Matsalolinmu sun bambanta da na sauran mayankar Abuja – Tafida Mafindi
Me ya baka sha’awar kafa wannan mayanka? Ni makiyayi ne, ina da gidan gona a Taraba da Nassarawa da Abuja. Bayan an wahala kiwo idan an zo sayarwa sai kaga farashi bai biyan kudin sabulu, a saya a bashi biyan kudi ya zama aiki. A na cikin haka sai Allah Ya hadani da marigayi Umaru […]
Me ya baka sha’awar kafa wannan mayanka?
Ni makiyayi ne, ina da gidan gona a Taraba da Nassarawa da Abuja. Bayan an wahala kiwo idan an zo sayarwa sai kaga farashi bai biyan kudin sabulu, a saya a bashi biyan kudi ya zama aiki. A na cikin haka sai Allah Ya hadani da marigayi Umaru Musa Yar’adua. Shi ma mutum ne mai sha’awar kiwo. Mun tattauna da shi sosai a kan irin albarkar noma da Allah Ya yi wa Arewa amma ma fi yawan manoma basa cin gajiyar nomansu bayan sun yi girbi alhali dukkan abin da ke ragewa a gona abincin dabbobi ne. Bayan nan ne sai ya kafa wata gidauniyar tallafawa manoma mai suna CAT wato Commercial Agriculture sannan ya ware naira biliyan 300 a ka ajiye a Babban Bankin Najeriya. An kira taron kwamishinonin gona na jihohin kasar nan a kan lamarin da kuma yadda manoma za su amfana. Ba a kai ga cin gajiyar tsarin ba Allah Ya mishi rasuwa, nan maganar ta waste.
Ya kuke gudanar da aiki a wannan mayanka?
Na farko mu na da wajen ajiye shanu wanda a ka yi shi a kan tudu tare da tsarin magudanur ruwa yadda shanu zai iya zama mako biyu ba tare da ya tagayyara ba. Daga wajen ne za a shigo da shi bangaren yanka, na’ura ce za ta kwantar da shanu, sannan wani limami ya yanka, sai wata na’urar ta garzaya da shi wajen fida. Na’ura ce za ta sabule fatar ta kuma nadeta, sai a tsaga jikinsa a kwashe kayan ciki a raba su nau’i nau’i, a wanke da ruwa mai sanyi da na zafi. Sai a gwada nauyin naman a sikele kafin a yi masa gwaji don tantance ingancinsa, idan an samu mara inganci a cika sai a rubuta, sai a kai naman wani waje da ke cikin mahautar a latata, a ka’ida, gwamnati ce za ta biya diyyar adadin nama mai illa, sai dai ba a taba biyanmu ba. Shi ko wanda a ka tabbatar mai inganci ne sai a tura wajen wankewa inda a ke amfani da ruwa mai sanyi da na zafi kafin a tura shi zuwa ma’adanar nama saboda naman shanu na bukatar kamar awa 10 kafin a ci. Za a rataye naman wuya na kallon kasa, a wannan lokaci ne duk wata karamar illa da ke jikin shanu zai bi ragowar jini ya tsiyaye. Sannan daga nan sai a kai shi wajen rarrabe nama, a wajen ne za a datse nama na tsire ko na balangu a kuma tsaga shi gwargwadon yadda a ke bukata, na kilishi a yi masa tsagunsa, haka nan inji ya kacancana na dambu. Shi ko kashi bayan an kwashe bargo, ragowar sai a busar a nike don amfanin masu yin abincin kaji ko na kifi, haka nan akwai na’urar busar da jinin shanun a mai da shi gari wanda shi ma masu abincin kaji da na kifi na bukata. Fatar kuma a jemeta da ruwan zafi inji ya aske gashin. A na amfani da fatar ta fuskoki daban-daban, na ganda daban ne sai an bishi da wutar babbaka na inji. Haka na dukanci, kuma akwai na yin zaren dinkin fida na likitoci wanda su ke amfani da shi a wajen tiyata a jikin dan Adam wanda idan mutum ya warke ba sai an zare ba. Bahayar kuma muna turashi bangaren gonarmu ne a matsayin taki bayan an yi masa wasu aikace-aikace, haka nan muna binne bahayan shanu sannan bayan wasu ’yan kwanaki ya koma wani irin tsutsa sai a busar da shi da na’ura wanda wasu ke sayen kilonsa a kan naira dubu 3, mu na kuma zubawa kwadi ko kifi da mu ke kiwo a matsayin abinci su na ci, ba mu da abin zubarwa ajikin shanu, hatta kahonsa komi kudi ne. akwai kuma ma’adanar nama da za a iya ajiye nama na tsawon lokaci ana fitowa da shi gwargwadon bukatar jama’a ba tare da ya samu lahani ba.
Wane gudunmowa ka samu daga gwamnati wajen kafa mayankar?
