Matsalolin Ilmi A Najeriya: An bar jaki ana dukan taiki
Idan har ana bukatar a yi wa al’umma kisan gilla cikin ruwan sanyi, wanda ya fi annoba, ya fi halbi da bindiga, yake daidai da bama-bamai illa, to gwamnati ta toshe duk wata kofa da jama’arta za su samu ilmi. Yayin da ta samu nasarar sanya su cikin duniyar jahilci, ta samu damar danne masu […]
Idan har ana bukatar a yi wa al’umma kisan gilla cikin ruwan sanyi, wanda ya fi annoba, ya fi halbi da bindiga, yake daidai da bama-bamai illa, to gwamnati ta toshe duk wata kofa da jama’arta za su samu ilmi. Yayin da ta samu nasarar sanya su cikin duniyar jahilci, ta samu damar danne masu kowane ’yanci, ta hukunta, ta lankwasa, ta karya inda ba gaba.
A karshen kowace shekara, gwamnoni da Shugaban kasa a Najeriya suna gabatar da kasafin kudi domin aiwatar da ayyukan raya kasa da samar da kayan more rayuwa ga jama’arsu. Amma za ka samu fannin ilmi na samun kason da bai kai kashi 20 cikin dari na kasafin kudin ba, yayin da kasashen D8 da E9 da Najeriya ke cikinsu, suke ware wa ilimi kashi 20 ko fiye da haka a kasafin kudinsu.
Babu yadda za a manta da gudunmuwar da shugabannin farko na Najeriya suka yo na nazari kan tsarin ilmi da tallafin da suka bayar domin amfanin mutanen Najeriya ba. A dalilin haka ya kyautu duk wani gyara ga fannin ilmi, gwamnati ta yi la’akari da tarihin waccan “Manufar Ilmi Ta kasa” da manyan masana suka tsara, wadda ta yi cikakkun tanade-tanade na yadda za a bai wa al’ummar Najeriya ilmi.
Duba da cewa a kasashen duniya ba a san tsohon Shugaban kasar Zimbabuwe, Robert Mugabe a matsayin shugaban da ke gasa wa al’ummarsa aya a tafin hannu ba, amma kashi 90 cikin dari na al’ummar Zimbabuwe masu ilmi ne, wanda kuma shi ne adadi mafi yawa a kowace kasar Afrika a shekarar 2008.
Duk da yunkuri da ikirari da Gwamnatin Tarayya ke yi, na taron majalissar ilmi ta kasa da ta kunshi Ministocin Ilmi da Kwamishinonin Ilmi na jihohin tarayya 36, a karon farko cikin shekara 18 na mulkin demokuradiyya a Najeriya ne aka samu Shugaban kasa ya shugabanci taro na musamman na majalisar zartarwa a watan Nuwamba 2017 a fadar Gwamnatin Tarayya a Abuja. Taron mai taken “Ilmi A Najeriya: kalubale Da Abin Da Ake Fatan Ya Biyo Baya.”
A taron ne akan duba matsayin da ilmi yake ciki da inda ya dosa da kuma irin yadda za a tunkari kalubalen da ke tattare da shi da yadda za a gyara shi. Wannan bai hana a kowace rana ka ji korafe-korafe na fatar baki daga jama’a ba, har da yajin aikin malaman makaranta da ya zama barazana kan tabarbarewar ilmi.
Gwamnatoci ke da alhakin daukar nauyin kula da ba da ilimi ga al’ummarsu a kan kowane fanni da mataki. Sai ga shi gwamnati ta yi sake da sakaci har an yi masu sakiyar da babu ruwa, kasancewar sun ba masu kudi lasisin gina makarantun renon yara da aka zura wa ido suka girma suka bunkasa ya zuwa jami’o’i.
Wadannan makarantu na masu zaman kansu, wurinsu ne duk wani da yake da wadata kuma ya damu da dansa ya samu ingantaccen ilmi yake kai ’ya’yansa domin su samu ingantaccen ilmi kafin daga baya ya tura su kasashen waje. Kuma wadannan shugabannin ne talakawa ke yaudarar kansu cewa za a inganta ilmi a makarantun da ’ya’yansu ke karatu?
