Matsalolin da suke janyo mutuwar aure a kasar Hausa da kuma hanyoyin magancesu (1)
Hakika ina jin takaicin a yadda yau aka wayi gari mace-macen aure ya yi yawa musamman a kasarmu ta Hausawa ko in ce matanmu na Hausawa, musamman idan ina kallon sauran yarurruka a fili ko a fim. Babban abin da yake kara daga min hankali shi ne yadda za ka ga kafin aure, mace lokacin […]
Hakika ina jin takaicin a yadda yau aka wayi gari mace-macen aure ya yi yawa musamman a kasarmu ta Hausawa ko in ce matanmu na Hausawa, musamman idan ina kallon sauran yarurruka a fili ko a fim. Babban abin da yake kara daga min hankali shi ne yadda za ka ga kafin aure, mace lokacin da mace take gidansu ana shan soyayya rigidi- rigidi, a wuni ana chatting a waya, dare na yi a taho zance, duk wata kulawa ana yiw a juna yadda yakamata amma da zarar an yi aure an dan gama cin amarci, an gama rububin juna, sai ka ga an fara samun sabani. Kamar da wasa sai ka ga ba a shekara ba sai ka tarar sun ishi juna daga nan sai taruwar matsaloli daga nan kuma sai ji ji saki ya auku. Wa iyazu billah.
To abin tambaya a nan ita ce me yake jawo haka? Me ya sa mata zawarawa suka yi yawaa kasarmu ta hausawa? Wani abin tausayi shi ne yau har an wayi gari duk da kunya da kawaici irin na ’ya mace sai ka ji mace bazawara ta fito gidan radiyo tana tallar kanta wai idan da mai so ya kawo kansa su sasanta.
To a bisa nazari da binciken da na yi abubuwan da na fahimta suke janyo yawan mace- macen aure a yau suna da yawa kuma ba bangare daya ne kawai yake da laifi ba, kowanne bangare yana da nasa laifin.
Abu na farko da na nazarta shi ne kwata-kwata auren ba a gina shi domin Allah ba. Wasu sun gina shi akan karya, wasu kwadayi wasu kuma domin wasu abubuwa da yake hange a tattare da macen wanda suke burge shi wanda da zarar an yi auren ya ga ba yadda ya zata ba, to sai ta fi ta daga ransa sai ya fara yi mata wulakanci daganan ya saketa.
Wannan maganar da na fada ba ina nufin kowa ba, ina magana akan mafi yawancin mutane.
Sannan abu na biyu wanda shi ma yake taka rawar gani wajen mutuwar aure shi ne kwadayayyun iyaye. Sai ka ga mai kudi yana neman auran yarinya ko ba ta so iyayenta za su tursasa mata sai ta aure shi saboda kwadayin abin hannunsa, ba za a tsaya a yi kyakyawan bincike ba saboda yanad a kudi, sai a dauki yarinya a aura masa, wanda a karshe sai irin wannan aure ya zama na nadama. Da ta shiga gidansa sai ya fara gwada masa irin halayensa na cin mutunci daga nan kuma sai saki ya biyo baya.
Abu uku kuma shi ne karya. Namiji zeai je ya yi ta yi wa mace karya, ya rudeta ta don ta aure shi wanda da zarar an yi auran sai ta tarar da sabanin abin da yake mata karyarsa daga nan sai ka ga an fara samun matsala, daga nan sai saki.
Abu na hudu shi ne rashin hakuri tsakanin ma’aurata, shi ma yana taka muhimmiyar ruwa.
Abu na biyar shi ne rashin iya rike juna da amana da tattala juna da nuna wa juna soyayya daga dukkan bangarorin biyu. Sannan kazanta tana taka rawar gani wajen mutuwar aure, musamman daga bangaren mace.
Akwai abubuwa da yawa wanda yakamata mu lura da su domin magance wadannan matsaloli na mutuwar aure.
Hakika aure wata hanya ce wadda ake samun aljanna a cikin sauki a cikinta sai dai ya danganta yadda ma’aurata biyu suka tafiyar da auren cikin tsoron Allah. Haka nan saki shi ma halal ne amma ba a son yinsa a addinance domin Allah SWT ba ya son a yi saki domin duk lokacin da aka yi saki sai Al’arshin Ubangiji ta girgiza.
To da wannan dalilai ya sa saki ya zama abin ki wanda ba a son sa sai ya zama dole domin akwai matakan da shari’a ta ajiye yadda za ka bi da mace wanda har in ta bijire to sai a saketa. Amma ba yadda ake yin saki birjik a halin yanzu ba, babu wata hujja mai karfi.
A nan nake kira ga maza su ji tsoran Allah domin su ne suke yin saki domin mace bat a sakin kanta sai dai namiji ya saketa.
