Matsalolin tattalin arziki:- Sarki da Soludo sun magantu saura gwamnati
A ranaikun Laraba da Alhamis din makon da ya gabata tsofaffin gwamnonin Babban Bankin kasa, Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Farfesa Chukwuma Charles Soludo a wurare daban-daban sun yi kira da gargadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da lallai ya tashi tsaye, ya yi dukkan mai yiwuwa, akan yadda zai tunkari gyara tare […]
A ranaikun Laraba da Alhamis din makon da ya gabata tsofaffin gwamnonin Babban Bankin kasa, Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Farfesa Chukwuma Charles Soludo a wurare daban-daban sun yi kira da gargadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da lallai ya tashi tsaye, ya yi dukkan mai yiwuwa, akan yadda zai tunkari gyara tare da farfado da tsare-tsaren tattalin arzikin kasa nan, muddin yana son ya kauce wa fadawa cikin irin yadda Gwamnatin PDP ta Shugaba Dokta Goodluck Jonathan ta samu kanta.
Mai martaba Sarki Sanusi II, shi ya fara bada wancan gargadi a Kano, a ranar Larabar da ta gabata, ya yin da ya gabatar da wata kasida mai taken “ Najeriya a kokarinta na neman sabuwar dabarar bunkasa,” a wajen taro na 15, na Hukumar Tsare-Tsare da Majalisar kasa akan bunkasa Tsare-Tsare, wanda aka gudanar a Kano, inda ya ce “Idan har wannan gwamnatin ta ci gaba da yin abubuwa irin na gwamnatin da ta gabata, to kuwa ba makawa zamu karke ne irin yadda shugaba Jonathan ya karke”. Anan Sarkin, ya kawo misali da irin yadda tun daga shekarar da ta gabata 2015, kasar nan ta ke samar da masu biliyoyin Naira da basu wani aikin a zo a gani ba, wadanda ta ke ba canjin musayara kudaden waje akan canjinta na N197, akan kowace Dalar Amurka, su kuma suna sayarwa akan N300. Ya ce bisa ga wannan tsari, wanda ya isa zai iya daukar wayarsa ya kira masu tafiyar da harkar canjin su ba shi $10miliyan akan farashin gwamnatin na N197, shi kuma ya sayar akan N300, wanda haka zai ba shi ribar N1biliyan nan take, abinda in ya yi sau hudu zai samu Naira biliyan hudu, a zaman ba cas ba as, yana zaune kawai,” in ji San Kanon.
“Masu yin haka a kullum suna fada mana cewa wannan manufa za ta taimaki talaka. Bai kamata ba mu karya darajar Naira ba, domin yin hakan zai kara jefa talakawa cikin matsanancin talauci.” In ji mai martaban. Ya ci gaba da cewa “Talaka shi ke biyan karya darajar Naira, ya yin da mai kudi yake kara cin riba, ga shi tsarin ya ci gaba har tsawon shekara guda, mun yi magana, mun yi magana, mun yi magana.” “Muddin wannan gwamnati ta ci gaba da yin abin da gwamnatin da ta gada ta yi, to, kuwa labudda za mu karke inda tsohon shugaban kasa Jonathan ya karke. Ba za ku so jin haka ba, amma hakan shi ne hakikanin gaskiyar lamari.” in ji Sarki Sanusi II.
A dai wancan munbari, Sarki Sanusi II, ya jaddada mamakinsa, tare da yin tambayoyi kamar haka:- Wadanne irin tsare-tsaren tattalin arziki mu ke tafiyarwa? Wa yake bai wa gwamnati shawara a kan tattalin arzikin, ta yadda zan yi magana da shi. A zaman martani tuni gwamnatin tarayya ta hannun daya daga cikin Kakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu, gwamnatin ta ce ko kusa ba ta da niyyar shiga ce ce-ku ce da Mai martaba Sarkin na Kano. Don haka sai ta nemi sauran Sarakunan gargajiyar kasar nan da suke da kowace irin shawara da suke son bai wa gwamnatin tarayya da su rinka tuntubar ofishin shugaban kasa ko ma shugaban kasar kai tsaye.
