Matsalolin da suka haifar da karancin fina-finan Hausa a 2014

A wani bincike da Jaridar Aminiya ta gudanar ta gano an samu karancin fina-finan Hausa a kasuwa a shekarar 2014 da muke ciki.Aminiya ta gudanar da binciken ne cikin shekara uku, wato daga shekarar 2012 da 2013 da kuma 2014. Wadansu sun alakanta karancin fina-finan a kan matsalar satar fasaha da barkowar fina-finan Hausa-Indiya da […]

Matsalolin da suka haifar da karancin fina-finan Hausa a 2014
Matsalolin da suka haifar da karancin fina-finan Hausa a 2014

A wani bincike da Jaridar Aminiya ta gudanar ta gano an samu karancin fina-finan Hausa a kasuwa a shekarar 2014 da muke ciki.
Aminiya ta gudanar da binciken ne cikin shekara uku, wato daga shekarar 2012 da 2013 da kuma 2014.
Wadansu sun alakanta karancin fina-finan a kan matsalar satar fasaha da barkowar fina-finan Hausa-Indiya da karanci/karyewar jari da hassada tsakanin ’yan fim da kuma rashin kyakkyawan shugabanci a bangaren ’yan fim.
Wadansu kuma sun dora laifin karancin fina-finai a kan ’yan kasuwa da ke handame kudin wadanda suka shirya fim, kodayake wadansu sun ce Hukumar Kare Hakkin Mallaka ta Najeriya da Hukumar Tace Fina-finai ta kasa da kuma ta Kano sun taimaka wajen samun karancin fina-finan Hausa a kasuwa, kasancewar sun zama kamar kyanwar Lami wajen yaki da satar fasaha.
Babban Daraktan Zartarwa na Hukumar Tace fina-finai na Jihar Kano, Alhaji Ahmad dahiru Beli, ya ce hukumarsu ta tace fina-finai 902 daga shekarar 2012 zuwa 2014, amma an fi samun karancin fina-finai a shekarar 2014.
Ya ce, a shekarar 2012 hukumar ta tace fina-finai 312; na barkwanci 120, na santimental 192. A shekarar 2013 ta tace  fina-finai 386, inda ta tace fina-finan barkwanci 134 na santimental kuma 252. A bana kuwa zuwa watan Satumba hukumar ta tace fina-finai 204, na barkwanci 106 na santimental 98.
Beli ya ce wannan babbar nasara ce domin hakan ya nuna cewa kalilan ne idan har ma da akwai fina-finan da suke wucewa ta bayan gida ba tare da sun tantance su ba.
Ya ce alkaluman sun nuna cewa daga wancan lissafi, sukan tace kimanin fina-finai 72 a kowane wata ke nan, sannan a tsawon wannan lokacin kashi 40 cikin 100 da suka tace, wato kimanin fina-finai 360 na barkwanci ne, inda kimanin kashi 60 cikin 100 na fina-finai masu motsa zuciya da kuma ban tausayi ne, wato kimanin fina-finai 542 ke nan.
Ya ce: “Abin da mukan samu a wasu ’yan lokutan kawai shi ne kokarin tsawatar wa masu shirya fim don su guji aro baki ko sababbin al’adu na zamani da ba su dace da al’adunmu ba. Laifuffuka da gyararrakin da muka samu a wannan lokacin ba masu yawa ba ne, domin kuwa a shekarar 2012 mun gurfanar da sanannen dan fim Sani Danja a gaban kotu don ya ki gyara abin da muka ce ya gyara a fim dinsa mai suna ‘Gudaliya’, sannan a bana mun gyara sunan fim din ar-Rahuz daga ‘Cakwala Dadi’ zuwa ‘Muna son juna.”
Kamal S Alkali shi ne shugaban kamfanin Kamal International da ke shirya fina-finan Hausa ya ce, matsalar fina-finan Hausa-Indiya ta kusa durkusar da harkar fim gaba daya.
“Fina-finan Hausa-Indiya da satar fasaha sun kusa mayar da harkar fim tarihi, idan har Hukumar Kare hakkin mallaka ba ta yi wani abu kai ba, to nan gaba kadan za mu daina katabus.” Inji shi.
Sani Rainbow babban dan kasuwa a harkar fim ya ce hukumar kare hakkin mallaka ba ta aikin da ya kamata ta yi, shi ya sa fina-finan Hausa suka yi karanci a kasuwa, saboda babu wanda zai zuba kudinsa a karshe ya san faduwa zai yi.
Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa hassada da rashin shugabanci na daya daga cikin dalilan da ya sa Kannywood ke cikin halin la’haula.
“Yan fim sun ki hada kansu, sai girman kai da nuna isa, babu wata kungiya da ke jajircewa wajen ganin an yaki satar fasaha da fina-finan Hausa Indiya, idan ba a gyara ba, nan gaba za a yi ’ya kwance, uwa kwance.” Inji majiyar.