Matsalolin Arewa: Shugabanni da mabiya mu ji tsoron Allah
Wani mai hikima ya ce: “Mutane da dama sun mutu amma halayensu na kirki ba su mutu ba. Wadansu mutanen suna raye cikin jama’a alhali matattu ne.” Muna da imanin cewa ba za mu tabbata a duniya ba amma aikin kwarai da shuka alheri sukan sa a tabbata ana tuna mai su a tsakanin mutane. […]
Wani mai hikima ya ce: “Mutane da dama sun mutu amma halayensu na kirki ba su mutu ba. Wadansu mutanen suna raye cikin jama’a alhali matattu ne.”
Muna da imanin cewa ba za mu tabbata a duniya ba amma aikin kwarai da shuka alheri sukan sa a tabbata ana tuna mai su a tsakanin mutane. Sukan gadar masa yabo da sanyawa a rika tuna shi da alheri da yi masa godiya da addu’o’i a rayuwarsa da bayan ya rasu.
Maganganu za su tabbata amma mutum ba zai tabbata ba. Idan muka yi nazari da wasu shugabannin Arewa da suka gabata, sun yi iyakar kokarin shimfida adalci, gaskiya, rikon amana da kaunar juna ga al’ummarsu, ba tare da sun nuna bambancin siyasa, kabila, addini ko bangaranci ba. Dalilin da ya sa a kowane lokaci aka tuna su, ake gode masu. Wadansu ma rana ake warewa a kowace shekara domin a tuna gudunmuwar da suka ba da, da yi masu addu’o’i.
Shugabanni irinsu Sa Abubakar Tafawa balewa, Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Janar Murtala Ramat Muhammad da Malam Aminu Kano. Kowannensu ya rike matsayi daidai da na Shugaban kasa ga jama’arsa amma har suka bar duniya ba wanda ya bar gidan haya, motar haya, gidan gona da ake kiwon dabbobi da tsuntsaye, kamfani ko kudin da suka boye a bankin Najeriya ko kasar waje. Sun sadaukar da kansu, sun yi aiki ba tare da gajiyawa ba ko ha’inci, domin ci gaba da farin cikin mutanen kasarsu. Sun yi rantsuwa da sunan Allah, idan har sun rasu ba za su bar komi ba sai gwagwarmaya domin ’yanci, mutunci da martabar mutanen Arewa da kasar Najeriya.
Shekaru sama da hamsin ke nan bayan shudewar wasu daga wadancan mutanen da muka ambata a matakin shugabannin kasa zuwa yau, mun kasa samun mutum daya da za mu yi kirari da alfahari, mu gwama sunansa da su ko da a matakin gwamnan jiha ko shugaban karamar hukuma a Arewa, duk da cewa gwamnonin da suka gabata da masu ci yanzu suna sane da ayyukan alheri da wadancan shugabannin suka yi.
Jihar Arewa ta lokacin wadancan shugabanni da take kunshe da larduna da yau suka koma jihohi 19 da kananan hukumomi 407, ba ta canza daga albarkar kashi 70 cikin 100 na adadin fadin Najeriya ba. Arewar nan ce ke da kashi 60 cikin 100 na yawan al’ummar kasar nan. Allah Ya albarka ce mu da sinadaran karkashin kasa har da man fetur da ake yi mana gori. Ga mu da faffadar kasa mai dausayi, muna sahun gaba wajen samar da dukiyar kasa mafi bunkasa, arzikin noma kiwo da kasuwanci amma abin takaici, rashin kishin zuci, rashin kishin kai, rashin kaunar juna da taimakon juna sun sanya duk mun watsar da su; musamman shugabanni masu jagorantarmu a mukaman ilmi, sarauta da siyasa.
Mun yi wa kanmu illa, mun kasa samun zaman lafiya. A Arewar nan ake rikicin Boko Haram, ake sace garken shanu, ake fadan kabilanci, ake fadan addini, ake garkuwa da mutane don samun kudin fansa, ake dirawa gidan masu kudi a yi masu kisan gilla, ake fashi a kasuwanni da kan hanyoyi; ake da sansanin ’yan gudun hijira, ake da mafi yawan mabarata, ake da koma-baya wajen samun sakamako marar kyau na jarabawar sakandare ta Afrika ta Yamma (WAEC). Mutanen jihohinmu ne suka fi talauci da fatara da rashin aikin yi.
