Matsayin boko a kasar Hausa (5)

Shin idan muka tsayu, muka natsu, ba za mu iya cewa lallai burin ‘yan Mishan ya biya ba? Shin buri da manufar ‘yan mulkin mallaka ba su tabbata ba a halin yanzu game da tabbatar da ilimin boko da kokarin kawar da tunanin Hausawa/Fulani/Kanuri/Musulmi? Ba sai an nanata ba, duk inda Musulunci ya ci karo […]

Matsayin boko a kasar Hausa (5)

Shin idan muka tsayu, muka natsu, ba za mu iya cewa lallai burin ‘yan Mishan ya biya ba? Shin buri da manufar ‘yan mulkin mallaka ba su tabbata ba a halin yanzu game da tabbatar da ilimin boko da kokarin kawar da tunanin Hausawa/Fulani/Kanuri/Musulmi?

Ba sai an nanata ba, duk inda Musulunci ya ci karo da wani tsarin ilimi daban da wanda ya aminta da shi ko makamancin haka dole a samu tashin-tashina, wannan ba a Nijeriya kurum ko kuma a Arewa ba, duk inda ruhin Musulunci ya kai to sai an sami takaddama tsakaninsa da duk wani abu da ya nemi ya kasance kishiya gare shi. Al’adar addinin Musuluncin ce da kuma tanade-tanadensa ta sabunta kansa daga zamani zuwa zamani, musamman a lokacin da ya gauraya da sabon yanayi ko aka yi masa jirwaye- mai-kamar-wanka. Sai dai sabuntawar kuma tana zuwa ta fuskoki mabambanta; ko dai ta wa’azi ko karantarwa ko jihadi! Haka wannan yanayi ya kasance ko da ilimin boko ya cudanya da ilimin addinin Musulunci a kasar Hausa. Sai dai a kula ko cikin masu wa’azin da karantarwar da jihadin domin a daidaita tunani ko sahu, akwai masu yin su bisa akidoji ko ra’ayoyi mabambanta. Akwai masu bi sese-sese, akwai wadanda za a iya kira ‘yan gargajiya, akwai wadanda ba su barin ko-ta-kwana, akwai kuma ‘yan kan gaba, akwai kuma masu fadar ta yadda take, ba surki ko kokarin yin kedafare! Wannan haka yake a ko’ina cikin duniyar Musulmi, shi ne kuma ya shigo da tunani irin na boko haram ko boko halal ko kuma yanzu boko akida ko ‘yan boko da makamantan su da muke ta faman kai-kawo bisa su.

Ke nan kokarin fahimtar yadda ilimin boko ya ginu da wanzuwa da kuma tabbatuwa har yake karon batta da na addinin Musulunci a irin wannan yanayi zai koma ne ga kokarin da wasu ke yi na jaddada da sabunta da inganta da daidaita da kammala tsarin addinin Musulunci kamar yadda Allah ya saukar da shi, annabin rahama ya gabatar da shi. To amma tambayar da za a fara da ita ba ta wuce, shin addinin Allah, (nan ina magana ne kan Musulunci), ya haramta ilimin boko ko kuwa annabin rahama ya ce kada mu yi mu’amala da ilimin boko ko wani ilmi da ba na addinin Musulunci ba? Shin addinin Musulunci ne ya ce idan muna son mu tabbatar da shi sai mun kashe rayuka kafin nan kamar yadda ‘yan boko haram ke ikirari? Ko kuwa haka annabin rahama ya yi a zamaninsa, ya ce ko ya koyar ko ya amince da cewa duk wani ilimi da ba addinin Musulunci ba ko duk wani wanda ba Musulmi, to bai dace da Musulmi da Musulunci ba? Shin saka bom, nan da can da kashe rayuka, daidai ne a addinin Musulunci? Shin neman ilimin addini tsantsa ba sufane, shi ne a’ala ga Musulmi da Musulunci? Shin ilimin boko da muke fama da shi a halin yanzu, abokin tafiya ne ko kuwa abokin watsi ne da shi a wani zango a lokacin tafiyar da aka faro? Shin abubuwan da zamani da ilimin ya zo da su, karatu da ilimin tsanta irin su likitanci, lauyanci, injiniyanci, akawutanci, kasuwanci, da makamantansu da wadanda suke tu’ammali da su abin a yaba ne ko kuma a zaga? Shin ba wata hanya da za a iya bi a ga ilimin boko ya zama dan gida a cikin ilmin addinin Musulunci da tsarin tafiyar da shi? Shin babu malaman addinin Musulunci da suka kasance ruwa-biyu a halin yanzu, Musuluncin ya zauna, bokon kuma ya zauna ba tare da matsala ba? Shin komawa ga tsarin ilimin addinin Musulunci tsantsa, irin na iyaye da kakanni a halin yanzu shi ne mafita gare mu ko kuwa?

Kafin mu kokarta amsa wadannan tambayoyi, ya dace a fahimci wani abu game da kungiyoyin da suke tashe a halin yanzu, mu soma da kungiyar Boko Haram. Kafin kashe-kashe da saka bama-bamai da suka zama ruwan dare a kasar nan, ba kowa ne ‘ya sanda ‘yan wannan kungiya a matsayin ‘yan tada hankali da jefa bama-bamai ba, sai daga baya.Wato dai kungiya ce kamar sauran kungiyoyi a cikin addinin Musulunci. Ta dade da wanzuwa, tana da’awa irin tata da kuma karantarwa da malamai da dalibai masu dama. An fi sanin su a bangaren Arewa Masu Gabas, musamman a yankin jihar Borno, daga baya suka barbazu zuwa sassa daban-daban na kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, da ma can wannan kungiya ta Jama’atu da kisan jama’a ta faro, ko da dasa bama-bamai ta soma da’awa? Ko alama! Domin kuwa tarihi ya nuna cewa an sha zaunawa da ‘yan kungiyar domin a tattauna. An sha yin mukabala da su kan addini da ra’ayinsu kan boko da illolinsa. Inda aka fara samun matsala a tawa fahimtar, shi ne lokacin da aka fara kamewa da daurewa da rushe gidajen ‘yan kungiyar da kuma bugewa da kashe ‘yan kungiyar, ba bisa ka’da ba. Ke nan za a iya cewa ko da ‘yan Boko Haram ba su da niyyar shiga cikin harkar tada-zaune-tsaye, to da alama abin nan ne da ake cewa tura ta kai bango, shi ya kai su ga yin fito-na-fito! Wato matsi da kisa suka sa suka koma amfani da makamai da bama-bamai, kila kuma da sa bakin wasu kungiyoyi masu irin wannan akida daga waje.

Duk wannan me ya nuna mana? Akwai abubuwa da dama da ba a fahimta ba game da wannan kungiya da ma wasu irin su game da wanzuwar boko da yadda ake kallonsa a halin yanzu. Tambayoyi ne kuma za su kara tuzgowa har kafin a fahimci ainihin gaskiya. Shin me ‘yan Boko Haram suke da’awa kan shi? Me ya sa suke tada zaune-tsaye? Me ya sa ake ta cece-ku-ce kan irin yadda suke far wa jama’a da kisa da raunatawa, ba ji ba gani?

Za Mu Ci Gaba