Matsayin boko a Kasar Hausa (4)

 Me ya sa aka zabi wadannan kasashe? kasar Masar dai kamar yadda muka sani, kasar Musulmi. kasar Sudan kuma, kasa ce, rabi Musulmi, rabi, wadanda ba Musulmi ba. Gwal Kwas kuma kasa ce wadda wadanda ba Musulmi ba suka fi yawa. Yankin Legas kuma na cikin sabuwar Nijeriya da ake son a assasa ilimin bokon […]

Matsayin boko a Kasar Hausa (4)

 Me ya sa aka zabi wadannan kasashe? kasar Masar dai kamar yadda muka sani, kasar Musulmi. kasar Sudan kuma, kasa ce, rabi Musulmi, rabi, wadanda ba Musulmi ba. Gwal Kwas kuma kasa ce wadda wadanda ba Musulmi ba suka fi yawa. Yankin Legas kuma na cikin sabuwar Nijeriya da ake son a assasa ilimin bokon da su tuni an dade da fara gudanar da shi. Ziyartar wadannan kasashe zai ba Hans bischer hasken yadda aka samu nasara ko akasin haka da kuma yadda za a bullo wa Arewacin Nijeriya da wannan sabon ilimin! Ke nan sai da Turawan Ingila suka yi nazari da bata-hankalin dare kafin su tabbatar da ilmin boko a Arewacin Nijeriya. Me wannan ya nuna mana ke nan? Turawa sun san cewa tsarin da za su kawo wa Arewa ba zai samu karbbuwa irin yadda suke so ba, saboda sun yi hannun riga da tsarin ilimin da ke gudana a Arewa a lokacin!

Tun farko dai mun bayyana cewa Hans bischer ba dan mulkin mallaka ba ne tun asali, dan Mishan ne. Duk wata dabara ko shiri ko tsari da aka nemi a nuna ko a bayyana na cewa an kawo Hans bischer ya samar da ilmin boko mara sufane, wanda ba zai cutar da Hausawa/Fulani/Kanuri/Musulmi ko mutanen Arewa ba, soki-burutsu ne, munafinci ne, yaudara ce!

Shi ya sa ko da Hans bischer ya dawo gida daga zagayen karo ilimi bai bada shawarar a zabi tsarin da ya gani a kasar Masar ba, domin na Musulunci ne zalla! Bai kuma amince da tsarin Gwal Kwas ba, domin ya san Musulmi ba za su amince da ilimin da bai da ruhin Muslunci ba. Daga karshe ya bada shawarar a samar da tsari mai kama da na kasar Sudan, domin shi ne yake jin cewa zai yi daidai da na Arewacin Nijeriya, inda wadanda ba Musulmi ba da kuma Musulmi suke cakude wuri guda.

A shekarar 1909 ne aka kaddamar da makarantar boko ta farko ta gwamnatin Ingila a kofar Nasarawa, da ke birnin Kano. Ganin cewa da sauran lokaci kafin a fara karatu, gadan-gadan, ga shi kuma ba malamai da kayan aiki, dole ta sa Hans bischer ya kafa makarantar horor da Malamai a watan Satumbar 1909, inda ya nemi Razdan-Razdan su turo masa yaran da zai koyar a matsayin Malamai domin su samu horo, su kuma shirya sosai, kafin dalibai su fara karatu a shekarar 1910.

daliban farko na wannan makaranta da aka turo domin su zama Malamai na farko, sun zo ne daga Lardunan Sakkwato da Kano da Katsina, ba kuma da son ran sarakunan Lardunan aka turo su ba, saboda kyamar da ake nuna wa tsarin. Ganin haka ya sa Razdan-Razdan na yankunan Sakkwato Da Kano da Katsina suka sa Sarakunan wannan yanki karan-zuka, suka matsa wa sarakunan don dole su turo malaman allo da za a koya wa aikin malantar boko, shi ma sarakunan suka turje, ba su bada hadin kai ba. Da matsin ya yi yawa, har ta kai ana son a tube rawunnan wasu sarakunan, daga baya suka suka amince su tura wasu mutane daga yankunan nasu, amma ba su tura mutanen kwarai ba, sai dai bara-gurbi, wato mutane wadanda ko da an lalata kwakwalwarsu da ilimin boko, ba komi, don ba za cutar ba. Daga Lardin Sakkwato, mazaunin Daular Usmaniyya malamai hudu da aka samu damar turawa Kano, ciki har da wani mai tabuwar hankali, wato mahaukaci, don dai kurum a faranta wa Turawan mulkin mallaka.