A bisa wannan dalili, an wayi gari yau Najeriya na da jami’o’i 117 cikinta, 36 daga cikinsu mallakar Gwamnatin Tarayya ne, wasu 36 mallakar gwamnatocin jihohi ne, yayin da sauran 42 mallakar masu zaman kansu ne. Ta kasance akwai jiha daya a Kudancin Najeriya (Ogun) da ke kunshe da jami’o’i 15, yayin da wata jihar a Arewacin Najeriya na kunshe da jami’o’i 3.
kananan hukumomi da gwamnatocin jihohi su ne jigo kuma kashin bayan da za a fara gyara ilmi mai inganci a matsayin harsashen gini. Amma haka ba za ta samu ba sai an daina yaudara, an fuskanci gaskiya, adalci da rikon amana daga shugabanni da mabiya. A wadata kayan aikin da za a gina ilmi da suka hada da wadataccen fili da za a gina makaranta a zagaye ta da bango, a gina wadatattun azuzuwa don kauce wa cunkoson dalibai. Gina dakunan gwaje-gwaje da kaya da sinadaren gwaje-gwajen, dakunan karatu da wadatattun littattafan darussan da ake koyarwa, wadatattu kuma ingantattun dakunan kwanan dalibai, gidajen malamai, masashe, filayen wasanni da kayan wasanni, kayan koyarwa da malamai ke bukata, gyara gine-ginen da suka lalace, wutar lantarki, ruwan famfo, dakin shan magani da malamin jinya ko likita, matakan tsaro, sai uwa-uba wadatattu kuma kwararrun malamai, kwamfutoci, masu abinci, banki da sauran bukatun karatu mai inganci tun daga firamare zuwa jami’a.
Amma abin takaici, ban haushi da al’ajabi, duk ikirarin da wasu gwamnatoci ke yi kan gyaran ilmi, a makarantun Arewan ne za ka samu makaranta mai gini daya ko biyu sama da shekara ashirin ko tun tsarin U. P. E. na shekaru 40 da suka wuce. Za ka samu gara ta cinye katako da silin, kwanon rufin ya yi tsatsa, wani rufin ya kware. Bangon ginin ya tsattsage ya zama maboyar kadangaru. Karyayyun kujeru da tebura suna nan jibge a filin makaranta. Rashin kewaye, rashin kayan koyarwa. Ba maganar masu daukar karatu kasa ake yi ba, da masu daukar darasi a karkashin bishiya ba – wannan ya zama kwalliya. An halatta cinkoson dalibi 80 zuwa 100 a aji daya domin daukar darasi, wadanda ba su samu wurin zama a aji ba suna da lasisin su zauna a ‘bencin-hajiya’ (taga).
Samun wadatattu kuma kwararrun malamai na daya daga cikin matakan da za a samu ilmi mai inganci. Haka ba za ta samu ba sai idan gwamnatoci sun maido da makarantun horon malamai, makarantun fasaha, addini da koyon sana’o’i.
Daga nan sai gwamnatoci su rike amana tsakaninsu da mahaliccinsu kan biyan manyan bukatun malamai na albashi, fansho, biyan alawus, karin girma, taron bita da karo karatu a kan kari. Idan hali ya yi, a rika karrama wadanda suka yi fice da zarra kan tallafa wa ilmi da tsare aiki akalla bayan kowace shekara biyu.
Gwamnatin tarayya na ikirarin yara miliyan 13 ne ba su zuwa makaranta a Najeriya a kiyasin shekarar 2017. Idan haka ne to ina makomarsu? Ina makomar wadanda za su biyo bayansu? Ina makomar wadanda suka yi karatun har zuwa jami’a, da NCE da difloma da suka kwashe shekaru da kammala karatun ba aikin gwamnati, ba jarin sana’a, ba mai taimakawa? Amsa ita ce, inda akuyar gaba ta sha ruwa, ta baya ma a nan za ta sha.
Kasancewar kashi 60 cikin 100 na mutanen Najeriya ’yan Arewa ne kuma ya kasance mafi yawansu suna rayuwa cikin karkara, fatara, talauci da jahilci sun yi masu daurin huhun goro, duk da haka suna kokarin tura ’ya’yansu makarantun gwamnati duba da bukatun yaran da a kullum safiya a ba da kudin tara, littafin rubutu ya cika, biro ya kare, wando ko rigar makaranta ta kece, babu jikkar zuba littattafai, takalmi ya cire, tayar keke ta yi faci. An ce a ba da kudin hoto, kudin tsintsiya, kudin kwallo da sauran bukatun makabta. Kuma a karshen makarantar ko wasikar Hausa ba su iya karantawa bare ya rubuta, ba maganar cin jarabawa ake yi ba.
Gwamnatin Tarayya, gwamnatocin jihohi, kananan hukumomi, kwamishinonin ilmi, daraktocin hukumomin ilmi, malaman makarantu, shugabannin addini da na gargajiya, manyan ’yan siyasa, attajirai, ’yan majalisun dokoki na jihohi da na tarayya, ya zama wajibi mu dubi girman Allah mu duba abubuwan da suka lalace, suke bukatar gyara a fagen ilmi na kasar nan. A ba da karfi kan ilmin addini, ilmin koyarwa, ilmin fasaha da ilmin koyon sana’o’in hannu domin tallafa wa matasa da rayuwar dalibai bayan sun samu ilmin – maimakon a kullum “an bar jaki ana dukan taiki.”