Matsalolin Najeriya: Taya ni mu gyara
A kwanakin baya ne shahararren mai kudin duniyar nan dan kasar Amurka ya ba da shelar cewa yana gaf da shigowa Nahiyar Afirika domin ya agaza mata ta bangaren kiwon lafiya. Nahiyar Afirika zai shigo, kai dagajin kalmar nahiya ka san cewa ba wai kasa daya zai shiga a nahiyar ba. Shahararren mai kudin wanda […]
A kwanakin baya ne shahararren mai kudin duniyar nan dan kasar Amurka ya ba da shelar cewa yana gaf da shigowa Nahiyar Afirika domin ya agaza mata ta bangaren kiwon lafiya.
Nahiyar Afirika zai shigo, kai dagajin kalmar nahiya ka san cewa ba wai kasa daya zai shiga a nahiyar ba. Shahararren mai kudin wanda ya kasance shi ne mai kamfanin Microsoft.
Kalmar nan ta Malam Bahaushe da yake cewa sai gida ya koshi ake bai wa dawa, to kai daga ji ka san shahararren mai kudin ya gama kosar da gidansu, ko in ce nahiyarsu, koma dai bai gama kosar da su ba to yana gaf da yin hakan.
A ’yan kwanakin nan na ji amon muryar shahararren mai kudin nan dan kasar Najeriya kuma wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirika, yana nuna sha’awarsa a kan yana da buri nan gaba kadan zai iya saka hannun jari mai tarin yawa a cikin kungiyar kwallon kafar nan wadda ake kira da Arsenal.
A cewarsa, yana da burin yin hakan walau yanzu ko an jima. Mai kudin da ya fi kowa kudi a Afirika ya kasance dan Najeriya ne kuma dan Arewa, kuma dan Jihar Kano. A Najeriya ba mu da wuta gaba daya, idan ma akwai ta to da ita gara babu, musamman ma a wannan lokaci na zafi, Arewacin Najeriya ya fi kowane bangare na bangarorin kasar nan matsalar wutar lantarki.
Jihar Kano ita ce mahaifar mai kudin Afirika kuma jihar tana bukatar wutar lantarkin da ta kai yawan 600MW amma a halin yanzun jihar ba ta samun wutar da ta wuce 140MW, kuma a ciki ake tura wa wani yanki na kasar Nijar, daga ta Kanon ake tura wa wani yanki na Katsina, daga ta Kanon ake tura wa garin Azare na Jihar Bauchi, idan an ciccire an bai wa wadannan garuruwan to jihar Kano a ta samu da yawa ta samu 80MW ko 70MW ita da take da bukatar 600MW.
Shin ina nazari da tunanin wannan mai kudin Afirikan ya tafi ne? Ka fi kowa kudi a duk Afirika amma mahaifarka da ke da bukatar wutar lantarki 600mw na fama da 80mw kuma 80mw din ita ake sayar wa kamfanoni, sai tsakar dare sannan ake tunawa da unguwannin talakawa a turo musu wutar ta awoyi biyu zuwa uku.
Ga wani mai kudin can daga wata uwa duniya ya shigo nahiyar yana kokarin agaza musu, kuma shi a kyauta ma zai taimaka musu, ina ma a ce shi ma wannan mai kudi na Afirika zai tuna da mahaifarsa, a ce ya zo ya saka jarinsa a bangaren wutar lantarkin a jiharsa ko a yankinsa na Arewa. Ya saka isasshen jari ta yadda wutar za ta samu, a samar da ita don kamfanoni ma, ma’ana a alakanta samun kudin shigarta mafi tsoka ya fito daga kamfanoni, a bar shi ma a ce Malam talaka duk watan duniya ya biya kudin wuta Naira 500 kacal, masu kudi kuma a yi musu nasu farashin daban.
A takaice a ce akwai gidajen talakawa a Jihar Kano dubu dari biyu, to ka buga 500 sau dubu dari biyu duk watan duniya! Banda kaso mafi tsoka da zai fito daga hannun kamfanoni.
Irin wannan kishin kan muka rasa a Nahiyar Afirika, shi ya sa muke zaune kullum cikin wani hali, kowa kansa ya sani, mai kudi daga matarsa sai ’ya’yansa sai kuma dangin matarsa, ba ruwansa da matsalar wuta in har akwai man fetur a gari. Jihar da take bukatar 600mw an ba ta 80mw me kake tsammani ke nan?
Da dadewa na taba karanta wani labari a BBC, cewa wani mai kudi wanda ya fi kowa kudi a Maiduguri ya dau alwashin zai yi wa Jihar Borno wutarta ta kanta, har ma za a wani yanki na Nijar, amma har yau har gobe shiru nake ji. Kusan shekaru biyu ke nan zuwa uku, karshe ma sai na jiyo labarin mai kudin ya je Amurka ya gina wata tafkekiyar kasuwa wadda aka kira da cibiyar kasuwanci. An kashe makudan kudade wajen gina cibiyar, karshe haka zai mutu ya bar musu ita a can. Tirrr!
Daga na gaba wai ake ganin zurfi ruwa, inji Malam danhausa, shin haka tunaninmu zai ta tafiya ke nan tun da muna ganin wadanda suka samu damar ba sa tsinana komai na kishin kai? Haka za mu yi ta zama ke nan mu? Hatta sarakunan nan da ke sanye da rawani, wallahi mahaukatan kudade gare su, amma ba su tunanin bunkasa al’ummarsu da jihohinsu. Su dai kullum su tara, kai wani ma kamar ya kwace naka ya hada da nasa wallahi!
Sarakuna kadai za su iya taimakawa wajen bunkasa noman rani, amma ina! Saboda tunaninsu ba na son ci gaban al’ummarsu ba ne, su dai su tara kuma su yi suna a duniya. Lambobin girma na banza har da na wofi kala-kala za kai ta jin su a wurarensu. Haka suke ta mutuwa suna ta barin tarin mahaukatan kudade a banza da kuma wofi!
Allah Ya kyauta, Ya kuma agaza mana. Allah Ya cusa mana son junanmu da son taimaka wa kanmu da kanmu! Amin.
Jama’are ya aiko daga [email protected] <mailto:[email protected]>; (08163055770)