Tamfar tsofaffin gwamnonin Babban Bankin biyu sun hada baki, sai ga shi kashegari wato Alhamis din da ta gabata, yayin da yake gabatar da tasa kasidar a wajen wani taro karo na hudu na kungiyar gwamnoni `yan gabadai-gabadai wato Gwamnonin jam`iyyar APC, a Kaduna, tsohon Gwamnan Babban Bankin kasar nan, wanda shi Mai martaba Sarki Sanusi ya gada a shekarar 2010, Farfesa Chukwuma Charles Soludo, shi ma yana gargadi da jan hankalin Gwamnatin Shugaba Muhammdu Buhari da ta daina zargin gwamnatin tsohon shugaban kasa Jonathan a kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan. Maimakon haka, in ji Farfesa Soludo kamata ya yi gwamnatin ta fara tunanin kawo tata mafitar. Ya kara da cewa “Zargin tsawon shekara guda ya isa, don haka ya kamata gwamnatin Buharin ta fara zargin kanta da kanta.”
Ba a nan Farfesa Soludo ya tsaya ba, domin kuwa ya bayyana tsare-tsaren tattalin arzikin wannan gwamnatin tamfar koma baya, yana mai nuni da sumar da kasuwar hada-hadar hannayen jari take ciki, da a kullum ta ke kara tabarbarewa ana ta asarar tiriliyoyin kudaden hannayen jarin da sauran kaddarori. Ya kuma koka a kan irin tsarin da Gwamnatin Buharin take yaki da cin hanci da rashawa da ya ce kamata ya yi ta faro shi daga yin hukunci abin misali maimakon taba nan taba can. Farfesa Soludo, ya kuma shawarci Gwamnoni APC, da su mike su yaki fatarar da ta yi katutu a jihohinsu ta hanyoyi mabambanta, bisa ga karfin arzikin da kowace jiha take da shi, yana mai nuni da jihohin Arewa 11, masu yawan al`umma miliyan 55, da su suka fi sauran jihohin kasar nan yawan al`umma, kuma suke da filin kasa mai fadin kashi 40 cikin 100, amma kuma su ke kan gaba akan annobar zaizayar kasa da kuma kantar talauci. Jihohin kamar yadda ya ambata su ne:- Katsina da Adamawa da Kano da Bauchi da Yobe da Kebbi da Gwambe da Sakkwato da Jigawa da Borno da Zamfara.
Da yake mayar da martini a kan wannan zargi na tsohon Gwamnan Babban Bankin, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda yake zaune a wajen taro a lokaci, cewa ya yi da hujja gwamnatin tarayya take sukar irin yadda gwamnatin da ta gabata ta ragargaza tattalin arzikin kasar nan, satar da ya ce ba a taba samu ba a duk wata kasar duniya. Yana mai nuni da cewa a bangaren ajiyar kudaden kasar nan na waje, da wani lokaci ta kai Dalar Amurka biliyan 30, amma sai ga shi kafin kyaftawar ido da bisimillah an sace Dalar Amurka biliyan 15.
daya-da-daya wadancan tsofaffin gwamnonin Babban Banki biyu, ba yadda za a yi ka iya fitar da su daga zargin sun taka gagarumar rawa a kan matsayin da tattalin arzikin kasar nan yake ciki a yau, walau na nasara ko na tabarbarewa, bisa ga irin mukaman da suka rike da kuma kasancewarsu masana tattalin arzikin kasa. Amma kuma dole ka jinjina musu a kan irin yadda suke yin ta maza suna furta albarkacin bakunansu a duk lokocin da suka ga ana yin ba daidai ba, ba tare da shayin suna cikin gwamnatin ba, ba tare da la`akarin gwamnatin ka iya bincikar barnar da suka aikata a kan wadancan mukami.
Alal misali, an sha jin Farfesa Soludo bayan ya bar mulki suna sa-in-sa da tsohuwar Ministar kudi da suka yi aiki tare a gwmnatocin tsoffin shugabannin kasa irin su Cif Olusegun Obasonjo da Dokta Jonathan, wato Dokta Ngozi Okonji Iweala. Shi kuwa mai martaba Sarki Sanusi II, busa usur din ma da ya yi wa Gwamnatin Jonathan a kan zargin bacewar wasu makudan biliyoyin kudaden man fetur ta sanya a cikin watan Fabrairun shekarar 2014, yana saura ’yan watanni kasa da shidda ya kammala wa`adinsa na farko, gwamnatin Jonathan ta ka sa hakuri da shi ta sauke shi da rana tsaka. Da wannan ke nan babu wani abin labari don yanzu sun fito a kan titi sun bayyana wa duniya irin halin da kasa take. Saura da me? Ya rage ga gwamnatin tarayya ta san na yi a kan irn tsananin mawuyacin halin talauci da tsadar rayuwa da talakawa suke ciki.