Matsalolin tsaron da ke addabar kasashen Afirka suna da yawa – Janar Dambazau

Hafsan Hafsoshin Najeriya Janar Abdurrahman Bello Dambazau ya ce rashin tsaron bakin iyakoki ne babban abin da ke haddasa fitina domin ta nan ake satar shiga da makamai da wasunsu zuwa kasashen Afirka.Janar Abdurrahman Dambazau ya bayyyana haka ne a tattaunawarsa da gidan Rediyon Muryar Amurka, inda ya ce matsalolin tsaron da suke addabar kasashen […]

Matsalolin tsaron da ke addabar kasashen Afirka suna da yawa – Janar Dambazau

Hafsan Hafsoshin Najeriya Janar Abdurrahman Bello Dambazau ya ce rashin tsaron bakin iyakoki ne babban abin da ke haddasa fitina domin ta nan ake satar shiga da makamai da wasunsu zuwa kasashen Afirka.
Janar Abdurrahman Dambazau ya bayyyana haka ne a tattaunawarsa da gidan Rediyon Muryar Amurka, inda ya ce matsalolin tsaron da suke addabar kasashen Afirka, sun zarce batun ta’addanci kawai, sun hada da dillalan miyagun kwayoyi da ke amfani da nahiyar a zaman zango wajen safarar kwayoyinsu da kuma safarar makamai, sai kuma uwa uba batun rashin shugabanci.
Janar Dambazau ya ce “Rashin shugabanci na kwarai a kasashenmu na Afirka na haddasa cin hanci da rashawa da kawo koma bayan tattalin arziki da lalata harkar ilimi da dakile kyautata jin dadin al’umma, abubuwan da sukan taru su kara wutar tashin hankali.”
Game da batun rashin tsaro, musamman a yankin Arewac, Janar Dambazau ya ce tilas sai an samu hadin kan kasashe makwabtan Najeriya kafin a magance shi, ya ce domin kuwa ta cikin wadancan kasashe makwabta ake shigo da makaman da ’yan ta’adda da ’yan fashi ke amfani da su.
Janar din ya kawo misali da cewa tsawon bakin iyakar Najeriya da kasashen Kamaru da Chadi da Nijar ya kai dubban kilomitoci, amma kuma tasoshin bakin iyaka guda 57 rak Najeriya take da su. Alhali kuma akwai barayin hanyoyi fiye da dubu daya da 500 da ake amfani da su wajen shiga da fita daga kasar.