’Yan uwana Musulmi maza ku sani cewa mata ba abun wulakantawa ba ne kamar yadda kuka mayar da su a yau. Kowace mace idan ka yi hira da ita za ka ji irin izayar da take ciki a wurin mijinta, idan ka ji na wannan, sai ka ji ai na waccan ya fi muni.
An wayi gari mata a wulakance wasu mazan sun maid a mata tamkar riga idan ya sa waccan, ya sa waccan. Wallahi wannan musiba ce kuke jawo wa kanku don wannan ba burgewa ba ce.
Kamar yadda Manzon Allah (SAW), yake fada a hadubarsa ta ban-kwana ina imuku wasicci da alkairi ga mata. To ku ji ’yan uwa yanzu tun da Annabinmu ya fadi wannan, mata yakamata su zamo abun wulakantawa? Annabinmu mu ne fa ya fadi wannan! Kuma kar ku manta duk rintsi mata ne suka haifeku.
Ina nasiha akan masu wannan dabi’a ta wulakanta mata akan su daina. Mace tana da daraja, kalmar mace tamkar zinariya take wajen yin walkiya a kowane lokaci.
Mata suna da sinadarai wadanda suke da tasiri, a cikin al’umma wanda har ta kai sun samu matsayi babba.
Mata suna da wani launi mai juya mazaje tamkar linzamin doki, komai matsayin mai mulki ko kudi ko sarauta.
Domin akwai wasu darajoji wanda mata suka dara maza. Abu na farko shi ne mece ce ta fara karbar Musulunci kuma ta yi masa hidima da dukiyarta. Ita ce Nana Khadija. Mace ce sanadiyyar samun taimama a shari’a, Nana A’isha. Mace ce ta ilimantar da Sahabbai bayan wafatin Annabi (SAW), Nana A’isha (rta). Mace ce ta zamo ma’auni na aure, wanda zai gwada kimarsa a wurin mahallinsa idan ya kyautata mata yana da sakamako mai kyau idan kuma ya cuceta akwai ukuba daga Allah.
Sannan kuma duk matsayin mutum sai da ita yake samun kima a idon mutane, kuma namiji b azai taba samun nutsuwa ba sai da ita, kamar yadda ita ma ba za ta taba samun natsuwa ba sai da shi.
Amma kuma a yau mata sune abun wulakantawa? Su ake saki birjik ba ji ba gani! Abin tambaya a nan ita ce zalunci ne ko rashin ilimi ne ko kuma rashin wayewa ne?
Hanyoyin da nake ganin yakamata maza su rike wurin kyautata zaman aure da magance saki su ne: Na farko a yi aure domin Allah. A daure, a rika hakuri, domin Kakanninmu abin da suka ci ribar zama kenan, domin a zamaninsu kafin a ji an yi saki aiki ne ja.
Ku daraja mata ku lallashesu,duk abinda suka yi ku yaba, idan suka yi kuskure ku yi masu nasiha, ba fada ko saki ba. Idan suka kyautata muku ku nuna sannan ku gode bayan kun sanya musu albarka. Sannan a baiwa soyayya muhimmaci, a cire kunya domin soyayya ba ta tsufa sai dai masoya su tsufa a inda wasu kabilun suka dare mu Hausawa kenan.
Zan juya ga ’yan uwana mata domin ku ma kuna da naku laifin. Kamar yadda na fada da farko,kuma ku ji tsoran Allah, ku gina rayuwarku ta aure saboda Allah, ba don kwadayi ko son zuciya ba. Kada ki daga hankalinki ki bar gidan miji saboda za a yi miki kishiya. Wannan shirme ne da rashin wayewa, da kuma yunkurin jayayya da abin da Allah ya halatta.
Mu ji tsoron Allah, sannan a rika hakuri, ban da rainuwa, domin Annabi SAW ya ce mata za su shiga wuta, saboda kafircewa mazajansu wajen raina alkairin miji (Bukhari da Muslim).
Sannan mu guji kazanta. Mace ta rika yi wa mijinta kwalliya saboda Annabi Mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, mace ta kiyaye abin da mijinta zai ji yana ki, daga jikinta kamar baki, jiki, gashi. Kki so mijinki tsakaninki da Allah, ki tsare amanarsa da sirrinsa, ki bi duk abin da ya ce matukar bai saba wa shari’a ba. Ki guji fita ba tare da izininsa ba. Ki kiyaye mutuncinsa a ko’ina. Ki so iyayansa tamkar naki. Ki bai wa ’ya’yansa tarbiyya.
A nawa ganin, idan aka bi wadannan matakan za a rage yawan mace- macen aure insha Allahu. A karshe ina kira da mu ji tsoran Allah, daga dukkan bangarorin aure koda kaddara ta sa ki zama bazawara, ki kiyaye mutumcinki sai Allah Ya dube ki, Ya yi miki mafita tagari. Allah Ya ganar da mu gaskiya Ya ba mu ikon binta.
Daga ’yar uwarku a Musulunchi Saddika Habib Abba Lulu. 07014566386.