Matsayi da muhimmancin addu’a ga Musulmi
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, sallallaahu alaihi wasallam, wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, tare da alayensa da sahabbansa, […]
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi, sallallaahu alaihi wasallam, wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa ranar karshe.
Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah, kuma mafi alkhairin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu, sallallahu alaihi wasallam. Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira kuwa bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, yau mukalarmu za ta gudana ne, kamar yadda muka fada a makon da ya gabata, kan muhimmanci da matsayin addu’a (rokon Allah). Yadda kanun mukalar ya nuna, a matsayin addu’a na babban makami, yana iya isa a ce lallai tana da muhimmanci, kuma kamar yadda mukalar da ta gabata ta nuna na cewa Allah na fushi da wanda ba ya rokonSa, yana iya isa a ce lallai tana da matsayi. In Allah Ya so, bayanin da zai zo, zai kara fito mana da wannan manufa sosai don mu fahimce ta. Allah Ya sa abin da za a karanta ya zama mai amfani gare mu duniyarmu da lahirarmu, amin.
Za mu takaita madubinmu ne a kan abin da shaihin malamai, Al’imam Abu Zakariyya Yahya bn Sharf Annawawiy ya gabatar a littattafansa biyu, in Allah Ya so, wato Riyaadhus Saalihiin da kuma Al’azkaar da fatar Allah Ya ba mu ladar abin da yake daidai, Ya yafe, Ya gafarta abin da yake kuskure a ciki, amin.
Saboda muhimmancin addu’a, idan an tuna, an karanci hadisin da Imam Ahmad ya ruwaito wanda aka samo daga Abiy Hurairata, Allah Ya yarda da shi, inda ya ce, Manzon Allah, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce, “Duk wanda bai roki Allah, Mai girma da daukaka ba, to (Allah) Yana fushi da shi (ko Allah Ya yi fushi da shi).” Da kuma matsayinta, saboda abin da Annabi, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce, “Mafi falalar ibada, ita ce addu’a.” Hadisin da aka ruwaito cikin Sahihu Abiy Dawuda, hadisi na 1,284.
Haka nan da abin da Annabi, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce, “Addu’a tana amfanar abin da aka saukar da ma abin da ba a saukar ba, saboda haka gare ku ya bayin Allah game da mayar da hankali wajen yin addu’a.” A hadisin da aka fitar a cikin littafi Sahihul Jami’u, hadisi na 2,635.
Abin Da Alkur’ani Ya Ce Game Da Addu’a
Farko dai Malam ya ce, “Babi Kan Falalar Addu’a”, sai ya kawo abin da Allah Ya ce a cikin Sura ta 40 (Ghaafir), aya ta 60: “Kuma Ubangijinku Ya ce, ‘Ku kira (roke) Ni in karba muku…” kamar dai yadda yake a cikin mukalar da ta gabata.
A cikin tafsirin Ibnu Katheer an ce, “Allah Ya ba mu karsashin mu roke Shi, kuma Ya ba mu tabbacin Zai karba mana addu’armu.” Ke nan wannan yana nuna mana matsayin addu’a da kuma muhimmancinta, saboda Wanda za a roka din ne ya ce a roke Shi, kuma Ya bayar da tabbacin Zai karba.
2. Allah Ta’aala Ya ce, “Ku kirayi Ubangijinku da kankan da kai da kuma a boye, lallai ne Shi, ba Ya son masu wuce iyaka.” Surar A’raaf, aya ta 55.
3. Kuma Allah Ta’aala Ya ce, “Ko wane ne yake karba wa mai bukata idan ya kira Shi, kuma Yake tunkude mummunan abu…?” Surar Naml, aya ta 62.
4. Haka nan Allah Ta’aala Ya ce, “Kuma idan bayiNa suka tambayeka game da Ni, to Ni kusa Nake (da su), Ina amsa kiran mai kira da zarar ya kiraye Ni…” Surar Bakarah, aya ta 186.