Muna da akalla mutum biyar ’yan asalin kowace karamar hukuma a Arewa da kowannensu zai iya sadaukar da Naira miliyan daya daga kudinsa, ya raba wa mata 50, matasa 50, a ba kowannensu Naira dubu goma da za su yi jari a kankananan sana’o’i kamar tuyar waina, kosai, kuli-kuli, awara ko dan wake, cajin waya, wankin babur ko mota da sauransu amma a kullum masu bara da roko da maula na sarari da na boye sai kara rajista suke yi a tashoshin mota, sha-talai-talai, gidan buki da gidan ’yan siyasa.
Da za ka daure ka kai ziyara asibitocinmu na gwamnatin jiha ko na tarayya, za ka samu majinyata talakawa masu bukatar taimako. Wasu daga cikinsu talauci ya kai matakin da ba su mallaki abin da za a saida a kai su asibiti ba. Suna nan kwance da kunarsu, ba mai taimaka masu.
Lokacin da za ka ji ana hirar wani jami’in gwamnati ko mai kudi ya tafi Dubai, Masar, Jamus ko Indiya domin duba lafiyarsa, a wannan ranar sai ka ji sanarwar neman taimakon kudin magani daga masu hali a gidajen rediyo da talibijin, Naira dubu ashirin domin a yi mai aiki ko a ba shi magani ko a ceci rayuwarsa. Haka a wannan ranar za ka ji an biya wa wani ko wata sama da Naira miliyan daya da rabi, kudin aikin Hajji domin neman biyan wata bukata ta gidan duniya. A wannan ranar za ka samu tiya daya ta masara ta fi karfin makwabcinsa ko ’yan uwansa na jini.
Lokuta ba iyaka, za ka ji ana gudanar da taron shugabannin Arewa na addini, na sarauta, na siyasa da niyyar yaya za a shawo kai ko kawo karshen matsalar talauci, matsalar tsaro, matsalar rashin aikin yi ga matasa, matsalar rikicin addini, matsalar rikicin kabilanci, matsalar tabarbarewar ilmi, matsalar fyade, matsalar fadan makiyaya da manoma, matsalar shaye-shaye, matsalar yawan sakin aure. Matsaloli ga su nan har ka kasa lissafa yawansu bare magance su. Kai ka ce duk duniya Arewacin Najeriya ta fi kowa matsala.
Duk wata na Allah, gwamnonin Arewa na jira a ba su kason kudin jiharsu na man fetur daga hannun Gwamnatin Tarayya, su biya albashi, fansho, ’yan kwangila da sauran ayyukan raya kasa, alhali suna sane da cewa kasar Masar tana amfani da rowan teku da ya ratsa kasarta, mutanenta ke noma abincin da suke bukata, har su tallafa da saida wa wasu kasashen duniya. A wasu jihohin Arewa, buhun takin zamani da yawa manomi ke bukata amma wani lokaci sai an yigirbin amfanin gona takin gwamnati ke isa ga manomi.
Ba maganar takin zamani ba, iri mai kyau, maganin kwari ma ba a ko labarinsu bare motar tarakta da za ta yi haro ko noma da sai gonar mai girma, mai marta ba ko honorabul – amma kullum gwamnati cewa take yi talakka ya koma noma. Al’amarin magana da masana ke fada, “idan mutum ya gano matsalolinsa kuma ya sansu, to ya samu rabin maganinsu.” Babbar matsala ga likita ita ce, idan ya kasa gane irin cutar da ke damun majinyacinsa. Tambayarmu har kullum ga shugabanninmu, zuwa yaushe ne za su gano matsalolinmu? Idan kuma sun gano, zuwa yaushe ne za su fara daukar matakin magance mana su ko wasu daga cikin manyan matsalolinmu, domin samun saukin rayuwa?