Matsalolin maza game da ibadar aure (10)
Assalamu Alaikum wa Rahmatullah wa Barakatuh. Barkan mu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan dubarun da maigida zai yi amfani da su don ganin ya gwanance wajen iya jan ragamar sha’awarsa, wanda cikin yardar Allah […]
Assalamu Alaikum wa Rahmatullah wa Barakatuh. Barkan mu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan dubarun da maigida zai yi amfani da su don ganin ya gwanance wajen iya jan ragamar sha’awarsa, wanda cikin yardar Allah zai tafiyar masa da matsalar fitar maniyyi da wuri, matsala ta biyu kenan daga cikin matsalolin maza game da ibadar aure; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Dabara Ta 3: Ja Da Ajiye Dogon Numfashi:
Fitar numfashi da sauri lokacin gabatarwar ibadar aure na hayakar da sha’awa, hakan kuma ke haifar da fitar maniyyi da wuri. Jan dogon numfashi da sakin sa kadan-kadan kuma a hankali na rage karfin gudun sha’awa, ta yadda za ta tafi a hankali kuma daidai da lokaci. Wannan zai rage saurin fitar maniyyi da wuri. Sannan ja da ajiye dogon numfashi na tafiyar da fargaba da duk wani jin dar-dar da mutum ke ji a lokacin gabatarwar ibadar aure.
Dabara Ta 4: Tsaidau, Tsaida Matsala!
In an tuna a baya na taba yin bayani kan wannan haki mai suna tsaidau, mai matukar alfanu wajen inganta lafiyar ma’aikatar sha’awa gaba daya. Lallai binciken masana kimiyya ya tabbatar da ingancin wannan haki wajen tafiyar da matsalar fitar maniyyi da wuri. Dadin dadawa, wannan bishiya akwai ta ko’ina a kasar Hausa, sai kila canjin suna da ka iya samun ta a garuruwa daban-daban. A wani wajen ana kiran ta da *Hana Takama*. Don haka sai a nemi wannan bishiya ta tsaidau, kuma a nemi ilmin yadda ake amfani da ita daga wajen masu ba da maganin gargajiya don tsayar da matsalar fitar maniyyi da wuri, da fatan Allah Ya sa a dace, amin.
Dabara Ta 5: Shan kwayoyin SSRI!
A hakikanin gaskiya ba wani sanannen kwayar magani da likitoci suka tsayar a matsayin maganin fitar maniyyi da wuri, domin shi wata matsala ce da dabi’a da sabo ne suka haifar da shi, shi ya sa babban magani shi ne rabuwa da wannan sabon ko dabi’ar. Amma akwai wasu jerin magunguna da aka tanada musamman don maganin tsananin huzni, damuwa da kunci, daya daga cikin *tasirin* shan wadannan magunguna shi ne natsantar da lazzar sha’awar ta yadda tsananin jin ta zai ragu kuma za ta rika hauhawa a hankali, wannan na tafiyar da matsalar fitar maniyyi da wuri. Ga wanda yake ganin bai iya jurewa har ya horas da kan shi ya zamana ya iya jan ragama da sarrafa sha’awarsa, to yana iya zuwa ya ga Likita ya yi masa bayani don ya rubuta
masa ya kuma ba shi izinin shan daya daga cikin jerin wadannan magunguna da ake kira *‘Selectibe Serotonin Re-uptake Inhibitors.*’ Amma a fahimci cewa, shan wadannan magunguna bai taba raba mutum da wannan matsalar, dole horar da kai wajen iya jan ragamar sha’awa shi ne mafi tabbas din hanyar rabuwa da wannan matsala.
Dabara Ta 7: Taimakon Da Uwargida Za Ta Iya Yi
Matar mutum na iya taimaka wa maigidanta don ganin ya rabu da wannan matsalar ta hanyoyi da dama. Da farko dai sai ta yi masa kyakykyawar fahimta, kar ta kullace shi ko ta rika ganin kamar wani rauni ne daga bangaren mazantakarsa. Sannan ta dage da ba shi kulawa da kyautatawa ta musamman lokacin gabatawar ibadar aurensu, ta yi hakuri ta kuma dage don ganin ta taimaka masa har ya koyi yadda zai iya tarbe sha’awarsa ta yadda ba za ta rika kubce masa ba. Uwargida na iya samun lokaci ta tausasa wa maigida dukkanin illahirin jikinsa, tausa mai kyau, don wannan zai kwantar masa da jijiyoyin jikinsa, wanda haka zai kara masa samun dama na iya tarbe sha’awarsa. Haka kuma wajen maganar horar da kai don iya jan ragamar sha’awa da bayaninsa ya zo a makon da ya shige, matar mutum na iya taimaka masa ta hanyar sarrafa wasu wurare ko gabobin da ka iya dakatar masa da sha’awarsa lokacin da ya ji tana gab da kubce masa.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba Insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.