Matsayin azumtar watan Ramadan a Musulunci (3)
Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa […]
Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta wa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne (SAW).
Allah Ya dada tsira da aminci ga ManzonSa da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, yau ma dai mukalar tamu za a ci gaba ne daga inda muka kwana dangane da falala da hikimomin azumi:
16. Shi azumi mai ceton mai yin sa ne. Haka nan Alkur’ani! Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Azumi da Alkur’ani masu ceto ne ga bawa a Ranar Alkiyama. Azumi zai ce, ‘Ya Ubangiji, na hana shi cin abinci da sha’awa, saboda haka Ka sanya ni ceto gare shi.’ Shi ma Alkur’ani zai ce, ‘Ya Ubangiji, na hana shi barci da dare, saboda haka Ka sanya ni ceto gare shi.’ Saboda haka sai su yi ceton.” Imam Ahmad, Hadisi na 6,626 da Hakim, mujalladi na 1, Hadisi na 554; da Abu Nu’aim, mujalladi na 8, Hadisi na 161, sun ruwaito shi ta hanyoyi masu yawa daga Huyayyi bn Abdullahi daga Abdurrahman Alhabuliy daga Abdullah bn Amr, kuma isnadinsa hasan (mai kyau) ne. Alhaisamiy ya fada a cikin littafin Majma’u Al-Zawa’id, mujalladi na 3, shafi na 181, bayan ya kara nasabarsa ga Addabaraniy, cikin littafin Alkabir, “Mazajen da aka ruwaito Hadisin daga gare su mazaje ne ingantattu.”
17. Azumi kaffara ne: Yana daga cikin abin da aka kebance azumi da shi na falala, cewa Allah Ya sanya shi kaffara dangane da wasu ayyukan da aka yi kan lalura ko kuskure ko ba-daidai din su ba a cikin ibada. Misali idan mutum ya yi aski cikin ihrami (haramin aikin hajji da umra), saboda lalurar rashin lafiya ko farauta kuma ba hadayar da za a biya; ko gyara a kan rantsuwa; ko zihari da makamantan wadannan, kamar dai yadda bayanansu ya zo a Surar Bakara, aya ta 196 da Surar Nisa’i, aya ta 92 da Surar Ma’ida, aya ta 89 da ta 95 da Surar Mujaadala, aya ta 3 da ta 4.
Haka nan ana gwama azumi da sadaka a cikin abin da yake kasancewa maganin fitinar da take samun mutum cikin dukiyarsa da iyalinsa da makwabcinsa, kamar dai yadda ya zo a cikin Hadisin da aka samo daga Huzaifatu bn Alyaman, (Allah Ya yarda da shi), ya ce, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Sallah da azumi da sadaka kaffara ne ga fitinar mutum a cikin iyalinsa da dukiyarsa da makwabcinsa.” Buhari, mujalladi na 2, Hadisi na 7 da Muslim, Hadisi na 144.
A makon jiya an yi nuni cewa wadannan falala da hikima da daraja mai girma, yawancinsu na yin kowane azumi ne, to, balle azumtar Ramadan, wanda yake farilla kuma daya daga cikin shika-shikan Musulunci. Shi azumin Ramadan ya yi fice ko ya kebanta da wadansu darajoji na daban, wadanda daga cikinsu akwai bayanin cewa shi wata ne na Alkur’ani, kamar yadda ya zo a Surar Bakara, aya ta 185.
Abubuwan kwadaituwa kan azumin Ramadan:
1. GAFARTA ZUNUBAI KOMAI YAWANSU:
Mai shar’antawa, Mai hikima, Allah, (Subhanahu Wa Ta’ala), Ya kwadaitar game da azumin Ramadan, lamarin da ya bayyana falalarsa da daukakar matsayinsa na gafarta zunubai ko da sun kai yawan kumfar teku, duk a dalilin wannan ibada mai tsarki, mai albarka.
An samo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Duk wanda ya azumci watan Ramadan, alhali yana mai imani (ya yarda da farillancinsa) da kwadayin lada, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa.” Buhari, mujalladi na 4, Hadisi na 99 da Muslim, Hadisi na 759.
Haka nan daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya hau mumbari, sai ya ce, “Amin, amin, amin.” Sai aka ce masa, “Ya Manzon Allah, ka hau mumbari, sai ka ce, ‘Amin, amin, amin (yaya al’amarin yake ne)?” Sai ya ce, “Lallai Jibril (Alaihis Salam), ya zo mini, sai ya ce, ‘Duk wanda watan Ramadan ya riske shi kuma bai yi abin da aka gafarta masa ba, ya shiga wuta, kuma Allah Ya nesantar da shi (can nesa), ka ce, amin.’ Sai na ce, “Amin”..…har zuwa karshen Hadisi.” Ibnu Khuzaimah, mujalladi na 3, Hadisi na 192 da Ahmad, mujalladi na 2, Hadisi na 247 da 254 da Albaihakiy, mujalladi na 4, Hadisi na 204, sun ruwaito shi ta hanyoyi da yawa. Hadisi ne ingantacce, wanda asalinsa yana cikin Sahihi Muslim, mujalladi na 4, Hadisi na 1,978.
2. KARbA ADDU’A DA KUMA ’YANTUWA DAGA WUTA:
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Lallai Allah Yana da a cikin kowace rana da dare, wadanda Yake ’yantawa daga wuta, a cikin watan Ramadan; kuma lallai ga kowane Musulmi yana da wata addu’a da yake yi, sai kuma a karba masa ita.” Albazzar, Hadisi na 3,142 da Ahmad, mujalladi na 4, Hadisi na 253 sun ruwaito shi ta hanyar Al’a’mash daga Abu Salih daga Jabir. Sai Ibnu Maajah, Hadisi na 1,643 ya ruwaito shi daga Jabir, kuma sahihi ne.
3. SHIGA JERIN SIDDIkAI DA MASU SHAHADA: An samo daga Amru bn Murrah Aljuhanniy, (Allah Ya yarda da shi), ya ce, ‘Wani mutum ya zo wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ya ce, “Ya Manzon Allah, yaya kake gani, idan na shaida babu abin bautawa da cancanta sai Allah kuma kai Manzon Allah ne, kuma na sallaci salloli biyar, kuma na bayar da zakka, kuma na azumci Ramadan kuma na yi tsayuwarsa, cikin su wa nake (mene ne matsayina)?” Sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “(kana) Cikin siddikai da masu shahada.” Ibnu Hibban ya ruwaito shi (a lamba ta 19 cikin Zawa’idah) kuma isnadinsa ingantacce ne.
Mu kwana a nan, sai mako na gaba mu ci gaba, in Allah Ya kaddara kaiwarmu. A sha ruwa lafiya, Allah Ya karba mana.
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!