Matsayin boko a kasar Hausa (2)

Makarantar boko ta farko da Turawan Mishan suka kafa a Arewacin Najeriya ita ce ta garin Lakwaja, a 1862, ita ma ba ta kowa da kowa ba ce, an kafa ta ce saboda bayin da Turawa suka ’yanta da su da ’ya’yansu, mun kuwa san dangantakar da ke tsakanin ’yantattun bayi da Turawa, bauta ce […]

Matsayin boko a kasar Hausa (2)

Makarantar boko ta farko da Turawan Mishan suka kafa a Arewacin Najeriya ita ce ta garin Lakwaja, a 1862, ita ma ba ta kowa da kowa ba ce, an kafa ta ce saboda bayin da Turawa suka ’yanta da su da ’ya’yansu, mun kuwa san dangantakar da ke tsakanin ’yantattun bayi da Turawa, bauta ce dai ko bayan samun ’yanci. Sauran makarantun bokon da suka biyo baya kuwa, makwabtan Lakwaja ne, yawanci kuma a wajen Daular Usmaniyya, wato ba abin da ya hada su da sassan da Musulunci ya yi kaka-gida.

Daga farko-farkon karni na 20 ne Turawan Mishan suka fara nuna sha’awar kutsowa cikin sassan Arewa da ke da mazauna Musulmi. A 1900 ne aka shirya tawaga ta musamman daga kungiyar Christian Missionary Society domin saduwa da Musulmin Arewa. Ita wannan tawaga an yi mata suna ne da ‘Tawagar CMS domin Kiristantar da Hausawa/Fulani/Musulmi,’ wadda ta kasance a karkashin jagorancin su Dokta Walter Miller. Wannan tawaga ta dumfari Kano ne kai-tsaye daga Ingila, ba Sakkwato ko Zariya ko Katsina ba, mun kuma san dalilin zabar Kanon; birni ne da ya kasance mai dadaddiyar hulda ta kasuwanci da kasashen duniya da dama, ga shi kuma wuri ne na ka-zo-na-zo, baki ba za su samu matsalar matsuguni ba. Amma me ya faru da suka isa Kanon suka nemi a ba su filin da za su zauna su kafa makarantu da asibitoci? Ga abin da Sarkin Kano Aliyu ya ce da su, “Kun zo ku kafa makarantu a nan? A’a. Muna da namu makarantu, kuma ana karantar da yaranmu Alkur’ani Mai girma! Kun zo da sababbin hanyoyin kiwon lafiya?  A’a. Ai muna da namu magani, domin kuwa magungunanmu suna nan a cikin Alkur’ani Mai girma da kuma sunan Allah. Ba mu bukatarku; ku koma can inda kuka fito. Na ba ku kwanaki uku, zan shirya muku jakuna dari,  da za su dauki kayayyakinku, ku koma Zariya, kuma har abada ba mu fatar mu sake ganinku.”

Me muka fahimta daga wannan takaddama da ta faru tun daga wancan lokaci? Sarkin Kano Aliyu cewa ya yi su fice masa daga kasa, bai son ganinsu, bai ma bukatar duk wani abu da suka zo da shi, domin kuwa suna da tsarin ilmin da Allah Ya sanar da su daga Alkur’ani Mai girma. Da suka koma ga batun kiwon lafiya na zamani da zai zama mai alfanu ga mutanen Kano da sauran Hausawa/Fulani/Musulmi, me ya ce da su? Shi ma ba sa bukata, domin kuwa duk wata cuta sai da Allah Ya samar da maganinta, duk wani magani da ake bukata kuma yana nan cikin Alkur’ani. Ya kuma kare da muhimmin bayani, “Kuma har abada ba mu fatar mu sake ganinku.” Me ya sa Sarkin Kano Aliyu ya fadi haka? Ya tabbatar Turawan Mishan ba su zo da manufa tagari ga Musulmi ba, idan kuma ya bar su, suka sake dawowa, to dukan akidun da suke dauke da su, wani abu na iya faruwa gare su, su salamce ko kuma su salwance.

Wannan kyama da aka nuna wa Turawan Mishan dole ta sa suka bar Kano, suka tasar wa Zazzau, can ma ba a amshe su da hannu bibiyu ba, domin tuni labari ya ishe Zazzagawa game da wainar da aka toya da Kanawa. Wannan ya sa suka kasance cikin tsaka-mai-wuya, ba su samu wurin zama ko matsuguni ba, sai cikin barikin rundunar sojojin Ingila da ke zaune a wajen birnin Zariya, can a wani kauye da ake kira Girku. Wannan mafaka ita ce ta ba su damar zaunewa a cikin kasar Zazzau. Da kuma sojojin Ingila da ke zaune a kasar Zazzau suka bar kauyen Girku, sai Lugga ya nemi Turawan Mishan su bar Zazzau su koma garin Loko, a can yankin Nasarawa da zama. Can din ma a barikin rundunar sojojin Ingila ne suka samu mafaka, Lugga ya yi haka ne saboda su samu tsaro da kariya daga al’ummar Musulmi da suka yi wa tsinke, idan sun bayyana manufarsu a fili.

Bayan wani dan lokaci tare da taimakon sojojin Ingila, a lokacin mulkin Sarkin Zazzau Aliyu ne Turawan Mishan suka sake dirkako kasar Zazzau domin idar da manufarsu ta tabbatar da addinin Kirista a tsakanin Hausawa/Fulani/Musulmi; nan suka bude makarantar boko ta farko a cikin birnin Zariya, wadda daga baya ta koma Wusasa da zama. Wannan zama a cikin birnin Zariya da kuma kafa makarantar boko, shi ya jawo aka fara ganin Hausawa/Fulani/Musulmi sun fara karbar addinin Kirista; ciki kuwa har da wani da ake cewa jinin sarautar Zazzau ne.

Saboda haka ko ba a nananata ba, kyamar boko da ilmin da ya zo da shi ta dade tsakanin Hausawa/Fulani/Musulmi, ba wai don ilimin bokon bai da alfanu ba, sai dai don wadanda suka zo da shi da kuma manufarsu ta assasa shi. Wannan ne ya sa tun farko masu karatun boko suka zama tamkar saniyar-ware a cikin al’umma Wasu lokutta ma ana ce wa masu karatun boko, suna bokoko, wuta!  Wadansu kuma waka suke faman yi musu, musamman in an gan su za su wuce ko kuma suna dawowa daga makarantar bokon, ana cewa: “ ‘Yan makarantar bokoko, ba karatu, ba Sallah, sai yawan zagin malam.” Ke nan daga irin wadannan kalamai za mu fahimci yadda wadanda suke kyamar bokon ke kallon duk wani dan boko, dan wuta ko mai niyyar shiga wuta ne, a takaice za a iya cewa daga tunanin irin wadancan mutane na farko, boko bai da alfanu, domin kuwa kyamar da Sarkin Kano ya nuna wa Turawan Mishan da suka zo da shi ta tabbatar da cewa boko ba abin alfanu ba ne ga Musulmi! Shin irin wancan tunani na Sarkin Kano Aliyu a farkon karni na 20, irinsa ne masu kyamar na yanzu ke da shi ko kuwa akwai wani na daban?

Za mu ci gaba.