Matsalolin jima’i ga dattawan ma’aurata
Yawan shekaru yana haifar da sanyin sha’awa da kuma sanyin gamsuwar ibadar aure.
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin.
Tambaya: Don Allah me mutum zai yi idan ba ya iya gamsar da matarsa saboda yawan shekaru?
Amsa: Fahimtar matsala rabin maganin da zai warkar da ita ce.
Don haka kai da uwargida ku fahimci cewa kamar yadda yawan shekaru ke canja yanayin jiki, hatta tafiya da sautin amon murya sukan canja saboda yawan shekaru, to haka ma yawan shekaru ke canja bangaren sha’awa da ibadar aure.
Yawan shekaru yana haifar da sanyin sha’awar ita kanta, sanyin gaba, saurin inzali da kuma sanyin gamsuwar ibadar aure.
Abin da a lokacin samartaka ake jinsa wutawuta sai ya koma garwashi ko ma toka-toka saboda gabatowar shekaru.
In ya kasance ita uwargida da sauran yarinta a tare da ita, shi ya sa ake samun wannan matsala, sai ta fahimci cewa haka yanayin yawan shekaru ya zo ga maigidanta, don haka ta sa hakuri da dangana a zuciyarta, don yawan damuwa da bayyana damuwar ba za su haifar da komai ba sai dai su kara dagula matsalar.
Musamman in ta tuna cewa akwai da yawan matan da suke auren matasa kuma suna fama da matsalar rashin samun gamsuwar.
Duk da cewa yanayin dan Adam ne raguwar karfin sha’awa lokacin tsufa, akwai wasu abubuwa da ke kara assasa tasirin haka:
Yawancin abin da ke haifar da matsalolin sha’awa ga dattawa shi ne raunin jijiyoyin jiki duka kuma musamman jijiyoyin al’aura.
Don haka sai a dage da yawaita motsa jiki a-kai a-kai, hanya mai sauki ita ce a yi tafiyar kasa ta tsawon minti 30 a kullum, sannan a rika motsa jijiyoyin al’aura, lallai wannan zai yi tasiri sosai wajen kara karfin sha’awa da rage aukuwar sanyin gaba ga dattawa.
Gabatowar shekaru na iya haifar da karancin sinadaran sha’awa cikin jini, binciken likita zai bayyanar da haka, in har hakan ta tabbata akwai kwayoyin da likita zai rubuta don samun karuwar sinadaran sha’awar.
Akwai wasu cututtuka da yawan shekaru ne ke assasa motsuwarsu kuma sukan yi tasiri kwarai ga ma’aikatar sha’awa, musamman ciwon suga na shafar jijiyoyin al’aura.
Sannan magungunan wasu cututtukan musamman hawan jini da ciwon suga na haifar da sanyin gaba, a irin wannan sai dai a yi aiki da umarnin likita
Tambaya: Ina fama da karancin maniyyi da rashin karfin gaba, a ba ni shawara.
Amsa: Abubuwan da ka iya haifar da raunin gaba da karancin maniyyi: Gabatowar shekaru na cikin abubuwan da ke haifar da rashin karfin gaba da rashin ruwan maniyya.
Don haka in an fara tara shekaru haka ya faru, to wannan haka tsarin al’adar jikin dan Adam take.
Amma in babu yawan shekaru, to abubuwa daban-daban ne ke haifar da haka da suka hada da: Karancin sinadaran sha’awa cikin jini, musamman in haka na faruwa hade da wasu cututtuka, kamar yawan gajiya, sanyin sha’awa da kuma tsotsewar gaba da maraina.
Sannan ciwon suga na haifar da raunin jijiyoyin jiki kuma kan iya sa hanyar fitar maniyyi ta dade maniyyin ya koma cikin mafitsara maimakon ya fito waje.
Cutar gwaiwa ma na iya haifar da karancin maniyyi da raunin gaba musamman wacce aka yi ma fida ko sakiya.
Haka nan shan magungunan hawan jini na iya haifar da wannan matsala don haka shawara ita ce a daure a yi wa likita bayani domin wannan matsala ce da take da sabubba daban-daban a likitance, binciken likita ne kadai zai bayyanar da musabbabinta da samar da maganin da ya dace.
Yawan cin kayan marmari, magungunan Musulunci, yawan cin kwadon ganyayyaki da kuma yawan cin farfesun kaza, farfesun naman shanu ko na rago da kuma romon ’yan shila na iya farfado ko kara karfin sha’awar da yawan shekaru ya sa ta lafa.
Tambaya: Idan lokacin sanyi ya zo gabana sai ya rika tsattsagewa da sanyi ya wuce sai ciwon ya mutu, wane irin ciwo ne wannan, sannan mene ne maganinsa?
Amsa: In dai lokacin sanyi kadai hakan ke faruwa, to wannan na nuna cewa akwai matsananciyar matsalar rashin isasshiyar lema a gaba daya jikin, yanayin hunturu kuma yana tsotse dukkan lemar da cikin sarari da kuma lemar fatar jikin dan Adam.
Abubuwan da za su taimaka don samun saukin wannan matsala sun hada da: A riki al’adar kula da fata a koyaushe ta hanyar tsabta da shafe dukkan jiki da mai ba sai lokacin hunturu kadai ba.
A rika sa gyauto na maza (wato pan ko dan diras na maza a ciki kafin a sa wando wannan zai ba da karin kariya daga busarwar da hunturu ke kawowa.
Yawan shan ruwa na kara yawan lema a jiki, yawan shayi ko naskafe kuma na rage lemar jiki don haka sai a kiyaye.
Haka nan yawan cin kayan zaki na rage lafiyar fatar jiki wanda hakan zai tasiri ga karantar man da fata ke sarrafawa don hana bushewa.
A guji wanka da ruwan sanyi domin hakan na busar da jiki, in ya zama dole a rika kashe zafi kadai.
Man kade na maganin bushewa da kaujen fata musamman in aka riki al’adar shafa shi sau biyu kullum, safe da yamma.
Da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.