Matsayin Boko A kasar Hausa (1)

A wannan tattaunawa, za mu sake komawa baya ne game da matsayin ilmin boko da yadda ake kallonsa a halin yanzu a tsakanin mabambanta mutane, musamman ganin irin yadda ake ta ce-ce-ku-ce dangane da matsayin ‘yan boko haram game da ilimin boko da kuma halin da wannan akida ta sa al’ummar wannan yanki a ciki, […]

Matsayin Boko A kasar Hausa (1)

A wannan tattaunawa, za mu sake komawa baya ne game da matsayin ilmin boko da yadda ake kallonsa a halin yanzu a tsakanin mabambanta mutane, musamman ganin irin yadda ake ta ce-ce-ku-ce dangane da matsayin ‘yan boko haram game da ilimin boko da kuma halin da wannan akida ta sa al’ummar wannan yanki a ciki, a ‘yan shekarun nan. Tambayoyin da ake  ta yi sun kunshi abubuwa da dama. Me ya sa wadanda suka yi rayuwa cikin duniyar ilimin addini ke wa boko da masu tu’amalli da shi wani kallo na daban? Me ya sa su kuma wadanda suka yi bokon tsantsa, suke ganin cewa rayuwar da ba boko cikinta akwai matsala? Me ya sa wasu ke ganin ‘yan boko tamkar wadanda ilimin addini bai dame su ba? Me ya sa ake ta sa-in-sa tsakanin wadannan tarayyar mutane, wato ‘yan boko da ustazai (kamar yadda wasu ke kiran su) dangane da rayuwa da ilimin boko da kuma ta addini?

A tawa fahimtar, fagen da ake magana shi ne na ilmin boko da tasirinsa a tsakanin al’umma, wanda kuma an dade ana ta faman tattaunawa kan sa tun da dadewa, ba wai a kasar Hausa kurum ba, duk wasu sassan duniya da Musulunci ya yi kaka-gida da farko, sa’annan daga baya ilmin boko ya kutso. A lura a nan, sai wadanda ke da ilmin abu ne za su gane illarsa. Ke nan, ba ilmin boko ne ke da illa ba, a tawa fahimta, sai dai irin yadda aka same shi da kuma gudanar da shi. Wannan shi zai kai mu ga tambaya ta gaba, me ya sa ilimin boko zai zama haram? Shin ruhin ilmin ne ke da matsala, ko makunshiyarsa ko kuwa wadanda suka zo da shi ne ke da matsalar ko kuma yadda ya yi tasiri a tsakanin wadanda aka zo wa da wannan tsarin ilimin? Shin a wannan zamani da muke ciki, anya akwai wanda zai da’awar ilmin boko bai da amfani ko ya ce kada a yi mu’amala da abubuwan da ilmin bokon ya zo da shi? Shin wannan zamanin da muke ciki ba a jin cewa ilimin bokon ne da ya yi katutu a rayuwar al’umma, ya sa ake ta wannan jele, dubi da tasirin da ilimin kimiyya da ci gaban zamani suka zo da shi? Zamanancin ne haramun ko ko me? Da alama ba haka batun yake ba, kila shi ya sa ake ta lalube cikin duhu game da wannan matsala ta ilimin boko da matsayinsa a cikin al’umma irin tamu, kuma bisa dukkan alamu, yawo kawai ake yi cikin da’ira, an kasa samun mafita! Me ya sa na ce haka? Akwai dalilai da dama, amma ba za su tallabu ba sai mun koma cikin tarihi tukuna. A kula, shi tarihi a kullum ba labarin jiya ba ne kurum, ko kuma abin da ya faru a jiyan, batu ne na leko jiya domin gane yadda yau take da kuma sanin makamar damukar gobe, in ta zo. Saboda haka, me ya sa yanzu ake nuna kyama a kan boko da makamantan karikitansa? Kafin mu bayar da amsa, mu fara tambayar kan mu tukunna, shin yau ne aka fara nuna kyama ga boko a wannan yanki namu? Ba za mu taba amsa irin wadannan tambayoyi ba sai mun koma cikin taskar tarihi, ta haka za mu kyallaro irin halin da muka samu kan mu a yau.

Ga yadda batun ya samo asali. Ko da Turawa suka kunnu kai a yankin da a yanzu ake kira Nijeriya, yanki hudu ne ke tashe, akwai yankin Arewa, ko kuma Daular Usmaniyya da Yankin Yarbawa da Yankin Imyamurai da Niger Delta da kuma yankin Legas. Wadannan yankuna su ne Turawa suka hade da karfi da yaji a shekarar 1914 suka kasance Nijeriya. Al’adu da addinai da kabilu da harsuna na wadannan yankuna duk sun sha bamban. A Arewa, a wancan lokaci ba wani tanadi da ‘yan mulkin mallaka suka yi dangane da tsarin da za a bi na kyautata ilmin boko, domin ba shi ne a gaban su ba ko kuma yadda za a yi da na Musulunci da aka iske. Amma ga duk mai hankali ya san lallai Turawa ba za su bar ilmin addinin Musulunci ya ingantu ba, haka kuma ba za su fito fili su kashe tsarin ba ko kuma su rushe makarantun Allo sama da dubu 25 da ake da su ba, ko kuma su kori dalibai masu karatu cikinsu, sama da dubu 300 da ake da su, a daidai wannan lokaci ba. Yin haka daga Turawa zai kasance tsokana ce, wadda kuma ba a san irin fitinar da za ta jawo ba. Me ya sa haka?

Abu na farko shi ne, tuni dai Turawa sun murkushe Kuduncin Nijeriya da yankin Legas, sun kuma assasa tsarinsu na karatu da ilimin boko sama da shekara 100 kafin su gangaro Arewaci. Abu na biyu kuwa ko da Turawan suka kunno kai a cikin Daular Usmaniyya a farkon karni na 20, sun sami Daular Usmaniyya ta zaunu, shekara 100, ita ma dauke da kebabben tsarin mulki da ilmi da al’umma da ta san ciki da wajen rayuwa da wayewar kai da kamala da sanin ya kamata da dawainiya da juna da son juna da zama lafiya da inganta makwabtaka, kamar yadda Musulunci ya tanada. Me muke so a fahimta a nan? Ko da Turawa ke watayawa da kulla zumunta a Kudancin Nijeriya daga farkon shekarun karni na 19, shi kuma [anfodiyo da mabiyansa, na ta jaddada addinin Musulunci ne, a Arewaci. Ke nan Turawa sun yi shekara 100 a Kudu kafin su waigo mutan Arewa, su kuma mutan Arewar da musulunci ya zaunu tsakanin su kusan shekara 900, sun shekara 100 suna cicciba shi, domin ya koma ga tushensa na asali.

Bisa irin wannan tsari, ke nan da wuya Turawa su yi katsalandan kai tsaye game da rayuwar mutanen Daular Usmaniyya. Kuma shin wa ya kawo bokon, in ce Turawa? Turawan kuma ai ba ‘yan mulkin mallaka ne ba, Turawan Mishan ne suka fara yi masa jagora. Idan kuwa Turawan Mishan ne suka tarkato boko, suka kuma tallata boko, ta yaya za a yi a ce boko ya karbu tsakanin Musulmi, ba wai ga ‘yan Daular Usmaniyya ba kurum, duk inda Musulunci ya tsira, ya girma, ya yi toho, kafin shigo da ilimin bokon?

Shi ya sa ko da Turawan Mishan suka shirya yaki da ilmin Musulunci da kuma bangaren Daular Usmaniyya a Arewaci da yake zaune daram, a munafunce suka soma harkar.

Za Mu Ci Gaba