Matsalolin da muke fuskanta a Manara Tb – Shugaban Manara
Tashar talabijin ta Manara da kungiyar Izala ta kafa don yada shirye-shirye masu nasaba da addini ta samu matsalar da ta kai an daina ganinta na wani lokaci kafin sake dawowarta. Aminiya ta zanta da sabon Babban Daraktan tashar, Alhaji Bashir Muhammad Sule wanda ya shekara sama da 30 a fagen aikin jarida kafin ya […]
Tashar talabijin ta Manara da kungiyar Izala ta kafa don yada shirye-shirye masu nasaba da addini ta samu matsalar da ta kai an daina ganinta na wani lokaci kafin sake dawowarta. Aminiya ta zanta da sabon Babban Daraktan tashar, Alhaji Bashir Muhammad Sule wanda ya shekara sama da 30 a fagen aikin jarida kafin ya yi ritaya. Ya yi bayani a kan halin da tashar ke ciki da kuma tsare-tsarensa na inganta ta.
Aminiya: Da farko sai ka gabatar mana da kanka.
Sunana Bashir Muhammad Sule. Ni dan asalin garin Zariya ne, a can aka haife ni yanzu ina da shekara 64. Na fara makarantar furamare a Kawo LEA na karasa a Rigacikum duk a garin Kaduna. Bayan nan na tafi Kwaleji na grade II, bayan na gama sai na yi aikin koyarwa kamar na shekara daya sai na wuce Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, inda na karanta fannin tsare-tsaren gabatarwa wato ‘Design Production’ wanda ya kunshi tsara abubuwa ciki har da na shirye-shirye na kafofin yada labarai, na gama a 1978. Na yi aikin hidimar kasa a Jihar Ribas a 1979.
Bayan nan sai na kama aiki a NTA Kaduna inda na yi ayyuka a bangaren tsara shirye-shirye da suka shafi rubutawa. Ina wajen sai aka min sauyin wurin aiki zuwa kwalejin NTA dake Jos a matsayin shugaban shashen koyar da shirye-shirye na makarantar, inda za a koyar da dalibai akan abin da ya shafi Production da Presenting da sarrafa camera har zuwa directing. Bayan nan sai na fada bangaren gudanarwa aka ba ni mukamin Babban Manaja na NTA Zariya da aka shirya kafawa a lokacin, inda na jagorancin aikin kafata kama daga neman wuri da gina wajen har zuwa fara shirye-shirye. Bayan nan sai a ka min sauyin wurin zuwa NTA Gusau, wanda babbar tasha ce da ta kunshi jihar Zamfara baki daya. A na nan sai a ka bude cibiyoyin yanki-yanki wato zone na NTA, inda aka tura ni shiyyar Sokoto a matsayin Mataimakin Darakta mai kula da NTA na wancan shiyyar.
Bayan nan sai a ka sauya min wurin aiki zuwa NTA Birnin Kebbi tare da karin girma na mukaddashin darakta, na yi kamar shekara uku a wajen sai aka dawo da ni hedikwata Abuja, inda aka bani mukamin babban mai kula da sashen adana shirye-shirye wato ‘Head of Archibal Department’ mun yi ayyuka da suka shafi tattara shirye-shiryen baya, tare da digitalizing dinsu don adanawa ta yadda za a rika zakulo su cikin sauki a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Na samu kamar shekara daya da rabi a wurin kafin aka turani zuwa Maiduguri a 2012 a matsayin darakta mai kula da tashar NTA na shiyyar.
Na samu garin Maiduguri a karkashin dokar ta baci inda a ke tashi aiki karfe 5 na yamma a NTA, sannan dokar ta kare da karfe 7 na safe. A lokacin da na je wajen ba a labarai, zuwana ne na yi tanadin wajen kwanan ma’aikata a ofis tare da samar da abinci, hakan ya bada damar da aka dawo da shirye-shiryen dare da suka hada da labaran gida da karfe 7 sannan idan tara ta yi mu bada gudunmawa ga labaran kasa da ake aiko mana daga wurare irinsu Yobe da Gombe da Yola mu hada da namu mu tura Abuja. Ina kuma wajen ne shekarun ajiye aikina ya yi na yi ritaya na koma gida. Sannan a watan Yuli na wannan shekara aka neme ni a nan Manara Tb don na bada gudunmawa.
Aminiya: To a wane irin hali ka samu tashar, kuma wadanne tsare-tsare ka faro don inganta ta?
A gaskiya na samu wajen da wasu matsololi. Na farko bayan an kaddamar da tashar ta yi aiki na wani lokaci sai kuma ta tsaya. Ba a jima da farfado da ita ba kenan sai aka kawo ni. Zuwana na samu matsalolin rashin sanin makamar aiki ga masu sha’awar son aikin, amma kuma akwai karancin sanin yadda za a aiwatar da shi. Sannan cikin wadanda suka san aikin da aka faro wajen da su, sun wuce ko kuma an sallame su. To abu na farko da na fara yi shi ne harhada tsoffin shirye-shiryenmu da muke da su, duk da cewa wasu sun makale a wasu wurare ba a karasa su ba, kuma babu yadda za a karbo su. Da ma shi shirye-shiyen talabijin ana sake sanya shi jifa-jifa, musamman ma dai irin wadannan na addini, kasancewar bayanansu ba sa tsufa. Abu daya da mai kallo ba ya so shi ne yawan maimaita abu guda a kodayaushe. Sannan a yanzu haka tuni muka fara yin wasu sabbin shirye-shirye kuma wasu maluman sun yi mana alkawarin za su zo mu sake daukar wasu sabbi da su da zaran sun huta bayan dawowa daga aikin hajji, kuma ina sa ran cewa nan da kamar mako guda za mu fara insha Allahu.
