Matsalar yin shaye-shaye ga manyan gobe (I)
An hallici komai a bisa dabi’un gudanarwa, komai na rayuwa a kan dabi’a, yayin da a duk hallitu babu wacce ke kokarin jirkita dabi’arta kamar Bil-adama, musamman wajen ci, sha da shaye-shaye. Idan aka yi maganar shaye-shaye a kan kawo giya, wiwi, shayi wadanda kan hana bacci, ko kwalaben benelin inda ake yin kwalan-kwalan a […]
An hallici komai a bisa dabi’un gudanarwa, komai na rayuwa a kan dabi’a, yayin da a duk hallitu babu wacce ke kokarin jirkita dabi’arta kamar Bil-adama, musamman wajen ci, sha da shaye-shaye.
Idan aka yi maganar shaye-shaye a kan kawo giya, wiwi, shayi wadanda kan hana bacci, ko kwalaben benelin inda ake yin kwalan-kwalan a fita daga hayyaci, sannan wani lokaci a kan sha alabukun, baliyom da tiramol ko sagadol don karin karfin aiki ko kar a yi bacci.
Duk abin da mutum ya saba, ya kan shaku kamar fura, goro da sigari, wannan kamuwa kan yi tasiri a jiki, ta yadda idan kwakwalwa ba ta samu wannan sinadari ba kai zai fara ciwo. Yayin da sunan jin dadi ko samun daukaka a kan sha zakami, tsimi, giya da shamfen, wasu kuma kan sha sifirt don jin dumi, musamman a kasashen da ake sanyi kamar Rasha.
A daidai lokacin da wasu ke naman ceto ‘ya’yansu da ‘yan uwansu daga halin shaye-shaye, wadanda tun ana cewa shaye-shaye da dadi suka fada shan duk wani abin sha don su fita daga cikin duniyar nan!
dabi’ar ba a manya ta tsaya ba, ta fara ne daga yara wani lokacin tun yara na firamare suke fara mu’amala da miyagun kwayoyi. Wani lokacin sai ka ga mutum kamar ya tashi daga bacci, shi kuwa ba bacci yake yi ba, yana cikin wani yanayi na walwala, yana hutawa yana jin ya samu daukaka. Mutum yana sata da rana, ya dauka ba a ganin sa!
karuwa mashaya kan zama matsala ga kasashe, domin akasari matasa ke fadawa hadarin kwana cikin shaye-shaye yayin da matasa ne maginan da za su gina kasar, idan suka gaza zuwa makaranta, ko kwakwalwarsu ta kasa daukar karatu, an samu barazana ga gobe, domin manyan gobe za su zama jidali.
Ta ya za a iya karatu a fahimta, balle a yi aiki a kamfanoni a gina kasar, abin takaicin ya fi damun kasashe irin Najeriya inda ‘yan siyasa, shugabanin mahukunta kan ba mabiya kwayoyi na sha da na hurawa don a masu aiki! Wai ina mafita?
Wasu daga cikin dalilan da suke sa ake ta’amuli da miyagun kwayoyin sun hada da jahilci, damuwa, mugan abokai, maraici, talauci, rashin aikin yi da dogon buri.
A hankali za mu fahimci kusan duk wadannan dalilan suna da alaka da juna watau idan ka dauki jahilci ko maraici kan sa a yi abuta da mugan abokai, maraici na haifar da talauci idan mahaifi ya rasu a kan rasa abinci, rashin aikin yi ga niyoyin cike gajeru da dogayen burikan rayuwa kamar aure da sauransu.
A kan saba wajen dalilan shaye-shaye wasu jin dadi da daukaka kan jefa su cikin wannan jifa’in, inda za ka ga ‘ya’yan manyan mutane masu mutunci sun shiga shago suna neman kwaya ko kwalabe. Duk da yaran nan a kebe suke ba su tsira ba, domin su kan su iyayen kan jefa iyalansu cikin kadaici da rashin ba lokaci muhimmancin wajen gina rayuwa, ba taimako, tausayi ko dan uwansu zumunci.
A duba ta yadda mutum ya gina rayuwasa, sharrin iyaye kan bi ‘ya’ya, amma Allah na shirya wanda Ya so. Abin mamakin shi ne wanda aka karrama da fin komai hankali da basira, amma yana neman haukata kansa!
Gata ko samun wuri, ko damuwa ce akwai hanyoyin da ake warwaresu.
