Matsayin tsarkake ayyukan ibada don Allah a Musulunci (4)
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu, Bawan Allah Muhammad tare da alayensa da sahabbansa baki daya da kuma duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako. Bayan haka, yau kuma […]
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu, Bawan Allah Muhammad tare da alayensa da sahabbansa baki daya da kuma duk wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya siffatu da sunnarsa, har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, yau kuma mukalarmu za ta ci gaba ne daga kan:
Fa’ida ko tasiri ko ribar ikhlasi:
Yadda al’amari yake dai shi ne ba a karbar kyakkyawan aiki dole sai da ikhlasi tare da shi (wato an tsarkake niyya, an yi shi saboda Allah kadai). Haka nan rashin ikhlasi a cikin aiki yana sanya a mayar da shi, ya zama mara fa’ida ga mai shi ko da an yi shi mai yawa (wato komai yawan aikin ibada, in dai ba yi ta tare da kyakkyawar niyya ta ikhlasi ba don Allah, to sai ya tafi a banza a tutar babu, ba za a samu sakamako a kansa ba).
Shi ikhlasi yana tattare da fa’idoji ko tasiri ko riba da ake samu dangane da tabbatuwarsa a cikin aikin ibada kamar haka:
1. Shi yin ikhlasi a kowane aikin ibada, yana taimakawa cikin yardar Allah, wajen kange sirdadowar (lallabowar) Shaidan ga bawan Allah, wanda zai sa har ya zame a cikin aikin, ballantana har ya bata shi. Allah, Wanda tsarki ya tabbatar maSa, Ya ce, dangane da Shaidan, “(Yayin da shaidan din) ya ce, ‘Ina rantsuwa da buwayarKa, ina batar da su gaba daya. Face bayinKa tsarkakakku (wato masu ikhlasi a ayyukansu) daga gare su.” (Surar Sad, aya ta 82-82). In dai an yi aikin saboda Allah, a karkashin koyarwar ManzonSa (Sallallahu Alaihi Wasallam), to ana samun kangiyar Allah daga lababowar Shaidan cikin aikin ballantana ya bata shi.
2. Shi mai ikhlasi tsararre ne a cikin tsaron Allah, daga aikata sabo da munkarai (duk abin da shari’a ta ki). Allah, Wanda tsarki ya tabbatar maSa, Yana cewa, dangane da al’amarin (Annabi) Yusuf (Alaihis Salam), “…. Kamar haka dai, domin Mu karkatar da mummunan aiki da alfasha daga gare shi. Lallai ne shi daga bayinMu zababbu (masu ikhlasi) yake.” (Surar Yusuf, aya ta 24). Allah Yana tsaron mai tsarkake niyyar aikin ibada dominSa, daga fadawa cikin sabo da munanan ayyuka.
3. Da ikhlasi ake samun daukaka ta darajoji daban-daban da kuma budin kofofin alheri iri-iri. Shi ya sa ma Annabin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), yake cewa, “Lallai (kai Musulmi) ba ka motsa ka aikata wani aikin ibada ba, alhalin kana nufin Allah da wannan aikin, face an kara maka daraja da daukaka saboda shi.” Muttafakun alaihi.
4. Ta yin ikhlasi ake samun natsuwar zuciya da dandanon sa’ada (samun shiga Aljanna) da kuma raha (walwala, sakakkar zuciya) cikin kankan-da-kai ga Alkhalik (Mahaliccin kowa da komai). Malam Fudailu dan Iyal, Allah Ya rahamshe shi, yana cewa, “Duk wanda ya san mutane, zai samu walwala, zai huta.” Wato idan ya san cewa lallai su mutane ba su iya amfanar da shi komai, kuma ba su iya cutar da shi da komai, sai ya samu walwalar rayuwarsa kuma ya huta da duk wani kame-kame, ya koma ya rike Allah, Mai kowa, Mai komai.
Yaya zan kasance mai ikhlasi don Allah a cikin ayyukana?
Shaidan yakan giggitta (halarto) wa mutum (Musulmi) abubuwa masu yawa mabambanta don ya bata masa kyawawan ayyukan ibadarsa (kamar riya da jiyarwa da girman kai ko jiji-da-kai da sauransu). Shi kuma mumini ba ya gushewa yana kokari (jihadi), iyakar iyawarsa, wajen yaki da makiyinsa (Shaidan – Iblis) har zuwa ranar da zai sadu da Ubangijinsa a kan imani da Shi (Allah) da kuma tsarkake dukkan ayyukan ibadar saboda Shi kadai.
