciki da wajen kasar nan ko masu fakewa da ita suna aikata ta’asa don neman kudi kamar garkuwa da mutane, ko kuma masu fakewa da ita a ciki da wajen jami’an tsaro suna samun dukiya da sunan yaki da Boko Haram din.
Masana harkar tsawo sun sha nanata cewa a mayar da hankali wajen tattara bayanan sirri don dakile ayyukan ’yan bindiga da suke barazana ga rayuwar jama’a.
Yayin da muke murnar fara shawo kan matsalar Boko Haram sai ta garkuwa da mutane ta ci gaba da kara habaka. Misali hanyar da ta fi kowace hanya muhimmanci a Najeriya ita ce hanyar Kaduna zuwa Abuja wadda ta hada Arewa da Kudu. Kuma abin takaici hanyar da kwata-kwata ba ta fi kilomita 200 ba, yau ba talakawa ya ayyuhan nasu ba, hatta manyan hafsoshin soja da ’yan sanda da ministoci da sauran manyan mutane sun kaurace mata sun koma bin jirgin kasa!
Kuma matsalar garkuwa da mutanen tana neman zama wata babbar barazana da kusan ba ta da bambanci da Boko Haram wajen ta’asa. Abin da ya raba su kawai wannan yana fakewa da addini, su kuma masu satar mutane babban abin da suke cewa INA KUDI! KUDI KAWAI! In babu suna iya nakasa mutum ko su hallaka shi. Mun sha jin labaran irin rashin imanin da masu garkuwa da mutane suke nuna wa wadanda suka kama. Mun sha jin labaran mutanen da masu garkuwa da mutane suka hallaka.
Ana dora alhakin akasarin garkuwa da mutane ga al’ummar Fulani makiyaya da a baya aka rika sace wa shanu ana talauta su. Sai To amma hatta satar shanun ba zai yiwu wanda bai san saniya ba ya sace ta har ya batar da ita. Don haka satar shanun babu masu yi sai Fulanin ko masu yi musu kiwo da mahauta.
To in haka ne mene ne amfanin jami’an tsaron da muke da su da ba za su iya bi cikin sirri su zakulo masu aikata wadannan miyagun ayyuka da suka addabi kasar nan ba? Mene ne amfanin jami’an tsaron kasar nan idan ba za su iya gano masu shigo da makamai suna sayar wa wadannan ’yan ta’adda ba? Ko kuwa zargin da mutane ke yi cewa akwai jami’an tsaro da suke da hannu a akasarin wadannan miyagun ayyuka gaskiya ne?
Domin an sha samun rahoton kama sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro suna sayar wa wadancan miyagu makamai ko suna daure musu gindi don samun nasu kason, ko suna ba su hayar bindigogi da samar musu da harsasai da sauransu.
Mun yaba wa Gwamnatin Tarayya kan rufe iyakokin kasar nan da ta yi, domin hakan ya taimaka wajen rage shigo da miyagun makamai, to amma ya kamata a fahimici cewa in Shugaba Buhari bai yi tankade da rairaya ga jami’an tsaro ba, to akwai yiwuwar wadansu miyagu su ci gaba da karbar NA-GORO suna bayar da dama ana shigo da makaman ta iyakokin da ake cewa an rufe.
Mahaukatan kudin da ake samu a garkuwa da mutane suna iya sa a sayi akasarin jami’an tsaron Najeriya, wadanda galibi sun shiga aikin ne don tara abin duniya. Don haka Shugaban Kasa ya bayar da umarni a yi bincike cikin sirri don gano masu hannu a wannan muguwar harka ta Boko Haram da garkuwa da mutane.
Lokaci ya yi da za a fara dora wa kowane DPO alhakin duk gazawar da aka samu a yankinsa. Haka a dora wa Kwamishinan ’Yan sandan jiha alhakin duk abin da ya faru a jiharsa a kori na kora a ladabtar da wanda aka samu da nuna gazawa. Duk wanda ya bari aka yi laifi a yankinsa a hukunta shi ta hanyar cire shi daga yankin a gudanar da bincike in gazawar ba ta shafi hadin baki ba, idan ko bincike ya nuna akwai hadin baki a yi masa korar kare daga aiki sannan a hukunta shi da sauran mukarrabansa. Haka ya kamata lamarin ya kasance a bangaren soja da sauran jami’an tsaro.
A bangaren manyan hafsoshin tsaro kuwa muna ganin kamar sun gaji da aiki ne, kila wannan ya sa Babban Hafsan Sojin Ruwa ya shaida wa duniya cewa za a janye sojoji daga inda ake fama da rikici. Ba don an yi ca kansa ba da an yi mana sakiyar da ba ruwa, mu mutanen Arewa maso Gabas. Me ya hada sojan ruwa da batun yankin Arewa maso Gabas ko Arewa maso Yamma da ske fama da tashin hankali?
Don haka tunda sun gaji Shugaba Buhari ya sallame su ya kawo sababbin jini a ga nasu irin kamun ludayin.
Alhaji Adamu Damboa ya aiko da wannan rubutu ne daga Unguwar Mpape, Birnin Tarayya, Abuja.
Za a iya samunsa ta: 08066073209, 08055945695