Aminiya: Kamar wadanne irin shirye-shirye ne ku ke yi a Manara Tb, kuma wadanne ne ka ke sha’awar shigo da su?
Shirye-shiryenmu masu nasaba da addini ne wadanda suka kunshi tafsirai, kuma kamar yadda na maka bayani a baya su ba sa tsufa. Idan ka kula akwai tafsirai irin na Sheikh Ja’aafar da ma na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi wanda rasuwarsa ya daura shekara 30 a yanzu, amma kullum ka sanya sai ka samu abun karuwa a ciki. Akwai kuma bangaren Fikihu da Hadisi da dai sauransu. Akwai na wanda mata ke gabatarwa da ya shafi al’amuransu kai tsaye. Sai kuma filin yara da mu ka dawo da shi, da Hausa ba dabo ba, inda a ke hira da manyan masana harshen Hausa, da filin nishadi wanda fadakarwa ce ta hanyar wasan kwaikwayo, da bayani akan dabbobi daga masanansu wanda ya kunshi bayani a kan rayuwar dabba da sauransu, da shirin sana’a huce takaici, don kwdaitar da mutane a kan sana’a, da al’amuran noma da dai sauransu. Ba ma yin labarai sai dai abinda a ke kira News bar, inda a ke sako labarai a rubuce daga kasa suna wuce wa.
Aminiya: Jama’a na korafin rashin kama tasharku a kafar da a ka saba, shin me ke faruwa?
Tsarin tashar Tb na tauraron dan Adam ya gaji sauya kafar da aka saba kama shi zuwa wani sabon kafa daban. Sai dai abin da ya faru a lamarin Manara shi ne: Wadanda su ka yi aikin kafa tashar sun shiga wata yarjejeniya a tsakaninsu da kafar yada tashoshin talabijin na Nilesat na tsawon wani lokaci kamar yadda aikin kwantaragin ya nuna. To bayan wa’adin ya cika sai alakar mu da Nilesat ya kare mu kuma da mu ka tashi sabuntawa sai mu ka koma na kafar Eutelsat wanda ke gudana a kan tsarin kati. Kuma daga baya-bayan nan mun kara da kafar NIGCOMSAT wanda ba sai an sa masa kati ba, sai dai ya na bukatar irin akwatin decoder da ake samun su. Kuma abin da jama’a ya kamata su sani shi ne al’amarin gudanar da tashar Tb irin wannan na bukatar makudan kudi don biyan kamfanonin yada shirye-shiryen a duk shekara baya ga dawainiyar gudanar da shi. Lalle Manara kasancewarta tasha ce ta addini, a na samun masu bada gudunmawar taimako na fisabilillahi wanda ya na taimakawa a wajen gudanar da ita, sai dai akan samu lokaci da abin da aka samun zai gaza, to wannan shi ne ya tilasta yin amfani da hanyoyin zamani irin na tsarin kati don samawa tashar kudin gudanarwa wanda zai taimaka idan aka hada da wancan da ake bada taimako, sannan idan aka samu rarar kudi sai a ci gaba da inganta wajen.
Aminiya: Wace hanya ku ke bi wajen sayar da katin ga jama’a?
Mu na da dillalanmu a dukkan jihohi da mu ke tallata sunayensu da lambobinsu na waya da kuma inda za a same su a labaran da mu ke rubutawa na News bar. Akwai na wata daya da a ke sayarwa akan naira dubu daya akwai kuma na shekara akan naira dubu 12 sai dai mu na shirin yin ragi akan na shekaran don kwadaitar da jama’a su rika sayansa. Kuma Alhamdulillahi yana samun karbuwa ga jama’a bakin gwargwado.
Aminiya: Wadanne rin nasarori za ka iya cewa an samu tun bayan kafa tashar zuwa yanzu?
Nasarorin su na da yawa. Na farko dai ya saukaka hanyar isar da sakon wa’azi cikin sauki tare da kaiwa ga wadanda ba lallai ne a samu lokacinsu ba idan ba ta irin wannnan hanya ba. Ya kuma karawa kungiyar Izala kwarjini ta kowace fuska tare da fitar da al’ummar musulmi baki daya daga kunya. Manyan mutane na zuwa wuraren wa’azuka na jiha ba sai na kasa ba fiye da baya a sakamakon tallata taron da a ke yi kafin yinsa da kuma saka shi da ake yi bayan an yi. Sannan mu na da kwamiti na Manara da ke da masu zuwa wuraren tarukan addini su na daukan shirye-shirye su aiko mana da shi nan mu sanya matukar ingancinsa bai gaza ba duniya ta gani. Sannan su kansu gwamnotocin jihohi na gayyatarmu zuwa aikin na musamman inda mu ke aika ma’aikatanmu daga nan Abuja su je su dauka a biya sai a saka matukar bai kauce tsari ba, duk wannan cigaba ne da tashar ta kawo. Ana kuma kama mu a daukacin Afirka ta yamma sannan kuma zuwan NIGCOMSAT a yanzu, za a iya kama mu har kasashen kudancin Afirka, sannan shirye-shirye sun yi nisa wajen hada zumunci da wasu kafofi dake Gabas ta Tsakiya ta yadda za a iya kama mu a yankunan kasashen larabawa duka.
Aminya: Ya kuma bangaren matsaloli ko kalubale?
Babbar matsalarmu ba za ta wuce ta kudi ba, wanda da shi ne za a samu irin kayan aikin da ake bukata da kuma gudanar da tashar, ana nan ana tsara yadda za a kyautata lamarin don inganta shi insha Allahu.