Yana daga cikin manyan muhimman makamai na tunkude Shaidan da tabbatuwar ikhlasi, Musulmi ya kasance yana:
1. Addu’a: Dukkan shiriya tana Hannun Allah, kuma su zukata suna tsakanin Yatsun Allah biyu daga cikin yatsunSa, Tabaraka Wa Ta’ala, Mai jinkai, Yana jujjuya su duk yadda Ya so, saboda haka (kai Musulmi) ka koma ka dogara ga Wanda a hannunSa shiriya take. Ka bayyanar da bukatarka gare Shi da kuma gazawarka a matsayinka na fakiri (mabukaci) gare Shi, ka roke Shi dawwamar ikhlasi a zuciyarka. Mafi yawan addu’ar Umar dan Khaddaab (Allah Ya yarda da shi), ta kasance yana cewa, “Ya Allah, Ka sanya dukan ayyukana su zama na kwarai, na kirki, Ka sanya su don zatinKa suna tsarkakakku, kada Ka sanya wani rabo cikinsu ga kowa.” Wato su kasance ba a tunkari kowa a cikinsu ba, ba a nufin kowa cikinsu, sai don Allah kadai aka yi su, ko ake yin su da kuma neman yardarSa da amincewarSa a kan haka, babu ko dan sofane a cikinsu (ayyukan ibadar) na shirka. Ba a hada kowa da Allah cikin ayyukan ba.
2. boye aikin ibada: Yana daga cikin makaman da ke tunkude Shaidan su tabbatar da ikhlasi a rika boye aikin ibada, matukar ba ya bukatar a bayyana shi.
Duk lokacin da aka boye aikin ibada, daga cikin abin da shari’a ta amince a boye shi, an fi sa tsammanin ya zama karbabbe, a samu sakamako a kansa, kuma ya fi samun matsayi a karkashin inuwar ikhlasi. Mai ikhlasi na gaskiya, ya fi son ya boye ayyukansa na kwarai kamar yadda yake bukatuwa ga boyuwar ayyukansa munana. Wannan kuwa haka abin yake saboda fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), cewa, “(Mutum) bakwai Allah Yana sanya su a karkashin inuwarSa, ranar da babu wata inuwa sai taSa: (1) Shugaba adali; (2) Matashi da ya taso cikin bautar Allah; (3) Mutumin da zuciyarsa take like da masallaci; (4) Mutane biyu da suke son juna don Allah, suke haduwa don Allah kuma suke rabuwa a kan haka; (5) Mutumin da kyakkyawar mata, mai matsayi, ta kira shi don ya yi fasikanci da ita, ya ce mata, ‘ina tsoron Allah’; (6) Mutumin da ya yi wata sadaka YA bOYE TA, ta yadda hagunsa ba ta san abin da damarsa ta bayar ba; da kuma (7) Mutumin da ya tuna Allah, shi kadai a kebance, ya zubar da hawaye (saboda tsoron Allah).” Buhari da Muslim suka ruwaito shi.
Bashar bin Alharis, (Allah Ya rahamshe shi), yana cewa, “Kada ka yi aiki don a ambata ko a tuna ka, ka boye kyakkyawan aiki, kamar yadda kake boye mummuna. Lallai, tabbas, an daukaka nafilar dare a kan nafilar rana; da kuma istigifarin lokacin sahur (karshen dare) a kan waninsa; saboda duk wadannan sun fi kaiwa matuka wajen sirri (boyuwa) da kuma kusanci zuwa ga ikhlasi.”
Allah Ya saka wa magabatan kwarai da alheri saboda irin wannan shiryarwa da suka yi wa na baya. Mu kuma Allah Ya datar da mu wajen kula da irin wannan karantarwa da yin aiki da ita don mu dace da samun jinkanSa, (Subhanahu Wa Ta’ala), abin da kowane mutumin kirki yake burinsa.
A nan za mu dakata sai mako na gaba, in Allah Ya so Ya kai mu, tare da fata Allah Ya kara zaunar da mu lafiya a kasarmu da ma duniya baki daya.
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!