Matsalolin Arewa: Da dangari ake cin gari

Hakika ko shakka babu duk wanda ya sanya tabaraun hangen nesa, ya kalli yankin Arewa, ya san babu wanda ya kirkira wa yankin Arewacin Najeriya mummunar masifar da ta yi wa yankin kawanya, illa kawai ‘yan siyasar Arewa da ‘yan Bokon Arewa da Shugabannin Arewa da attajiran Arewa, da ma sauran masu fada a ji, […]

Matsalolin Arewa: Da dangari ake cin gari
Matsalolin Arewa: Da dangari ake cin gari

Hakika ko shakka babu duk wanda ya sanya tabaraun hangen nesa, ya kalli yankin Arewa, ya san babu wanda ya kirkira wa yankin Arewacin Najeriya mummunar masifar da ta yi wa yankin kawanya, illa kawai ‘yan siyasar Arewa da ‘yan Bokon Arewa da Shugabannin Arewa da attajiran Arewa, da ma sauran masu fada a ji, tare da talakawa. Dalilaina a nan shi ne tun farkon wannan dimokuradiyyar a shekarar 1999, wadannan rukunin al’umma ke taka rawa sosai wajen yin biris da dimbin matasa, tare da kauda kai ga nema wa matasa ayyukan yi. 

Don haka mu dubi dimbin ma’ilmanta da Allah ya hore wa Arewa kamar ‘yan Bokonmu na Arewaci Nijeriya, shin wai ko sun yi amfani da Ilimin da Allah ya ba su wajen ciyar da yankin? Ko kuma sun yi amfani da Iliminsu ne wajen gina kansu da Iyalansu kawai? Wani abin ban takaici da ban haushi, shi ne da yawan ‘yan Arewa masu Ilimi da zaran sun samu damar dare madafun iko, sai kawai ka ga sun kauda kai da halin da ‘yankin Yake ciki. Don haka anan ko shin ko shi ne tukuicin da suka bai wa al’ummar da Arewacin Najeriya? Duk da dai cewa ba a taru a ka zamo ɗaya ba. Saboda haka har gobe dai akwai hazakar ‘yan Boko masu kaunar ganin Arewa da al’ummarta na ci gaba. Amma su o’o ya kamata a saita tunani, tare da sanya Arewa da ‘yan Arewa a gaba.
A gefe daya idan muka dubi ‘yan siyasar Arewa su ma sun taka rawa sosai wajen durkusar da ‘yankin na Arewa, musamman ‘yan Majalisar wakilai da na dattawan Arewa da ma sauran tarkacensu, su suka watsa wa ‘yan Arewa kasa a ido wajen karkata daukacin abin da Arewa ke samu daga Gwamnatin Najeriya, inda za ka tarar da wani dan Majalisar Wakilai da na Dattawa ya yi wa wadanda yake wakilta batan dabo, sai dai kawai su gan shi a akwatunan talabijin ko, a ji shi a rediyo, wanda ba za ka sake ganinsa ba har sai lokacin kadawar guguwar Siyasa.
Matasa a yi kokarin auna al’amura akan sikelin kwakwalwa, tare da iya bambance tulin hanjin jimina da na zakara; wato sahihan ‘yan siyasa da ‘yan jarin siyasa.
Wani rainin hankalin, shi ne, da ‘yan Majalisarmu na Aewacin Nijeriya suka yi na yunkurin tsige Shugaban kasar Najeriya a bisa da watsa musu barkonon tsohuwa, alhali ga dimbin jama’a na rasa rayukansu ba su dauki matakin tsige Goodluck ba. Wannan ya nuna karara ba su damu da halin da al’ummar Arewa maso Gabas ke ciki ba.
Su ma attajiran Arewa da suka zamo innuwar giginya na nesa dai ke morewa, domin kowa ya san cewa akwai rawar da ya kamata su taka wajen farfado da yankin, musamman wajen dawo da darajar aikin gona da shigowa da kananan masana.antu.
Amma wani abin ban takaici da ban haushi, shi ne, sai ka ga sun dauki dukiyarsu da kamfanoninsu zuwa Kudu da ma kasashen waje, wanda a haka ne suke ci gaba da kashe Arewa. Wannan makahon matakin da attajiran Arewa suka dauka a kan al’ummar ko ya dace? Kowa dai ya yi da kyau, to fa zai ga da kyau.
Saboda haka su kuma masu fada aji ko mene ne ya kamata su aiwatar wa al’ummarsu? Kowa ya ga irin bakin kisan kare dangin da ake yi wa talakawan Arewa, inda masu karfin fada aji suka ja bakinsu suka yi shuru, ba tare da cewa komai.
Sarakunan Arewa kuna da matukar kima ga idon Jama’a, amma duk da cewa wasu daga cikinku na iya kokarinsu na gaya wa ‘yan siyasa da ‘yan bokon Arewa da ma masu fada aji gaskiya. Sai dai kash ! Wasu na kokarin bata rawarsu da tsalle
wajen ka sa gaya wa masu rike da madafun iko gaskiya. Shin ko kun manta cewa za ku karbi dimbin tambayoyi a gobe kiyama abisa shugabancin da Allah (SWT) ya baku ? Don haka aiki dai ya rage wa mai shiga Rijiya, kuma ‘gyara kayanka dai bai zamo sauke mura ba.’ Don haka masu azancin magana dai na cewa sai da dangari ake cin gari, musamman halin da Arewa take ciki, kowa ya san idan babu hannun ‘yan Arewa da kamar wuya a samu damar tarwatsa yankin Arewa. Saboda haka ko akwai rawar da su ma talakawan Arewa za su taka?
Akwai rawar da za su taka sosai wajen rungumar kananan masana’antu, tare da watsi da dabi’ar nan na zama ‘ci ma zaune’ (ko kwance), ta yadda kauce wa shawagi gidaje tarkacen ‘yan siyasa, domin karbar maula da zubar da mutuncinsu, da kungiyoyin tarzoma ko kuma na asiri.
Da fatanAllah ya sa wannan jan hankali ga magabata, ga kowa da kowa ya shiga kunnuwan basira da aikin da su.
Wai ko kun manta da cewa sai kun amsa dimbin tambayoyi a kotun da babu lauyan da zai kare ku? Kuma mene ne ya hana ku shiga zaman makoki kan irin kashe-kashe da daddasa Bama-bamai a kasuwani da masallatai da coci-coci, illa kawai kuwar siyasa? Shugabannin Arewa dai siyasa kawai ta dame su, ba wai samun zaman lafiyar al’umma ba.
A karshe ina mika sakon ta’aziyata ga al’ummar Jihar Kano da masarautar Kano, kan da harin da wasu barayi, kuma ‘yan ta’adda suka kai a Babban Masallacin wannan birni mai tsohon tarihi. Da fatan Allah ya tona asirinsu, duk mai hannu ga wannan aika-aikar . Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu ya kuma bai wa wadanda suka ji rauni lafiya.
Allah ya taimaki Arewa da al’ummar ma
Nijeria baki daya.
Wanda ya rubuta Hassan Muhammad
Binanchi,Sakkwato,/ [email protected]/08093994429.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya