Matsayin matasa da yadda za su tafiyar da rayuwarsu a cikin al’umma
A yau kuma MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171), nazari da tambihi ta yi game da matasa. Shin wane ne matashi, me ya kamata ya yi domin ci gaban kansa da na al’ummarsa, ta yaya zai zama mai amfani ga kansa da kuma rayuwarsa da ta jama’arsa gaba daya? Wadannan da ma wasu tsokacin, su ne […]
A yau kuma MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171), nazari da tambihi ta yi game da matasa. Shin wane ne matashi, me ya kamata ya yi domin ci gaban kansa da na al’ummarsa, ta yaya zai zama mai amfani ga kansa da kuma rayuwarsa da ta jama’arsa gaba daya? Wadannan da ma wasu tsokacin, su ne ke kunshe cikin wannan mukala:
Matasa su ne kashin bayan kowace al’umma. Hikimar haka a bayyane take, domin tun daga haihuwar yaro sabon mutum zuwa shekarun balagarsa, yana karkashi kulawar mahaifansa ne, cinsa da shansa, sutura da ilmartar da shi duk sai an taimaka masa kafin ya amfana da su.
Daga lokacin da yaro ya balaga, ya fara shiga shekarun karfi da hankali da kaifin basira da zurfin tunani ke nan, har ya zuwa shekaru hamsin. Wadannan su ne shekarun tashe, mai dauke da su shi ake kira da matashi. Daga wadannan shekaru hamsim zuwa sama kuwa su ne ake kira da shekarun tsufa.
A cikin wadannan shekarun tashe ne matashi yake jin karfi da kuzari suna ratsa jikinsa da zuciyarsa, sai ya kasance ba ya da bukata ga wancan halin da yake cikinsa a da na sai an taimaka masa zuwa ga son ya dogara da kansa saboda hankalinsa ya cika, ba sauran wautar kuriciya a tare da shi, kwakwalwarsa na da kaifin basirar gane abu mai kyau da marar kyau, ba kamar lokacin kuruciya ba da sai dai idan manyansa sun lurar da shi hakan. Yanzu zuciyarsa takan iya zurfafa tunaninta, ta duba, ta tantance kafin ta zartar da hukuncin wani abu da zai gudana a rayuwarsa.
Wannan hali da mataki da rayuwar matashi kan shiga, suna da matukar muhimmacin gaske. Domin lokaci ne da matashi yakan gane muhimmancin kansa da kansa, da kuma muhimmancin kansa ga al’ummarsa. Matashi kashin baya ne ga al’ummarsa, kashin mai kwari ko marar kwari; ya danganta da irin kalar matasan da al’ummar ke dauke da su.
Wasu matasa sukan yi la’akari da wannan yanayin da jikinsu ke zo musu da shi a cikin shekarun tashe, su ga sun yi amfani da shi su more wa rayuwarsu da shi. Wasu kuwa yanayin shekarun tashen zuga su yake yi, su yi ta ayyuka marasa amfani har shekarun su kare ba tare da sun amfana ko sun amfanar da al’ummarsu da komi ba.
Matashin da yake amfana da shekarun tashensa, shi ne mai tunani da neman ilimi, domin yana sane da cewa ilimi shi ne fitilar duniya. Ilimin kuwa ya hada da na addininsa ko na zamani, koma dai ilimin wata sana’a ko wata huldar rayuwa ne. Neman ilimi ya zama wajibi ga matashin da yake son ci gaban rayuwarsa, har ma da rayuwar al’ummarsa, domin haskensa kadai ya isa ya haska jama’arsa koma duniya baki daya. Ilimi ne yake haska rayuwar matashi, ya yi mata ado har ya zama tauraro a cikin sa’o’insa.
In dai matashi ya yi kokari ya samu ilimi, to lallai kuwa ya dace da babbar garkuwa, domin ba za a ci shi da yaki ba, ba za a yi ba shi ba, ba kuma za ya kunyata a cikin jama’arsa ba. Ka zama gandun ilimi, kar ka yarda ka zama gandun jahilci a cikin jama’arka. Jahilci kaskanci ne, tozarci ne, wulakanci ne da yake jawo wa mai dauke da shi ja’iba.