To bayan rasuwar shugaban kasa Umaru ’Yar’aduwa sai mu ka rasa wanda za mu iya tinkara da wannan batu har tsohon Shugaban kasa Jonathan ta nada Dokta E.A Adeshina Ministan gona. Shi ne ya ziyarci gonata bayan na tuntube shi, ya duba wannan mahautar, sannan ya tsara yadda ma’aikatarsa za ta tallafa mini. A sakamakon kokarin ministan, ma’aikatar aikin gona ta taimaka min da aikin titi da ya taso daga babban hanyan wannan gari na Jikwoyi zuwa nan gefe wanda ya ci kamar naira miliyan 30. Sannan ya sa a ka yi rijiyar burtsatse mai samar da lita miliyn 30 na ruwa a wuni guda da injin sarrafashi. Bayan nan kuma na jawo wuta daga babban titin gari zuwa wajen nan mai karfin 33 Kb wanda ya ci wajen naira miliyan 28, hakan ya taimaka wa wannan jejin ya bunkasa a cikin hanzari. Na fara aikin mahautar ne tun a shekarar 2010 sannan a ka bude a 2013 inda tsohon Shugaban kasa Jonathan ya ziyarci wajen har sau biyu.
Wadanne irin kalubale ne ka fuskanta?
Kamar yadda na maka bayani na fara aikin kafa wannan waje tun a 2010 amma sai a 2013 ya fara aiki a saboda matsalolin kudi da kuma na shigo da kayan aiki. Jami’an kwastam sun sha rike mana kaya, su ce ba na mahauta ba ne kasancewar ba wanda ya taba shigo da irin su. An taba rike min kaya na wata 6, ban samun kayan ba sai da Allah Ya san a hadu da da tsohon Shugaban kasa Jonathan a wajen wani taro. ya tambaye ni ya labarin mayanka? Na ce da shi kwastam sun rike mini kaya, sai ya hada ni da ministan kudi Okonja Iwella wadda kwastam ke karkashinta, ya ce da ita ta je warware matsalar, nan ta kira shugaban kwastam sannan ta bashi umarnin su sake mini kwantenonina guda 9 ba kuma batun biyan kudin ajiya. Sai dai ko da na bude an cire wasu na’urori sai da na kashe wajen naira miliyan 2 na sayi wasu na’urorin.
Su waye abokan huldarku?
Mu na hulda da manyan gidajen Otel-Otel a nan Abuja da Legas da Fatkwal, da kuma Kamfanoni irinsu Bega ko na mai. kamar awaki kuma mun fi kai su Kudu maso Gabas kamar Enugu da Onitsa, kuma mu na amfani ne da manyan motoci masu kayan sanyi wajen safaran naman.
Sai dai da alama kamar wajen baya aiki, me ke faruwa
Matsalar tawayar tattalin arzikin kasa da a ke fama da ita ce matsalarmu. A lokacin da wajen nan ya fara aiki a rana guda ana yanka shanu daga 50 zuwa dari. Manyan Otel irin Nicon su kan yi odar nama kamar kilo dubu 10 zuwa 20 a wata sannan idan ana bukukuwa su bukaci hakan a cikin mako daya ko mako biyu. A wancan lokaci su na samun baki sosai daki a wajensu bai samuwa sai an yi tanadi saboda baki na shigowa kasar kuma ana tarurruka a Abuja, amma a yanzu da bakinsu bai wuce kashi 25 cikin dari na adadin dakunansu, ba sa wuce sayan kilo dubu daya a wata, saboda su kansu ’yan bakin da su ke samu sun gwammace su fita waje su ci nama ko abinci saboda neman sauki. Su ko kamfanin Bega a lokacin su na odar kamar kilo dubu 5 a wata su a jiye. Amma duk wannan ya ja baya a yanzu. A lokacin ma’aikatanmu sun haura 100 amma yanzu ba su kai 20 ba.
Wace irin nasara za ka ce kafa wannan waje ya kiwo?
A gaskiya na samu babbar nasara, kafa wannan waje kadai ba karamar nasara ba ce saboda a lokacin da a ka yi aikin dala ta na kan naira 120 ne amma a yanzu gashi ta koma kusan 400, sannan girman wajen nan wanda ya kunshi gidan gona da mayanka ya kai hekta 150, wannan kadai ma nasara ce.
A karshe wace kira gareka ga hukuma?
Ta samar mana da filin kasuwanci a cikin gari kamar yadda aka yi wa masu kifi wanda zai hada da kai ruwa da wuta don kafa na’urorinmu na sanyi ko da a gefen gari ne kamar Zuba, na tabbata jama’a za su rika zuwa su na sayan nama kwargwadon kamar yadda dama aka tsara za a yi mana tun a farko. Irin wannan aiki ya kamata a yi wa manoman masara da na gyada da na wake da na auduga ba komi a rika daukansa haka nan a na sayarwa kasashen waje ba, ba tare da an sarrafa ba. Saboda manomi zai samu ribar da ya ke bukata, ya samar da aikin yi sannan ya bai wa gwamnati haraji.