Matsalolin Mata Game da Ibadar Aure (6)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaba da bayani a kan matsalolin mata game da ibadar aure, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, amin. Jin Zafin Ibadar Aure: […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaba da bayani a kan matsalolin mata game da ibadar aure, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, amin.
Jin Zafin Ibadar Aure: Idan ya kasance uwargida tana jin zafi lokacin ibadar aure, musamman idan zafin mai tsanani ne, to fargaba da tsoron wannan zafin zai dakusar mata da sha’awarta har ya kasance ta daina jin motsuwarta gaba daya, ballantana har ta iya kai wa ga biyan bukatar sha’awarta. Abubuwan da ke haifar da jin zafi lokacin ibadar aure sun hada da:
1. Rashin isasshiyar lema a ‘yan matanci: Idan ya kasance babu isasshiyar lema a ‘yan matanci, to uwargida za ta rika jin zafi lokacin ibadar aure.Ruwan maziyyin da kan zubo lokacin da aka fara jin motsuwar sha’awa, amfaninsa kamar amfanin man ‘grease’ ne a injina. Wasu cututtuka masu addabar jikin dan Adam, kamar su bushewar jiki, rashin isasshiyar lema a jiki, wani ciwo da ya shafi koda ko mahaifa, da gabatowar tsufa duk suna iya sa rashin isasshiyar lema a ‘yan matancin mace. Sannan rashin cin lafiyayyen abinci musamman ‘ya’yan itace da kayan lambu na iya haifar da karancin lema. Sannan tsoron jin zafin ma kansa, ko kin da uwargida ke yi wa ibadar aure na iya hana sarrafuwar ruwan da ke kawo lema. Hanyar kawar da wadannan ita ce, uwargida ta dage da cin kayan lambu da ‘ya’yan itace, ta kuma rika yawan shan ruwa, sannan ta cire duk wani tsoro ko fargabar jin zafi daga zuciyarta. Idan kuma da wani ciwo mai dangane da ma’aikata da injinan sha’awarta, to sai ta yi kokarin warkar da shi tukuna. Uwargida na iya amfani da man shafawa na basilin lokacin ibadar aure har kafin wannan matsalar ta kau daga gare ta cikin yardar Allah SWT.
2. Tsukewar ‘yan matanci: Wannan yanayi na iya haifar da jin zafin ibadar aure ga uwargida, watau ya kasance jijiyoyin dake kofar ‘yan mantancinta sun cika tsukewa sosai ko kuma sun cika tsauri don haka ba su ja su buda lokacin ibadar aure. Idan an fahimci hakan ne ke haifar da matsalar jin zafin, to sai a je a ga likita. Akwai ‘yar karamar tiyatar da za a iya yi don tafiyar da matsalar in Allah ya so.Haka kuma samfurin motsa jijiyoyin ‘yan matanci na kejel shi ma yana maganin tsaurin jijiyoyin al’aura ya kara masu laudi.
3. Salewar mafitsara: Saboda kusancin mafitsara da kofar ‘yan matanci, salewar wajen fitar fitsari, ko ya kumbura yana zafi, na iya haifar da jin zafin ibadar aure ga uwargida. Akwai magunguna da za su warkar da wannan nan da nan in an ziyarci likita.
4. Bankarewar jijiyoyin kofar ‘yan matanci: Wannan bankarewar jijiyoyi lokacin ibadar aure na haifar da tsananin zafi maras misaltuwa ga uwargida, wanda dole ta ji kwata-kwata ba ta kaunar ibadar auren.Sannan ga shi ba wai wata kwayar cuta ce take haifar da wannan ba illa dai wani kala kalar tunanin da ya yi karfi a zuciyarta game da ibadar auren, musamman idan akwai wani abu da take tsananin ki a ciki, kuma kin yayi karfi har zai sa jijiyoyin ‘yan matancinta, maimakon su yi lum-lum su kwanta yadda har za ta iya jin sha’awa, sai su bankare su haifar da tsananin zafi a gareta, da rashin samun isasshiyar gamsuwa ga maigidanta. Hanyar magance irin wannan matsalar ita ce, uwargida ta daure ta kawar da duk wata kyama, wani tsoro da duk wani karkatacce da birkitaccen tunanin da ta rike a zuciyarta game da ibadar aure, game da mijinta ko game da yanayin dangantakar da ke tsakaninsu.Sannan ta daure ta rika sakin jikinta lokacin ibadar aure; ta natsu ta kwantar da hankalinta, ta saita dukkan na’urorin kwakwalwarta a kan ibadar auren. Yau da gobe, in Allah ya yarda za ta ga ta yi nasara; ta daina jin irin wannan zafin.
Haka kuma wani babban maganin wannan matsalar shi ne, a dage, a rika motsa su wadannan jijiyoyin da samfurin motsa su na ‘kegel’, sai a nemi ‘yar karamar na’urar ‘kegel-master’ a rika yi a-kai-a-kai. Da fatan Allah ya sa a dace, amin.
5. Kumburi da salewar kwada na iya zama sanadin jin zafin ibadar aure ga uwargida, kuma da an warkar da wannan ciwo in sha Allahu za a daina jin zafin.
6. Fitowar yadin shimfidar mahaifa: Wannan shi ma yana haifar da jin zafin ibadar aure, kuma da an magance shi a asibiti, jin zafin zai tafi in sha Allah.
7. Salewar da kumburin labban ‘yan matanci na haifar da tsananin jin zafi lokacin ibadar aure.Wani lokacin har yakan zama ciwo mai tsanani sosai.Gwajin likita ne kadai zai tabbatar da irin kwayar cutar da ta haifar da ciwon, don magance ta da irin maganin da ya dace. Sannan rashin isasshiya da kuma cikakkiyar tsabtar wajen na daga cikin abubuwan da ke haifar da irin wannan ciwo. Haka wasu kayan zamanin da ake amfani da su kamar su sinadarin musamman don wanke ‘yan matanci ‘baginal douche’ yana iya haifar da wannan ciwo, domin yanayin halittar ‘yan matanci iri daya ne dana kwayar idon dan Adam, an halicce su da ruwan da ke wanke su ya fitar da datti ya turo waje.Kamar yadda muka san ba a sanya sabulu a wanko cikin kwayar ido, to haka ma bai dace ba wanko cikin ‘yammatanci da ‘baginal douche’ da ire-irensa.
8. Mannewar yadin cikin kugu guda biyu waje daya:Shi ma na iya haifar da jin zafin ibadar aure, amma da an yi tiyata an raba su shi ke nan ciwon zai warke in sha Allah.
9. Haka ma wasu cututtuka masu dangane da mahaifa; irin su ciwon kaba na mahaifa, watau ‘fibroid’ da kaluluwar cikin mahaifa ‘cysts’ duk suna iya sa jin zafi lokacin ibadar aure.Hanya mafi dacewa sai a je asibiti don a tabbatar da ainihin abin da ke haifar da hakan, da fatan Allah ya sa a dace, amin.
Allah ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.