Matsalata da shugabannin PDP – Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce shaida wa shugabannin Jam’iyyar PDP cewa duk da zai ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar, sadaukarwarsa ga hadin kan kasa da nasararta suna gaba da na jam’iyyar. Cif Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Lahadi cikin wata sanarwa ga manema labarai a garin Abeokuta fadar […]

Matsalata da shugabannin PDP – Obasanjo
Matsalata da shugabannin PDP – Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce shaida wa shugabannin Jam’iyyar PDP cewa duk da zai ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar, sadaukarwarsa ga hadin kan kasa da nasararta suna gaba da na jam’iyyar.

Cif Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Lahadi cikin wata sanarwa ga manema labarai a garin Abeokuta fadar Jihar Ogun, inda ya ce, “Burina da sadaukarwata ga Najeriya ya shallake na siyasar jam’iyya, kuma babu abin da zai kashe min gwiwa wajen sadaukarwata ga Najeriya ta kowane.”
Tsohon Shugaban Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP Obasanjo ya kara da cewa, Najeriya tana tsaka-mai-wuya da ake bukatar hada hannun kowa don ceto ta. “Yau Najeriya tana bukatar hadin kan kowa don magance manya matsalolin da suke damunmu da suka shafi rashin tsaro da batun ’yan matan Chibok da karuwar rashin adalci da rashinn kayan inganta rayuwa da mulkin nuna gadara da rashawa da talauci da batun ilimin matasa da koyar da sana’o’i da samar da aikin yi.”
Cif Obasanjo ya ce wadannan su ne abubuwan da suke damun mafi yawan ’yan Najeriya. Kuma akwai bukatar mu hada hannu don kai ta gaba. Ya ce babu bukatar sai ya roki haka.
Obasanjo wanda ke mayar da martani kan kiraye-kirayen da shugabannin PDP suke yi masa nay a dawo jam’iyyar, ya ce bai kulle da kowa a cikin jam’iyyar don haka kuskure ne wani ya yi kira kan ya dawo jam’iyyar. Ya ce a karkashin jam’iyyar ya zama Shugaban kasa kuma hakan ya isa hujar ci gaba da kasancewa dan jam’iyyar amma dalilinsa na komawa gefe ya shafi batun akida da kare mutunci ne.
“Misali a matsayina na tsohon Shugaban kasa, kuma Shugaban Hkumar Yaki da Fataucin Miyagun kwayoyi ta Afirka ta Yamma, kuma wakili a Hukumar Yaki da Miyagun kwayoyi ta Duniya, ba zan yarda dillalin miyagun kwayoyi da ake nema a Amurka ya zama jagoran shiyya na jam’iyyata ba. Wane irin bayani zan yi ga abokaina a ciki da wajen Najeriya?” yana nufin Buruji Kashamu, jagoran PDP a Kudu maso Yamma kuma na hannun damar Shugaba Goodluck Jonathan.
Ya ce wannan daya ne daga cikin batutuwa da dama da ya sha bayani a kansu, ya ce amma zai ci gaba da harkoki da PDP a matakin unguwa, kuma ya ce ya bayyana wannan damuwa ga shugabannin jam’iyyar kamar Shugaba Jonathan da Shugaban Majalisar Dattawa Dabid Mark da kuma Shugaban Jama’iyyar PDP ta kasa, Ahmadu Mu’azu.