Matashi ya zama mai fafutuka a cikin shekarun tashensa saboda a cikin fafutukarsa ne sa’arsa da arzikinsa suke, wanda bai tashi ya nema ba ta yaya zai samu? Allah ma Ya ce ‘tashi in taimake ka. Kar ka damu da rashin nasara ko wani kalubale da ke tusgowa yayin nema, wannan duk darasi ne a cikin makarantar nema. Kai dai ka nema kuma ka jajirce, ka nuna kwazo da dagewa a yayin neman. Kuma ka tabbata kana a kan turbar gaskiya a yayin neman, domin neman halaliya shi ne nema mai tsabta da dadin ci hankali kwance.
Shin wai ma mi zai hana matashi neman halaliyarsa, alhalin dukkan dama yana da ita kamar yadda yanayin shekarunsa suka nuna? Ka yi kokari ka raba kanka da kasala ko lalaci, domin malalaci bai amfani kansa ba ma ballantana wani, kullum yana nan kwance zuciya a mace, duk abin da ya raya zai fara yi na fafutuka sai zuciyarsa ta raya masa gazawa. To kai ba ka tunani da wadanda suka iya, ya aka yi suka iyan? Ta yaya suke samun nasara? To ka sani ba a wane ga banza, in ba dare ba ya sha rana. Kai ma ka zage damtse ka nemi naka, ka huce wa kanka takaici, ko ka zama abin tinkaho ga al’ummarka. Kuma ka sani, cikin shekarun tashe ne za ka yi wa tsufanka tanadi, don tsufa yana tafe ne da gazawa na jiki na zahiri da na badini. Don haka jikinka a tsufa ba lalle ne ya bar ka ka iya yin wata fafutuka ta rayuwa ba, don haka ka zama mai tsimi da tanadi a cikin fafutukarka. Kar ka zama almubazzarin matashi, domin karshenta ka kare da zama matsiyacin tsoho a karshen rayuwa.
Matashi mai wadatar zuci ya samu nasara mai yawa a rayuwarsa, domin shi ne a tunaninsa ya gamsu hani’an da ni’imomin da Allah Ya yi masa, ya san akwai da babu, ya san samun nasara mataki mataki ce. Idan ya samu kadan ya gode, ya tattala. Idan ya samu da yawa, nan ma ya san daga Allah ne. In ma ya rasa ya san wani hani ga Allah baiwa ne. Yana da kyau matashi ya zama mawadaci a zuciyarsa, zai hana shi kwadayin abin wani da sa ido a kan kayan wani. Ka yi hakuri da kadan, ka gode da yawa. Kar ka yi kyashi ko hasada, Allahn da Ya yi mai arziki shi ne ya yi matsiyaci kuma yana da hikimarsa ta yin haka. dabi’ar raina samu, ita ta samar da matashi barayo, domin da zuciyarsa a wadace take bai raina baiwar da Allah Ya yi masa ba, da bai dauki kayan wani ba.
Matashi mai ladabi da biyayya shi ne ya dace a cikin rayuwarsa. Domin ladabi da biyayya su ne akalar nasarar rayuwa. Mai biyayya shi ke kwantar da hankali har ya sani kuma ya iya ba tare da wata wahala a kansa ba. Raini kuwa shi yake kai matashi ya baro. Kar ka raina magabatanka, kai ma za ka so kanananka su girmama ka. Marar ladabi ba ya bin doka da oda, wannan halin kuwa illa ce a rayuwar matashi.
Matasa mu hankalta, mu gane muhimmancin rayuwarmu a cikin al’ummarmu. Mu ne kashin bayan jama’armu, ba wata al’umma da ta ci gaba alhalin matasanta ba su a kan turbar ci gaba. Mu guji yin ababen da za su tagayyara mana shekarun tashenmu a banza, irin su shaye-shaye da zaman banza, tada zaune tsaya da rashin ganin muhimmacin rayuwa da zaman lafiyarmu.
Mu rika tunani da ababen da za su inganta rayuwarmu, irin su neman ilimi, yin sana’a da sauransu. Mu rika kawo ababen ci gaban jama’armu da muhallinmu, irin su ayyukan taimakon kai da kai da tsaftace muhallinmu, wanzar da zaman lafiya, ture fitina a tsakaninmu da dai sauran ayyukan cin gaban rayuwarmu.
Ya Allah Ka shirye mu, Ka ganar da matasanmu mu rika kyautata rayuwarmu da inganta ta ko ma zama kashin bayan al’ummarmu mai inganci da kwari, ta yadda jama’armu za su dogara da mu, su mike; amin.