Matsayin boko a kasar Hausa (3)

Kafin mu ba da wannan amsa, ya dace mu bibiyi yadda bokon ya samu gindin zama sosai a tsakanin Hausawa/Fulani/Musulmi da tsarin mulkin mallaka ya zaunu a wannan yanki. A tuna fa da Turawa ‘yan leken asirin kasashen Afirka da Turawa ‘yan mishan da Turawa ‘yan kasuwa da Turawa ‘yan mulkin mallaka da suka biyo […]

Matsayin boko a kasar Hausa (3)
Matsayin boko a kasar Hausa (3)

Kafin mu ba da wannan amsa, ya dace mu bibiyi yadda bokon ya samu gindin zama sosai a tsakanin Hausawa/Fulani/Musulmi da tsarin mulkin mallaka ya zaunu a wannan yanki. A tuna fa da Turawa ‘yan leken asirin kasashen Afirka da Turawa ‘yan mishan da Turawa ‘yan kasuwa da Turawa ‘yan mulkin mallaka da suka biyo bayan su, duk manufa guda ce ta kawo su kasashen Afirka, su tatse tattalin arzikin nahiyar, su kuma tabbata addininn Kirista ya rinjayi duk wani addini da suka iske, musamman ma dai addinin Musulunci! Abin nan ne da ake cewa daurin gwarmai, ‘yan leken asiri Turawa sun leka sun gano masu yadda kasashen Afirka suke ciki, daga baya masu yi cinikayya suka shigo, sai ‘yan mulkin mallaka don su mulke su, aka kuma tabbata Bayibul ne a hannun Mutanen Afirka, ba Al’kur’ani ba, musamman a kasar Hausa idan suka yi haka, to sun ci wannan da yaki na har abada.

Saboda haka ko da Turawan mulkin mallaka suka shantake a wannan yanki, da su da sauran abokan huldarsu suka ci-karensu-ba-babbaka, sun yi hakan ne domin manufarsu ta mulki da tatse tattalin arziki. Haka batun ya kasance dangane da ilmin boko da ‘yan mishan suka shigo da shi. Ko da Turawan mulkin mallaka suka fara tunanin tabbatar da ilmin boko a wannan yanki, cikin dabara da munafinci suka yi hakan.To sai dai wani abin la’akari shi ne ko da ake ta wannan je-ka-dawo game da ilmantar da Hausawa/Fulani/Musulmi na wannan yanki, wasu daga cikin Razdan na wancan lokaci sun nuna damuwarsu kan yadda aka bar ‘yan Mishan kadai ke gudanar da harkar, sun bada shawara da bayanan irin yadda ya kamata a fito wa wannan harkar ba tare da an sami tangarda ba. Wani wanda ya fi nuna damuwarsa kan wannan batu shi ne Razdan Manjo Burdon na Sakkwato. Tun farkon kama aikinsa ya yi watsi da tunanin barin Turawan Mishan su kadai su ci gaba da kafa makarantunsu a cikin Lardunan da Musulmi suka fi yawa duk da wannan shi ne tsarin da gwamnatin Ingila ta kafa, ake kuma bi. Ganin cewa an fara raja’a zuwa ga ba ‘yan Mishan dama su ratso kasashen Musulmi, kuma an samu nasara mai yawa ya sa Manjo Burdon ya kafa tasa makarantar boko ta Elementare da yawun gwamnatin Ingila, wadda ita ce makarantar boko ta farko, a Sakkwato da Arewacin Nijeriya ta gwamnati, a shekarar 1905.

Da yake Manjo Burdon ya san ‘mugun’ abu ne ya zo da shi, ya nuna damuwa da tsoransa game da wannan sabon tsari da ya nemi ya tsira a Daular Usmaniyya ga gwamnatin da yake wa aiki yana neman agaji da taimako da kuma shawarwari. Ba a dade ba Sarkin Musulmi da sauran sarakai da hakimai da dagatai na wannan yanki na Sakkwato suka nuna rashin jin dadinsu game da wannan sabon tsari na ilmin boko. Wannan ya sa shekarar farko ta fara karatun, a 1906, daliban makarantar ba su wuce hudu ba da suka amince a tura makarantar, su ma ‘yan tagajan-tagajan ne daga cikin al’ummar ta su. Sai dai daga baya ne  ta hanyar matsi da farfaganda, inda Turawa suka nuna wa sarakunan cewa ilmin da ake ba yaran a Makarantar ba na addinin Kirista ba ne ya sa aka fara amincewa da shi, ta yadda a shekarar 1907, akwai dalibai 36 daga masarautar Sakkwato da Gwandu da Argungu da suke karatu a wannan makaranta ta Manjo Burdon.

