Matsalolin Auratayyar Bahaushe 1
Assalamu Alaikum Makarantan mu, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, ina mana murnar idin Babbar Sallah, da fatan Allah Ya sa mun dace da dukkan alheran da ke cikin watan Zul’kadah, kuma Allah Ya kai mu ta badi cikin rayayyen imani da kwanciyar hankali, amin. Cikin yardar Allah za mu fara gabatar da […]
Assalamu Alaikum Makarantan mu, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, ina mana murnar idin Babbar Sallah, da fatan Allah Ya sa mun dace da dukkan alheran da ke cikin watan Zul’kadah, kuma Allah Ya kai mu ta badi cikin rayayyen imani da kwanciyar hankali, amin.
Cikin yardar Allah za mu fara gabatar da bayanai kan matsalolin auratayyar Bahaushe da kuma hanyoyin magance su. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da tambayoyi a kan haka, amin.
1. Matsalar Rashin Bayyanar Da Soyayya
Wannan matsala ta rashin bayyanar da soyayya ta zama ruwan dare a cikin rayuwar auratattar Hausawa, ta yadda ma’aurata kalilan ne suke rayuwar aure mai cike da nuna so da kauna a cikinsa. Ko a cikin iyali za a tarar yara kanana ne kadai ke samun dadaddiyar soyayya ta hanyar wasa da ake musu, yawan runguma da sumba; kalamai masu dadi da yawan yaba masu da sanya su murna ta hanyar murmushi da dariyarsu, haka da zarar ransu ya baci kuwa nan da nan za a rarrashe su, kuma ko sun yi laifi ba a rikonsu da laifin har ya sa a daina bayyanar musu da kaunar da ake masu. Amma su ma din suna girma irin wannan abubuwan suna raguwa har sai ta kai soyayyar da ake nuna masu kadai ita ce ta samar masu da duk abubuwan bukatarsu amma ba irin dadadan abubuwan da akan yi masu lokacin da suke kanana. Idan muka yi nazari za mu fahimci duk rai na dan Adam na bukatar irin wannan dadadan abubuwa, ba dan Adam kadai ba, duk halittun Allah SWT na bukatar yanayin kulawa irin haka.
Wannan fili ya yi ta samun koken wasu daga cikin ma’aurata kan yadda suke fuskantar wannan matsala daga wajen abokan zamansu:
“Na karanta bayaninki kan hanyoyin kayatar da maigida ranar sallah, na kuma aikata hakan amma maigidana bai nuna mini jin dadin abin da na yi ba, ya ma goge duk wani sakon nuna kaunar da na aika masa a wayarsa.”
-Maman Aisha
“Yanzu da gaske akwai irin matar da ke iya yi wa mijinta irin wadannan abubuwan nuna soyayya? In kuwa akwai, to sadakinta ko nawa aka sa bai yi tsada ba!”
-Wani Bawan Allah
“Na karanta bayaninki kuma na ba matana biyu sun karanta, amma ba lallai ba ne su aikata. Zan so a ce akwai wata makaranta ko aji da za a rika koya wa mata irin wadannan halaye, don ni dai ina bukatar su.
-A.M Wudil
Don Allah Yaya matata za ta fahimci wadannan abubuwan kuma ta rika yi mini su domin ni dai hakan na matukar burge rayuwata.
-M. Sani, Kano
Idan muka yi nazari za mu fahimci cewa haka abin yake a mafi yawa daga cikin ma’aurata Hausawa; yawanci ma’aurata ba su damu da bayyanar da so da kauna ga junansu ba, ta hanyar kalamai masu dadi da suka dace; wasanni da barkwanci, kulawa ta musamman da sauransu. Ko kuma ya kasance daya daga cikin ma’aurata na kokarin bayyanar da soyayya, amma daya bai nuna jin dadinsa balle har shi ma ya yi kokarin yin irin yadda ake masa.
Abubuwan da ke hana bayyanar da soyayya:
1. Al’ada: Yanayin al’ada na taka muhimmiyyar rawa sosai wajen rashin bayyanar da soyyaya a cikin rayuwar aure. A al’adance ba wata soyayyar da ake yi da ya wuce namiji ya samar da kayan bukatun rayuwa ita kuma mace ta kula da gida da yara; kowa yadda ya tashi ya ga ana yi a gidansu, a garinsu, haka zai yi, wanda ko duk aka ga ya fita daban ta hanyar yin abubuwan nuna kauna da kulawa nan da nan za a sami wani lakabin da aka yi masa saboda hakan.
2. Halin Mazantaka: Yanayin halayyar da namiji tasa ya fi iya nuna soyayyarsa da kulawarsa ta bangare daya kawai, shi ne ta hanyar sadaukar da dukiyarsa, lokacinsa da karfinsa ga iyalinsa; wannan kam lallai shi ya fi muhimmanci kuma ya fi amfani, amma dayan da ba su cika yi ba, shi ya fi dadi da sa kwanciyar hankali da aminci a zuciya.
3. Tsoro: Wannan shi ne ja gaba daga cikin abubuwan da ke hana ma’aurata bayyanar da soyayya tsakaninsu; yawanci ma’aurata maza na ganin bayyanar da soyayya, kamar bayyanar da rauninsu ne, kuma hakan zai sa matan su raina su, su kuma daina ba su kima. Su kuma matan na tsoron in su cika bayyana soyayyarsu, mazan za su dauke su ba bakin komai ba, kuma ba za su samu irin kulawar da suke so ba daga gare su.
4. Rikon laifi: Kasawar wasu ma’auratan ga yafe laifin da ma’auransu suka yi musu na hana su iya bayyanar da soyayyarsu, domin rikon laifi na dakushe soyayya ko ma ya sumar da ita gaba daya.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.