Wannan ya kara tabbatar mana da cewa ko da ‘yan mulkin mallakar suka amshi ragamar samar da gudanar da ilmin boko, ba su samu sukunin yin haka cikin ruwan sanyi ba. Sai dai duk da wadannan matsaloli, Hans bischer bai yi kasa a gwiwa ba, gwamnati kuma ta daure masa gindi.

Domin a samu hadin kai sosai, a kuma tabbatar da nasara a wannan makarantar bokon ta farko, ta gwamnati, an fara ne da bude dakunan horaswa guda biyu na Malamai. Hans bischer shi ne Malami, kuma shugaba, yana koyar da karatu da rubutu da lissafi da labarin kasa. Ana fara karatu ne daga karfe 8 na safe zuwa 12 na rana, a bar yara su tafi domin sallar azahar, can kuma in an sarara daga karfe 2 zuwa la’asar a ci gaba. Haka aka dinga gungurawa har lokacin da sauran sarakuna suka amshi kiran Hans bischer sosai; ta yadda daga watan Maris na shekarar 1910 akwai dalibai 35 a makarantar dan Hausa a Kano, ya zuwa watan Disamba na shekarar 1910 kuwa, daliban sun kai 100.

Ta haka ne aka shiga samar da sauran ma’aikata da malamai, su kuma Sarakuna suna fitar da kudi daga Baitulmali domin gudanar da makarantar, sai dan taimakon da ba a rasa ba daga gwamnatin mulkin mallaka daga Ingila.

Ganin nasarar da aka samu daga tsarin da Hans bischer ya gudanar aka soma tunanin samar da wasu makarantun a wasu Larduna can daban. An fara ne da Kano a kofar Nasarawa a shekarar 1911, inda aka samar da makarantar Lardi, a 1912, aka kuma bude wata a Sakkwato da Katsina. Niyyar dai ita ce a samar da makaranta daya a kowane Lardi ko babban gari, da alama kuma komi ya daidaitu, domin yawancin Lardunan da wasu manyan garuruwa sun samu nasu makarantu daga 1914. Daga nan Malamai suka yawaita, dalibai sai tururuwa suke yi zuwa makarantun boko, wannan ya sa Turawa suka kara ganin kimar Hans bischer sosai ta yadda daga 1914 aka kara mai girma, ya zama Daraktan Ilmi na dindindin a Arewacin Nijeriya. Daga watan Oktoba na 1912 zuwa Agusta na 1914, malamai da Turawa masu gudanar da ayyukan makarantar dan Hausa sun kai ishirin da shida. Su kuwa dalibai da aka yi wa rejista a ranar 31 ga watan Disambar 1913 sun kai 209.

Wannan shi ne hoton rayuwar samuwar ilimin boko a wannan yanki. Ba a assasa shi domin ya taimaki mutanen wannan yanki ba. Tun asali da ma can manufar ita ce bokon ya kasance abin da zai raba Hausawa/Fulani/Kanuri/Musulmi da kyawawan akidojin da aka san su da su. Ya raba su da addinin Musulunci. Ya sa musu son duniya fiye da komi, a maimakon neman lahira. Ya mayar da mutanen yankin su kasance tamkar Turawa ta kowace irin fuska. Manufar dai ita ce daga baya, bayan tsawon shekaru, Turanci da tunanin Turawa, ya kasance hanyar rayuwar al’ummar wannan yanki. Ta yadda idan al’ummar yankin suka zauna suna nazari da tsinkaya, za su ga cewa sun yi nisa da turbar da kakanni da kakkaninsu suka dora su. Za su ji labarin jihadi da gwagwarmaya, tamkar tatsuniya ko labaran mutan da. Wannan ita ce babbar manufar mulkin mallaka da ma duk wani abu da ya zo da shi.

Za Mu Ci Gaba