Ke nan abin da su Dokta Miller, ‘yan Mishan suka dade suna hankoron su cimma na shigar da ilimin boko cikin Daular Usmaniyya tun da dadewa, ga shi ya fara samuwa cikin ruwan sanyikon gwamnatin mulkin mallaka. Ganin irin nasarar da aka samu ta kafa wannan makaranta a Sakkwato, sai maganar matsa wa Hausawa/Fulani/Musulmi su amshi ilmin boko ta ci gaba da hayayyafa. Batutuwa sun dinga tasowa mabambanta a tarurrukan gwamnatin, amma Gwamnatin Ingila ba ta sami karfin da za ta yi wani abu game da matsalar ba, saboda tsoron abin da zai biyo baya, musamman ganin irin artabun da aka yi da malaman ‘Yandoto da na Satiru a Sakkwato, wanda ya jawo aka murkushe da radaddage garin Satiru, garin ya koma tamkar biranen Hiroshima da Nagazaki, wato inda aka yi wa ruwan bom, saboda turjiyar da Musulmi suka nuna game da Turawan mulkin mallaka a wannan yaki da fadin kasar Hausa baki daya. Ke nan Turawan mulkin mallaka sun san abin da suke bukata da suka nemi shigo da ilmin boko, su kuma al’ummar wannan yanki ko a wancan lokaci sun gano wayon nasu.

A daidai lokacin da Manjo Burdon ke nasa kokarin a Sakkwato, tuni wani mashahurin dan Mishan, wanda aka fi sani da Hans bischer ya zama dan kasa a Arewacin Nijeriya. Da ma can tun asali ya zo kasar Hausa domin aikin mishan daga shekarar 1900 zuwa 1902, ciwon zazzabin cizon saura ya sa ya koma gida Ingila,man magani, bayan ya warke, ya sake dawowa Arewacin Nijeriya a watan Satumbar shekarar 1903, wannan lokaci a cikin sabuwar riga ta matsayin Mataimakin Razdan a lardin Borno, ba dan Mishan ba.

A lokacin da Hans bischer da ya koma gida neman magani, bayan ya warke, ya karo karatu, ya kuma dawo Arewa da digirinsa na biyu, ga shi ya iya Hausa da Larabci, sa’annan ya nakalci Arewacin Nijeriya, saboda ya yi aikin mishan na shekara biyu a cikinta. Wannan ya sa Turawan mulkin mallaka suka karbe shi hannu bibiyu, wanda ya sa suka ba shi mukamai masu yawa, ta yadda daga baya saboda iya munafunci, ya sa aka yi masa lakabi da [an Hausa. Ya yi wa Turawan mulkin mallaka aiki tukuru ta yadda ko da aka fara maganar yaya za a yi da batun ilmin boko a tsakanin Hausawa/Fulani/Kanuri/Musulmi, kuma wa za a dora wa wannan nauyi, ba wata tababa, yawancin Razdan-Razdan na Arewa, shi suka ga ya dace a dora wa wannan nauyi, musamman kuma da yake mutum ne da ke ‘son’ Hausawa/Fulani/Kanuri/Musulmi.

A daidai shekarar 1908, kimar Hans bischer ta kara fitowa fili inda aka fahimci cewa ya nakalci harshen Kanuri da Fulfulde, baya ga Harsunan Hausa da Larabci da tuni ya kware kan su. Duk da cewa ba a samar da Ma’aikatar Ilmi a Arewacin Nijeriya a wannan lokaci ba, an sanya Hans bischer ya kasance shugaban Sashen Ilmin a kaikaice.

Ganin cewa bai da kwarewa a wannan fanni na ilmi, tun da dan Mishan ne, kuma ga shi Arewacin Nijeriya ta kasance daban dangane da batun ilmin boko a kasashen da ke karkashin mulkin Ingila, ya sa aka ba Hans bischer hutun wata shida, aka kuma umurce shi da ya ziyarci kasashen da Ingila ke mulka da dama domin ya yi nazarin tsarin ilminsu (na boko da addini) domin ya sami damar gudanar da aikinsa da kyau a Arewa. Da farko dai an tsara Hans bischer ya ziyarci kasashe kamar su Sifros da Masar da Sudan da Gambiya da Saliyo da Gwal Kwas da kuma Kudancin Nijeriya. Daga baya aka kawo Malesiya da Zanzibar cikin jerin kasashen da zai ziyarta. Da aka tace kasashen daga baya, sai aka bar shi da ziyartar kasar Masar da Sudan da Gwal Kwas da kuma yankin Legas, a Kudancin Nijeriya.

Za Mu Ci Gaba