Matsalar wuta: Ƙananan ’yan kasuwa sun sauya dabara

Ƙanana da matsakaitan ’yan kasuwa sun koma amfani da wasu hanyoyin samun wutar lantarki sun haƙura da ta gwamnati.

Matsalar wuta: Ƙananan ’yan kasuwa sun sauya dabara

Ƙanana da matsakaitan kamfanoni da ’yan kasuwa da ke buƙatar wutar lantarki don gudanar da harkokinsu, sun koma amfani da wasu hanyoyin don samar wa kansu wutar, inda suka haƙura da wutar gwamnati.

’Yan kasuwa a masu sana’o’in hannu sun yi wa kansu ƙiyamul laili, bayan gazawar Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DisCos) sakamakon durƙushewa da rikirkicewar tsarin wuta a Nijeriya.

Ba kamar manyan kamfanoni da masu masana’antu ba waɗanda suka daina amfani da tsarin wutar lantarki na ƙasa, matsalolin ƙanana da matsakaitan kamfanoni da suka dogara da wutar gwamnati sun ƙara dagulewa ne cikin ’yan makonnin da suka gabata.

Tun watan Oktoban bana, wutar lantarki a Nijeriya ta shiga cikin wani mummunan hali, lamarin da ya sa kamfanoni da dama suka rasa maqudan kuɗaɗe.

Binciken Jaridar Aminiya ya gano cewa, yawancin ƙanana da matsakaitan kamfanoni da sana’o’i sun koma amfani da wasu hanyoyin samar da lantarki na ƙashin kansu, don ci gaba da harkokin kasuwancinsu ba tare da jiran ta gwamnati ba.

Gwamnatin Tarayya dai ta danganta durƙushewar tsarin lantarki na qasa da lalacewa da kuma tsufan kayan aikin samar da wutar.

A makon jiya Ƙungiyar Masana’antu ta Nijeriya (MAN) ta bayyana cewa, ’ya’yanta sun kashe Naira biliyan 238.31 wajen samar wa kansu wutar lantarki, a cikin wata shida na farkon 2024, wanda ya ƙaru da kaso 7.69% idan aka kwatanta da wata shida na ƙarshen 2023.

Rahoton MAN na tattalin arzikinta na wata shidan farkon 2024 ya danganta ƙaruwar tsadar da tashin farashin man dizal da iskar gas da sauran nau’ukan makamashi da kuma buƙatar masana’antu su saka jari wajen samar da wutar ta ƙashin kansu saboda rashin tabbacin ta gwamnati.

Haka nan, Kamfanin Masana’antu na Bunƙasa Wutar Lantarki, wanda Ƙungiyar MAN ta kafa ya bayyana cewa, tsadar wutar lantarki tana matuƙar wahalar da masana’antu, ta yadda ba za su iya jurewa ba, musamman waɗanda ke rukunin Band A.

Don shawo kan matsalar, kamfanin ya ce ya samar wa da kamfanoni 10 mafita wajen samar da hanyoyin lantarki mai ɗorewa.

Sun haƙura da wutar gwamnati

Wasu ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu da Aminiya ta zanta da su sun bayyana yadda suka nema wa kansu mafita daga matsalar wutar lantarki ta qasa.

Wani mai kamfanin kayan kwalliya a yankin Kubwa da ke Abuja, Isaac Iwu ya ce, ya koma amfani da lantarki mai amfani da hasken rana (sola) bayan lalacewar na’urar samar da wuta a yankin, yana mai cewa hakan rage masa fiye da rabin kuɗin wutar da ya saba biya.

Aliyu Usman, wani mai kula da shagon sayar da kayan sha a Abuja, ya ce, yana amfani da sola ce wajen sarrafa firinjinsa guda biyu, amma yana yin hakan ne a mataki-mataki saboda tsadar tsarin.

Shi kuma Sanusi Abdullahi, wanda ke sayar da kayan sanyi a Kano, ya ce duk da cewa hasken rana yana da kyau, amma yana buƙatar babban jari don kafa shi.

Malam Sanusi ya bayyana cewa, ya kashe sama da Naira miliyan biyar wajen girka na’urorin sola, wanda hakan ya rage masa wani babban kaso na jarinsa da ya yi amfani shi domin sanya na’urorin.

Shi kuwa Abubakar Suleiman, tela ne da ya ce ya daina amfani da wutar gwamanti gaba ɗaya, ya koma yin amfani da janareta mai aiki da iskar gas.

Falalu Ahmad, daga vangaren masu walda ya ce, rashin tabbas na wutar gwamnati ya sa ya daina dogaro da ita, ya koma aiki da janareta kaxai wajen gudanar da aikinsa.

MAN ta yi kira ga gwamanati

Shugaban qungiyar masu fitar da kayayyaki zuwa qasashen waje ta MAN, Odiri Erewa Meggison ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta zuba jari a ɓangaren samar da wutar lantarki mara gurvata muhalli, wanda ya ce zai rage wa masana’antu tsadar gudanar da kasuwanci.

Ya ce, masana’antu ba za su iya ci gaba da dogaro da tsarin lantarki na gwamnati na yanzu ba, a yayin da waxanda ba za su iya siyan man dizal ba aikinsu ba zai riƙa wuce awa biyu zuwa huxu ba a kowace rana.

“A yanzu yawancin masana’antu suna iya yin aiki na awa biyu zuwa huɗu ne kawai a rana, saboda ba za su iya sayen man dizal ko fetur ba. Amma za mu iya magance wannan matsala ta hanyar amfani da makamashi so-muhalli don rage tsadar gudanar da kamfanoni,” in ji shi.

Meggison ya bayyana cewa, kamfanoni suna canzawa daga amfani da man dizal zuwa gas da hasken rana duk da cewa hakan ma yana buƙatar babban jari.

“Kan tafi kan je, wannan zai taimaka wajen samar da gogayya da gogoriyo a kasuwanni. Saboda haka akwai buƙatar gwamnati ta taimaka. Akwai kamfanoni da dama da suka fara shiga wannan fannin na makamashi don rage tsadar wuta ga masana’antu a Najeriya’’, in ji shi.

 

Daga Faruk Shuaibu da Adam Umar (Abuja), Ahmad Datti (Kano), da Maryam Ahmadu-Suka (Kaduna). Fassara: Ahmed Ali, Kafanchan