Duk da yadda ake ganin an samu karuwar wannan harka, amma ta wata fuska an samu sauki domin a ‘yan shekarun da suka wuce a birane irin su Katsian da Sakkwato, mata kan sha sugari a bainar jama’a, amma a yau an manta da wannan al’adar. Kuma a da a kan sha giya a fili a gina gidajen karuwai, amma a yau an samu saukin wannan fitinar, mashaya sun koma karkashin kasa!
Sai dai babban hadarin barna ita ce yin ta a boye, kamar yadda bincike ya tabbatar da yadda ‘yan, mata da zaurawa a cikin gidaje ke kwankwadar maganin tari, maganin da aka yi ka sha na kwana hudu zuwa biyar sai mutum ya kwankwade a zama daya! Ta ya za a yi karatu, mutane ma ba su fahimta ba, balle rubuta jarrabawa a nan duniya, lallai
karshen ‘yar maye hawaye!
Lokaci ya yi da za a kebe wasu wurare don shan taba domin sigari na cutar da wadanda ba su sha, a haka a haramta sha a bainar jama’a, kamar a cikin asibitoci, kasuwanni da makarantu. Sannan a hana tallar ta a bangwaye ko a shaguna, domin hakan kan ja ra’ayin wasu su gwada ta yadda za ka ga mutum ya bankawa sigari wuta ka ga wawa a gefe guda, wuta a daya gefen!
Tabbas kwayoyi na kawo kudi, shi ya sa mutane da dama ke fataucinsu, kuma zu zama hamshakai a wannan harka, shi ya sa ko mai sayar da sigari zai gaya ma ya fi samun kudi a sigarin a kan sauran kayan masarufin da yake sayarwa. Falke ka watsa yaransa wajen tsayawa da kafafuwansa, a haka ma sai ka gaza gane wane ne madugun.
A tsaftace hanyoyin neman aure, wani saurayin sai ya zuka yake zuwa zance! Sannan akwai hadarin ‘yan mata su rika karbar kyaututuka daga wajen samari, domin a halin yanzu mazaje na yin allurar sinadaran kashe jiki a lemu, tuffa ko inibi, ta yadda hankali zai gushe, musamman masu hira a mota ko masu rufe gidan idan sun gama!
Wajen kawo karshen wannan harkar kan bi matakan al’umma a kashe al’adar zuwa gidajen biki ko kwana a gidajen kawaye ko daren Larabawa ko kauyawa fati da sauran shagulgulan da ake kebe yara da manya, mata da maza wadanda ba muharamman juna ba!
Su kansu iyaye na da irin rawar da za su taka, su bar bari ana wasan banza tsakanin abokan wasa, ko hutu, su lura da lokacin ‘ya’yansu, kuma su jawo ‘yayan jiki. Idan hali ya canza su sa ido, su gane a ina ‘ya’yansu suke bata lokaci!
Gwamnati za ta iya sa ido kan irin fima-fiman da ake kawo wa wannan kasar inda ake nuna ana fataucin miyagun kwayoyi da nuna rayuwar wasu mashaya. Akasari kan nuna dilalan a matsayin jarumai, yayin da idan aka so a sauyawa mutane tunani sai a nuna makomar mashaya, inda suke yin gajeruwar rayuwa, kuma su kare da takaici da nadama, a yaki jahilcin ta hanyar nuna dalilai da illar ta’amuli, domin idan ka san cuta sai ka guje ta. Sannan a sallami duk malami, ko likitan da ya yi suna wajen zuwa wajen aiki a buge ko masu shigar bakaken gilasai ba rana ba dare don kar a gane kalolin idanunsu!
Hukumar NDLEA na iya yakar wannan harkar ta fuskoki da dama, da farko aiki gadan-gadan da masu fatauci da mashaya ai an san inda suke! Kuma an san manyan da kananan, an san yadda da inda suke shiryawa, sarrafawa da sharholiyar. A shirya bitoci, lacca a jami’a da makarantun sekandare, buga fasta a kasuwanni, shaguna, makarantu da
tashohi wajajen tarruruka da sauransu.
NGOs watau masu zaman kansu za su iya taka rawar gani wajen yakar wannan fitinar, ta hanyar shirya tarruruka da yin bita game da illar shaye-shaye. Mutane za su iya taimakawa, wajen kai kara inda suka ga ana hura hayaki!
Idan hankalin mutum ya fita, za a iya aikata komai, abin ba a kansu ya tsaya ba! Fita daga hayyaci ya fi komai zama hadari, wani daga nan sai Lahira. Kuma kar mu manta mu taya mashaya da addu’o’in su daina, Allah ya tsare.
Buhari Daure
Modoji, Jihar Katsina.