Matsalolin jarrabawar shiga manyan makarantu a 2019
Duk da irin makudan kudi da lokaci da Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), ta dauka ko ta samu don shirya jarrabawar shiga manyan makarantu a bana ba tare da an shiga matsalaba, jarrabawar shiga manyan makarantu (UTME) da aka kammala kwanakin baya ya hadu da matsalolin kayan aiki da na na’urori wadanda suka […]
Duk da irin makudan kudi da lokaci da Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), ta dauka ko ta samu don shirya jarrabawar shiga manyan makarantu a bana ba tare da an shiga matsalaba, jarrabawar shiga manyan makarantu (UTME) da aka kammala kwanakin baya ya hadu da matsalolin kayan aiki da na na’urori wadanda suka dabaibaye gudanar da jarrabawar. Matsalolin da jarrabawar ta ci karo da su, sun hadar da na rashin fara jarrabawar a na’urar kwamfuta (CBT) a kan lokaci wanda ya hadu da rashin wadatattun na’urorin kwamfuta da za a yi amfani da su wajen rubuta jarrabawar da yawan daukewar da na’urorin ke yi yayin jarrabawar. Sai kuma matsalar nan ta tafiyar hawainiya wajen tantance masu rubuta jarrabawar, gabanin shigarsu dakunan jarrabawar.
A galibin cibiyoyin rubuta jarrabawar, bayanai sun ce an fara jarrabawar bayan sa’a daya ko kuma fiye daga aihinin lokacin da aka tsara. A cibiyar jarrabawar da ke Jami’ar Tarayya ta Dutse, an tsara soma jarrabawar da misalin karfe 1:30 na rana, amma ba a fara ba sai da misalin karfe 3:00 na rana. A dai Dutsen, wata cibiyar jarrabawar, na’urorin kwanfuta sun yi ta kashe kansu da kansu, a lokuta da dama. Dama dai, na’urorin kwanfuta, galibi kan nuna shafuka fayau, idan har an samu daukewar lantarki.
Moses Okokon, wani dalibi ne da ya rubuta jarrabawar a wata cibiya, a birnin Uyo, ya yi rakin yadda kwanfutocin da suke rubuta jarrabawar shi da wadansu abokansa, suka tsiya cik, bayan sun riga sun amsa tambayoyi kimanin 20. Wani da ya rubuta jarrabawar, cewa ya yi: “Sun tantance zanen yatsunmu da misalin karfe 1:30 na rana, amma mun yi ta jiran gawon shanu a waje har zuwa karfe 7 na yamma, ba wanda ya ce mana ko da ‘ku ci kanku’…….. Sai dai, da misalin karfe 8:30 na yamma, mun ci sa’a mun shiga dakin rubuta jarrabawar, amma ni kwamfutata, ba ta ko kunnu ba. Kodayake, wadanda suke zaune kusa da ni, nasu, sun bude, sai dai fayau allunan ke nunawa.
Wani uba, a Bauchi, ya gaya wa manema labarai cewa, a lokacin da dansa ya je harabar rubuta jarrabawarsa a ranar Asabar, an gaya masa cewar an dage jarrabawar zuwa ranar Litinin, zai samu sakon hakan ta wayar hannu. Amma bai dai ga wannan sakon ba, don haka ya sake garzayawa zuwa cibiyar rubuta jarrabawar a ranar Litinin din, kwatsam sai aka shaida masa cewa ‘ai an riga an gudanar da jarrabawar!’ Har ila yau, wani mahaifi, a dai Bauchin, ya ce dansa bai samu damar rubuta jarrabawar ba, a wata cibiyar jarrabawar ta Odford Science Academy, da ke kan hanyar Gombe, sakamakon yadda dakin rubuta jarrabawar ya yi cikar kwari, don haka aka umarci dansa da ya saurari umarni na gaba, da za a tura masa ta sakon waya, amma ya ce, shiru ka ke ji…An dai ce, dakin jarrabawar na da na’urorin kwamfuta 200 ne kawai.
A kuma wata cibiyar da ke cikin Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Abubakar Tatari Ali a Bauchin, wadansu masu zaman jarrabawar ba su samu damar haka ba, sakamakon yadda na’ura ta ki karbar zanen yatsunsu. Sai kawai aka gaya musu, su mika takardun shiga jarrabawar, kana su koma baya. Wani jam’in hukumar ta JAMB, ya fada wa manema labarai, cewa: “Mun ci karo da wasu matsaloli nan da can, wadanda ba su taka kara sun karya ba, inda na’urar tantance masu jarrabawar ta ki shaida wasu da suka yi rajistar rubuta jarrabawar.’’ Mummunan cikas din da ya fi muni, ya faru ne a cibiyar Global Distant Learning Centre, da ke daura da Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, a Abuja. A cibiyar ce wani jami’in hukumar ya tabbatar da cewa wasu tambayoyin darasin Physics, ba su da gurbin cankar amsoshi, sakamakon guraben amsoshin fayau suke a allunan kwamfuta. Kwatankwacin hakan ya faru a cibiyar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta ECWA da ke Jos. Jarrabawar ta bana, an fara rubuta ta ce a duk fadin Najeriya, a ranar Alhamis 11 ga Afrilu, zuwa Laraba 17 ga Afrilun 2019, ranar da aka tsara nakasassu za su rubuta jarrabawarsu. An kiyasta kimanin mutum miliyan daya da dubu 800 ne suka yi rajistar zaman jarrabawar, a cibiyoyi fiye da 600 da hukumar ta sahale musu a fadin kasar nan. Lura da irin bunkasar da hukumar ta samu wajen shirya jarrabawar ta hanyar amfani da na’urorin kwamfuta, a ’yan shekarun nan da kuma hada hancin sakamakon jarrabawar cikin sa’o’i 24 har ma da daina amfani da kati wajen rajistar jarrabawar, abin takaici ne matuka, a ce ire-iren kalubalen da suke ta kawo tarnaki ga gudanar da jarrabawar tun lokacin da aka kirkiro da gudanar da jarrabawar da na’urar kwamfuta, har yanzu su ne, suke ci wa hukumar tuwo a kwarya. Galibin kalubalen da masu rubuta jarrabawar suka ci karo da su, tushensu ya samo asali ne daga rashin kyawun yanayin cibiyoyin da hukumar ta sahale su gudanar da jarrabawar. Lallai ne Hukumar JAMB, ta kaddamar da bincike a kan dukkan cibiyoyin da aka ci karo da gagaruman matsalolin rashin soma jarrabawar kan lokaci ko kuma aka fuskanci matsalar daukewar na’urorin kwamfutar. Dole ne a hukunta duk wani jam’in hukumar da aka samu da laifin sahalewa cibiyar da karanta bai kai tsaiko ba. Lallai ne kuma hukumar ta dakatar da hada kai wajen shirya jarrabawar da kamfanonin fasahar sadarwa ta zamani (ICTs) da kuma makarantun Sakandaren da ba su kai munzalin shirya jarrabawar ba. Abin da ya kamata, hukumar ta yi a anan, shine ta takaita hada gwuiwar da Jami’o’I da Makarantun Fasaha da ma Kolejojin Ilmi, wadanda suke da wadatattun kuma ingantattun na’urorin kwamfuta ma su aiki, da yawa-yawan su ke jibge a sashen koyar da Kimiyyar Na’urar Kwamfuta da kuma sashen koyar da Injiniyanci. Hakan ka iya kawo karshen ire-iren kalubalen da aka ci karo da su a jarrabawar shekarar 2019.