Game da wannan aya ta Surar Bakarah, aya ta 186, Shaikh Ja’afar Mahmud Adam, a cikin littafinsa Tarjama da Sharhin Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma, shafi na 119, ya ce, “Dangane da lafazin ‘kusancin Allah’ da ya zo a wannan aya, kusancin Allah Ta’ala ba kusanci ne na gangar jiki ba, kusanci ne na ilimi, cewa Yana sane da mutane da iliminSa; kusanci ne na ji, cewa Yana jin duk abin da suke yi; kusanci ne na gani, cewa Yana ganinsu; kusanci ne na taimako da bayar da gudunmawa a kebance ga bayinSa muminai. Wannan shi ne nau’i na kusanci da malamai suka fassara ‘kusanci’ da shi, kamar yadda ayoyin Alkur’ani da hadisai suka nuna.
“Hadisi ya tabbata daga Abu Musa Al’Ash’ariy, Allah Ya yarda da shi, ya ce sahabbai sun kasance idan ana cikin tafiya, lokacin da duk suka hau kan wani tudu, sai su yi kabbara, lokacin da duk suka yi gangara, sai su yi tasbihi, to sai suke daga murya, sai Manzon Allah, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce da su, kiran Allah ba a daga murya, don wanda yake nesa shi ne yake bukatar ka daga masa murya don ka kiraye shi.” [Bukhari, hadisi na 4,205 da Muslim, hadisi na 2,704]. Amma Ubangiji Ta’ala da Yake kusa da kai, Yana jin ka, to daga murya din sai ya zamo rashin ladabi ne….”
Duk wannan yana nuna matsayi da muhimmancin addu’a ga musulmi, saboda haka sai ya mayar da hankali wajen neman samun dacewa.
Abin Da Hadisi Ya Ce Game Da Addu’a
An samo daga Nu’uman dan Bashir, Allah Ya yarda da su, ya ce, Manzon Allah, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce, “Addu’a ita ce ibadah.” Imam Ahmad da Haakim suka ruwaito shi, kuma Shaikh Nasiruddinil Albaniy ya inganta shi a cikin littafin Sahihul Jami’u, hadisi na 3,407. Haka nan wasu daga cikin As’habus Sunan, wato Attirmdhi da An-Nasa’i da Ibnu Maajah; sai kuma Ibnu Abiy Haatim da Ibnu Jarir, sun fitar da hadisin, wanda Imam Attirmidhi ya ba shi darajar “Hasan Sahih,” Imam Annawawiy ya fitar da shi ne a shafi na 387, hadisi na 1,161 a cikin littafin Al’azkaar a karkashin kanun ‘Kitabu Jami’u Adda’waat’. Sannan Abu Dawud da Attirmidhi da An-Nasa’i da Ibnu Jarir sun fitar da shi a wani isnadi na daban.
2. Annabi, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce, “Mafi falalar ibada, ita ce addu’a.” Sahihu Abiy Dawuda, hadisi na 1,284.
3. Haka nan Annabi, Sallallaahu Alaihi Wasallam, ya ce, “Addu’a tana amfanar abin da aka saukar da ma abin da ba a saukar ba, saboda haka gare ku ya bayin Allah game da mayar da hankali wajen yin addu’a.” An fitar da wannan hadisi a cikin littafin Sahihul Jami’u, hadisi na 2,635.
Nan za mu takaita, sai mako mai zuwa za mu gabatar da wani abu na ladubban addu’a, amma kafin nan ga wata addu’a da Manzon Allah, Sallallaahu Alaihi Wasallam yake yawaita yi: An samo daga Anas, Allah Ya yarda da shi, ya ce, “Mafi yawan addu’ar da Annabi, Sallallaahu Alaihi Wasallam ya fi yi ita ce, ‘Allaahumma rabbana atina fiddunya hasanatan wa fil akhirati hasanatan wa kina azabannaar’ wato Ya Allah Ubangijinmu, Ka ba mu, a duniya, abu mai kyau da kuma a lahira, abu mai kyau, kuma a tseratar da mu daga azabar wuta.” Bukhari, hadisi na 6,389 da Muslim, hadisi na 2,690 suka fitar da hadisin.
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!